← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 141

Sashe 21

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innalilahi, zaunewa ta yi ta shiga irgawa jiki na rawa , sai da ta irga dubu talatin cif a cikin ledar nan sannan ta bude wayar ta ciro ta ta ringa jujuyawa kafin ta dago tana duban Imtee dake kallonta a tsorace ta ce" Mama, na shiga uku, mama dan kin ce in amso ne na amsa, ko in mayar masa da abinsa???"

Da dan karfi mama ta ce" Ina? Ki mayar da me? Innalilahi Imtee ai kudin nan sun gama shigowa kuma sai dai su fita ta kashi idan mun yi daga Ni sai ke"........

Sai kuma ta sauke muryarta sosai kasa kasa ta ce" Zauna mana imteena "

IMTEE ta zauna du a darare

Maman yara ta ce" Tabbas na haifi y'a mai farin jini, kwarai nima wata rana sai na yi fice........, wai bai wani damu ba ya baki abubuwan nan yau kadai?"

IMTEE ta gyada kai tana kallon maman nata

Maman yara ta ce" To ki ji da kyau, ladabi da biyayya, yi na yi bari na bari tsakanin ki da shi, domin wannan idan ya kubce mana ai mun shiga uku.......wai tsaya ma, bai ce yana so ki zama matarsa ba?"

IMTEE ta sauke ajiyar zuciya, ita du abin wani iri take ganinsa, sai dai ai mamanta ne, ta tabbata ba zata taba sakata a muguwar hanya ba, ba zata cutar da ita ba, kuma ai tana da gaskiya idan ta masa gardama ko rashin kunya tafiyarsa zai yi Shikenan...........

A hankali ta ce" Yace wai yana so ya fara zuwa zance....." Ta karashe tana rufe fuskarta dan nauyin da ta ji maganar ta mata a bakinta

Maman yara ta rangada guda, lokaci daya tana rufe bakinta ita din ma ta ce" Ban mu kashe......"

Ta riko hannun IMTEE suka taba

A hankali ta ce" Bar min ragamar nan, in sha Allah yau da dare zan yiwa babanku maganar kin yi masoyi yana so ya fara zuwa zance, dan so nake yi ke da shi ya zamo zumuncin ku ya yi gaggawar zamowa aure, maza je ki yi wanka ki zo ki ci abinci ki huta da ranki, kai Allah na gode maka, bakinki shiru kar ki yarda ki bari kowa ya ji maganganun nan"

IMTEE ta ringa gyada kai, a hankali ta shiga cire tufafin ta, sannan ta dauki zanin maman nata ta daura ta fice ta nufi bayi

Tana fitowa aunty ta sake raka ta da kallo har ta shige bayi, haka kawai jikinta ke bata da wani abin dake faruwa, sai dai ba zata tambayeta a yanzu da mama ke gidan ba

Wanka ta yi ta fito

Har zata shige daki kunnayenta ke jiyo mata kiraye kirayen sallah

Haka kawai ta ji amon kiran sallar tamkar ana tura zuciyarta wajen yin alwallah ne

Lokaci daya ta kuma tuna dadin katifa da barcin da zata yi dan ta huta sosai, ......har zata shige dakin ta ji Muryar aunty a tausashe ta ce" In cika maki buta ki yi alwallah?"

IMTEE ta juyo da sauri ta zubawa aunty ido

Aunty ta ɗan matso, kasa kasa sosai ta ce" Kin san sallah itace aikin da za'a fara tambayar bawa a cikin kabarinsa idan ya rasu......, zan so ace sallar ki ta yi kyau, dan ki samu rabauta NUR"

IMTEE ta kifta idannuwanta a hankali, sai kuma ta sake kallon auntyn yara.........

A hankali ta langwabar da kanta, a sanyaye sosai ta furta" Eh, bari in zuba AUNTY"

Auntyn yara ta yi murmushi ta koma wajen wankin ta, tana hangen ta ta cika ruwa a buta ta zauna ta shiga gabatar da alwallah

Har ta gama aunty na hankalce da alwallar Tata, ai kuwa ta yi ta dai-dai, dan tun ba yau ba take shiga sabgar alwalarta, cikin ikon Allah yau sai ta ga ta yi ta dai-dai, hakan ya sanyaya zuciyarta sosai

IMTEE na karewa ta sake duban auntyn yara, sai ta samu kanta da jin wani sanyi a c'
en karkashin zuciyarta, a hankali ta shige cikin dakin su ta je ta saka riga a saman zanin ta saka hijab ta kabbarta sallah ba tare da ta bi ta kan mamansu da kudin nan ke daf da sakata dumumuwa, saboda sai irgawa take tana shinshinawa, sai da Muryar A'isha ta yi Salama ta mike da sauri ta totse kudin ta boye hadi da nufar akwati ta saka kudin, sannan ta fito tana kwabar aishar da ta ce" O ashe gida kika yo kika saka nake cen ina nemanki ko? Sai ki gama ki fada min dalilin ki na zuwa gida bayan cewa Malama ta yi ki je ki koyi hadisin da aka koya mana ki kawo harda, wallahi idan baki maida hankali a kan karatu ba Allah sai na hada ki da aba!"

