← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 141

Sashe 6

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta nufi ciki imtee ta zuba mata ido har ta shige dakin ta, da mamaki ta dubi A'isha ta ce" Anya kuwa lafiyarta kalau? Ko bata da lafiya ne????"

A'isha ta dubeta, tana sake zuba musu miya ta ce" Na kula, kamar inda aka kai baiwar Allahn nan bata je cen ba, ama kin ga, in sha Allah zamu zuba ido mu gani, idan har mun hangi cutarwa sai mu janye jikin mu, Ama wallahi kin bani mamaki wai da kika ki ci me kike tunani ne?, kina tunanin zata cutar da ke ne?"

Imtee ta dubeta ta ce" Me zai hana in ki yin tunanin zata iya cutar da Ni? Ki duba ki gani baiwar Allahn nan du motsin da zan yi laifi ne a wajen ta a gidan nan, kina gani Mama bata taɓa sa hannunta a jikina da nufin dukana ba, Ama ita fa? Sau nawa tana kai min duka? , ko ɗinki na yi sai tace bai yi ba, ko fita na yi ba hijab sai ta min duka d'anta ma ya min, ai kuwa kin ga dole in kiyaye ta tunda Mama sheda ce ina jaririya tace ta kusan sakani a rijiyar cen dan namiji ta so haihuwa ba ni mace ba!"

A'isha ta zuba mata ido, tsoro fal a zuciyarta na irin abinda take gani a kan mahaifiyarta wato mama.....
Ita dai mama ce ta haifeta, itace mahaifiyarta, Ama har ga Allah lokuta da yawa takan ji tsoron halayyar mama da irin yadda take mu'amalantar auntynsu harma da tausayin auntyn da kuma imtee na kamata, sai dai ita ta sani karshen alewa kassss, tana kuma tsoron ranar da Allah zai bayyana mai gaskiya a cikin gidan nan, tabasss kowa sai ya ji kunya a gidan nan.

A hankali ta ce" Wasu lokutan, kece ke ce min in yi taka tsantsan da lamarin rayuwa....., ke kuma ban san yaya aka yi sam baki iya taka tsantsan da lamarin da ya shafi Macen da ta fi kowa daraja a duniyarki ba.................., uhum bari in kai kayan abincin ciki ki share wajen"

Daga haka ta shiga tatare kayan abincin, ita kuma Imtee ta sake binta da kallon mamakin yannayinta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta shiga ninke tabarmar tana jin kiwyar yin sharar.

A kantin Aban yara

Kanti ne dan madaidaici na zana mai dauke da kayan masarufin abinci sai yan slifasss haka na yara da na manya.......wannan itace sana'ar aban yara kuma da ita yake ciyar da iyalinsa gwargwadon samunsa

A kofar kantin suka zuba abincin shi da abokinsa amininsa Usman suka shiga ci sunna tadin rayuwa, shi kuwa Sulaiman yana daga cikin kantin yana cin nasa a cikin kwanon yana kallon waya.

Fira ta yi fira, malan Usman ya dubi abokinsa ya ce" Yanzu Malan Adamu ba zaka tashi daga anguwar nan ko dan yan yayanka yan mata ka bar wajen nan da ake ta fadin abinda yake faruwa da makotanka na baya ba? Anguwa du an tashi an bar musu sun saye filayen layin Ama kai ka ki ka saida musu?"

Malan Adamu yayi dan murmushi yana dubansa ya ce" Wato kana cikin mutanen nan masu daukan jita jitar bakin mutane su rike matsayin makamin yakar kansu da kansu a gaban Allah ko?"

Malan Usman ya ce"A'a ko daya, Ama ai ba a Boye lamarin nan yake ba , a bayane yake ko? Ka duba ka ga tsayin ginin cen, ka duba ka ga irin motocin da ake fitowa da su , ba zaka taba gane me da me ke wakana a cikin gidan ba, sai dai ka hangi shigar motoci ko ka hangi fitowar su, kana gani du an saki gidajen da suke mane da naka an yi shaguna sai kai kadai ke nan? Baka tsoron ace tunanin da ake yi cewar a wancen tangamemen dajin gidan yankan kai ake yi a wayi gari su rasa mutanen yankawa su shigo maka gida? Ko kuma maganar da ake yi cewar akoy wata budurwa a gidan dake bin maza kake so idannuwan yayanka su gani har a gurbata musu tarbiya? In dai basu da abin boyewa yaya aka yi du tsayin lokacin nan ba za'a gane waye wa na cikin gidan ba sai bayanan da yaron gidan wancen takaradin da itama bata da kirki ne ya ishe ta ba, yaron nan Anas wanda yake direba a gidan ya fada ko? To ai ko jikina duka kunne ne Ni ba zan yarda cewar wai uwar dake gidan tana koyar da islamiyyar cen ba, harma ace tarin alkhairan da ake yi a islamiyar tasu ce... ba kuma zan yarda cewar d'anta shine mai taimako a anguwar nan ba, kai dai ai ba mahaukaci bane da zaka yarda da abubuwan nan, kai yanzu ko irin yadda direba tsal ba wata tsiya ba yake murza kudi, ya yiwa mahaifiyarsa gini ya zama itama yanzu wai sai masu kuɗi take mu'amala da su ba zai sa ka gudu da iyalanka daga anguwar nan ba?"

Malan Adamu ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" Shi dai zato zunubi ne, koda ya kasance gaskiya ne....., kai ka san Ni ba ruwana da jita jita malan Usman, to rayuwar nan ta yanzu ana ta gero ina za'a iya haɗawa da saka ido a abinda ba zai anfani mutun ba?, to kadara ma duka kaf abinda aka fada gaskiya ne, Ni fa Ni suka tardo a nan sai dai mutuwa ta dage Ni ba dai wai dan wannan abubuwan ba, in Allah yayi ta hanyar yanka zan mutu da iyalina fitar zan yi da nufin guduwa in tarda wukar, lamarin rashin ji kuwa da ake kira cewar ana yi a cikin gidan ai zamani ya kawo mu lokacin da sai dai ka bi yan ya'ya da addu'a da nasiha, domin lalata ta gama zaga duk wani lungu da sako da kake tunanin babu, sai dai Allah ya sawake....., haba bari wannan batu mu dibi girkin auntyn yara dan miyarta ta yau yada ka san ta kara kafi zakara dan ta ta yi dan karan zaki a ciki"

Dariya suka yi irin ta manya, shima malan Usman din ya bar zancen, domin dama shima mutun ne mai taka tsantsan sosai da kiyaye hakin dan adam, kawai dai malan Adamu ne ya zamo amini na kusa da kusa shi yasa har magana irin wannan ta shiga tsakaninsu.........daga nan sai suka buge da barkwoncin da suka saba har kiraye kirayen sallah ya tashe su.

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Tallah, tallah, tallah

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

*4*

A ranar nan maman yara bata shigo gida ba sai da ta fuskanci lokacin malan Adamu na iya shigowa gidan sa harma ya je dakinta dan nemanta ne ta shigo, haka kuma ta dawo ne fuskarta wasai kamar yadda ta sake dauro damarar abinda yake zuciyarta , domin tana zuwa ta dinke a daka da ƴaƴanta ta sake musu wani shirin na kalaman da a yau da ace ta kula basu da mugun tasiri a kan wace ta haifa din ma wato A'isha bale kuma Imtee, sai dai kasancewar yara ne masu biyayya sun saurare ta sun kuma jima a tare da ita har kiran sallar magariba ya sa suka nufi alwallah baki dayansu ba tare da ta takurawa daya cewar ya tashi yayi sallah ba, bayan a da sai ta yi ta surutun yin sallar karshe ma sai ta yi banza da imtee tace da ita tunda yarinya ce ita ta yi zamanta kawai..............., sai dai ta basar bata wani nuna mamakinta na ganin sun yi sallah ba tare da an saka su yi din ba ta ci gaba da zuba ido dan samun lokacin da ya dace ta yi nata abinda ya dace din.

Washe gari kusan karfe takwas na safe auntyn yara ta gama share balbalin gidan tasss ta shige wanka ta fito ta saka riga da zaninta sasauka sannan ta dauki litafinta ta zauna kofar dakinta saman tabarma ta shiga karatun addini a hankali muryarta bata tashi sama sama ama idan kana daf da ita kwarai zaka iya jiyo sautin karatun dake fita cikin nutsuwa da kwarewa..........
Chapter 6 · 0% Book details