"Ki hada tan, nace ki hada tan, aikin banza kin ga A'isha zan saba maki a kan yarinyar nan, idan har kika bi layin yan bakin cikinta a gidan nan tabas sai na daga maki hankali dan du mai neman tadawa yarinyar nan hankali da Ni yake magana, kin ga idan na ga takura mata zaku yi makarantar nan tsaf zan soke ta, in ga ta tsiya, wace irin masifa ne Ni a gidan nan da ake son takurawa karamar yarinya? Aikin banza kawai!" Maman yara ta katse A'isha rai bace tana ta fada sannan ta suri hijabinta ta zurma ta sake hararan A'isha ta ce" Zan je in dawo, saura ki sake shiga abinda ba'a saka ki ba, aikin banza ke kam idan na yi sake wata rana sai kin hada kai da makiyan mu a gidan nan!

Jikin A'isha ba karfi ta bi maman da ido har ta bacewa ganinta sannan ta nemi waje ta zauna dan tana halin périod ne ita, shi yasa ma bata yi alwalar ba, zuciyarta cike da tunanin me kuma aka yi haka? Me yake faruwa? Idan mama na maganar makiyan su sai ta ji kalmar ta yi tsauri da yawa, a gidan nan yaya za'a yi ace sunna da makiya? Allah ya kyauta

IMTEE na gamawa ta mike ta karaso inda take da litafin Fa'iza a sanyayen itama ta ce" Ba guduwa na yi ba saboda harda A'isha, hasalima na shanye hardar, wani abu ya faru na tsotata, to na fito kuma sai na hadu da yaya Anas shi ne ya kawo Ni ma, kin ji abinda ya faru"

Nan ta kwashe komai ta shiga labartawa A'isha har abinda ya faru tsakaninta da Anas da yadda mama ta ce

Gaba daya A'isha sai ta rasa kalmar fada na tsayin lokaci saboda abinda take son fada din bata sani ba ko zai zamo alkhairi ko fitina idan kanwar Tata ta ji????

Ama ba zata taba iya yin shiru ba

Ba zata iya kawar da kai ba

Dan haka a tausashe ta ce " Imtee, kudinsa kika amso da ƙatuwar waya?"

IMTEE ta lumshe idannuwanta tana jin kirjinta na son yi mata nauyi, ta mike tana cire hijabin nan ta ɗan dafe gaban goshinta a hankali ta ce" na san me zaki ce, cewa zaki yi yaushe ma muka hadu har da zan amshi abin hannunsa? Cewa zaki yi in ji tsoron mazan zamani, ba duka suke yin kyauta dan Allah ba, yawanci idan suka baka sai sun ciri abinsu a jikinka, cewa zaki yi idan har na yarda na gina mu'amalata da shi ta sigar kwadayi tabbas wata rana sai ya zage Ni da abinda kaina ba zai dauka ba, cewa zaki yi in mayar masa da abinsa idan so na yake yi ya bi hanyar da ya dace sannan ya tanadi dukiyarsa ya aure Ni!"

IMTEE ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya, A'isha na kallonta, a hankali ta ce" Abinda zaki ce kenan ko?"

A'isha ta yi dan murmushi ta ce" Ni ai ban yi magana ba!"

IMTEE ta girgiza kai tana jinginuwa da garu ta ce" Na san kalaman dake cikin zuciyar ki tun kafin ki furta......, ina gane abinda kike nufi koda baki fada ba......to Ama yaya kike so in yi ne? A'isha ta ina zan fara ne? Ke kin san tana so na, kuma ba zata taba saka Ni a hanyar da zan lalace ba......, ita ce ta rungume Ni ta kaunace Ni ......inada wanda ya fi ta ne?????"

Jikin A'isha ya yi mugun sanyi, ita da kanta lokuta da yawa takan shiga halin tunanin rayuwa da son samun amsar tambayoyinta a zuciyarta.....
Ba dai duka, ba kuma zagi, Ama wani sashi na zuciyarta ke fada mata cewa kamar ana zama irin na kisan mummuke ne a cikin wannan lamari....., ya Allah kai kadai ka san abinda ke boye a tafiyar nan, Ubangiji ka sakawa wanda ake cutarwa , ka sanyaya zuciyar uwa, ka gyara lamura.

A'isha bata ce komai ba sai shigewa da ta yi daki ta tube ta bude littafin nan ta shiga karantawa, domin ita dama ta fi Imtee maida hankali sosai a harkar neman ilimi.

Ana daf da magariba mama ta dawo da farin ciki harma ta shiga gyare gyaren filin gidan dan ta gama samo hanyar da zata fuskanci baban yara a kan maganar nan.

Lokacin da ya saba shigowa ya shigo, sai dai irin yadda ya samu maman yara a filin gida tana ta shagalinta sai da ya shaku da mamaki, Ama bai nuna ba, hasalima sai ya saje ya zauna aka ringa labari da shi bayan ya sa auntyn yara fitowa ta zauna cikin su

Sai da dare ya dan latsa maman yara ta kori Yan matan sannan ta fuskance shi ta ce" Baban yara ina din yin magana da kai"

Baban yara ya dubeta, kafin ya ce" To to to Bismillah," a kasan zuciyarsa kuwa yana jin tsoron korafi ne zata kawo masa kuma, bayan ana zaune kalau.

Auntyn yara ce ta motsa da alamun zata yi tafiyarta dakinta, sai baban yara ya ce da ita ta dawo, dan ba zai so ya daga murya kirawota ba, dan ya tabbata maman yara cewa zata yi ta yi mata wani laifin, ya fi so su yi su gama dan har ga Allah shi barci ma yake ji.
Chapter 21 · 0% Book details