← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 141

Sashe 84

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karashe yana sake dan buga gefen kafadarsa sannan ya juya zai nufi wajen motar ne ya hango su sunna magana, sai ya dawo ya sake zuba masa ido a tausashe ya ce" Sannan ka kula, ka daina kula mata a wajen aikin ka, kuma ANAS ba kowace mace bace ake tsarewa a titi, kar ka yi makacewar da zaka ka rigimar da ta fi karfinka, wani filin ba na yara bane na manya ne, kar ka zama mai duhun kan da zaka janyowa kanka fitinar da ba zaka iya tara ba.......ka yi aiki da hankalin ka, ka nazarci abinda yake faruwa .......ta haka zaka fi samun abinda kake so a wajen aikin ka!"

Daga haka ya sake kai dubansa ya ga sun rufe office din kafin ya juya ya koma ya tsaya yana duban hanya

Anas ya jima kadan yana tunani , tunda ya cewa Aliyu wai a kan me zai ringa turke shi kamar shi ne mai gidansa, Aliyun ya tabbatar masa cewar shi ne mai gidansa, kuma yana daga masa kafa ne kawai dan OGA ya nuna kar ya masa komai, ko me zai yi ya masa uzuri ya koyar da shi aiki, sai bakin shi yayi tsit ya bi bayanshi da ya janyo shi nan suka yi magana..........

To shi du kansa ya daure, kwarai ya san yana da dan shashancin jira sai Anna ta kiraye shi ko FARHANA wani lokacin ya zo, Ama yau ai Anna da kanta ma tace kar ya je cen suna nan, kenan bai fita da wuri bane har suka fita???? Kai, ai kuwa zai ga maida hankali a kan aiki, in sha Allah in takamarsa sauko shi sai ya nuna masa a hanya yake kwana......, kuma maganar kula matan nan da yake yi ya tabbata dan ya ganshi sau biyu kawai a kofar makaranta suna magana da Na'ima ne yake fadin haka, to shi ai gaisawa kawai suka yi sai maganar yaushe zai je gidansu da ta masa yace zai je , daga wannan ai bai ganshi yana wani abin da zai je ya daina kula mata ba ko? Ko me yake nufi ne????, hum in dai Na'ima ce zai daina kula ta a nan zai tarda ita gidansun dan ba daina waya suka yi, kawai dai ya fada mata ne in dai tana son shi to ta yi hakuri har a gama maganar Nur kawai.
Bayan ya gama tunaninsa komawa ya yi shi ma kusan motar da yake ja ya tsaya yana hangen Aliyu hadi da tabe baki............a ransa ya ayyana 'zaka yi bayani, kwontan bauna nake maka, sai na raba ka da aikin nan, in dai kaki ne Ni ma zan roki oga a min hanya idan ya so sai in ga ta daga kai!'

Su HALLAH da suka sake shiga office din na Anna, a yanzu bata je inda Anna take ba, sai A'isha ce ta je ta gaisheta ta hanyar dukawa hadi da gaishe shi shi ma, domin dazu bai tsaya a wajen ba da ta gaishe shi.

Amsawa suka yi, Anna da kula sosai, shi kuwa a yanzu bai bude idannuwan nasa ba yana dai rike da hannun Anna a saman lebensa ya furta " lafiya" kafin yayi shiru.........., yau din nan du baya jinsa dai-dai, ga kuma jikin Anna, ga na MAZNA da ya baro, wace fir ta ki ya kaita asibiti, tace ta warke......shi dai abu daya ya fada mata ta duba abinda yake damunta idan tana da bukatar wani taimako ko wani iri ne ta fada masa, Ama ta sani a gabar da yake yanzu in ba dole ba yana da bukatar ta Dube shi!

Zaunawa Hallah ta yi saman cafet a hankali ta ajiye jakarta a gabanta sannan ta bude ta ciro litafinta da byro kawai ta bude ta shiga rubutu a hankali ba tare da ta kara cewa kowa komai ba

Anna dake duban FARHANA tana sakata harhada mata wasu takardun da take son dubawa na daliban sabodo za'a kwana biyu ba'a zo ba ta dube shi a tausashe ta ce" Yanzu nan da sati ana gama shafa fentin nan na ko'ina?"

Du idan Anna ta fara magana, yakan bude idannuwansa ne ya bata hankalinsa, hakan ya sa yanzu ma ya bashi hankalinta ya ce" Eh, zasu gama komai"

Anna ta gyada kai a tausashe ta ce" maganar korar daliban da basu da kwazo a harkar karatun nan ina so ka duba mana"

A hankali HALLAH ta sauke dubanta a kansa gabanta na dan faduwa cike da tunanin maganar nan na nan Kenan?, to ai idan maganar nan na nan tana cikin farko farkon wa'inda za'a kora a makarantar nan, innalilahi

Anna ta ɗora da fadin" Zan so a basu dama, koda wata biyu ne a kadaice su, a musu lesson na kirki a tsaurara a harkar nasu karatun a gani, idan an ga wasa ne kawai ke hana wasun su yi sai a musu uzuri a tallafa musu , ta haka za'a taimaki yaran nan sosai, kuma a taimaki iyayensu da suke zuba musu kudin neman ilimin nan "

Kai HALLAH ta gyada a ranta tana ayyana ' Eh wallahi Anna, dan Allah kar ki yarda ya ci zalinmu....., shi kam wannan kamar ba danki na cikinki ba, mutun sai fada da keta? Sam bai yi sansanyan halinki ba Annata'

A tausashe ya ce" In sha Allah za'a yi hakan....., ama idan na fara koyar da su, ba zan yiwa wanda baya son a yi masa uzurin ba"

Ido HALLAH ta fitar a hankali ta furta" Mun shiga uku, kai kuma?"

Anna ma da mamaki ta ce" Kai zaka dauki horon nasu?"

Idannuwansa ya lumshe yana gyada kai kafin ya ɗora da fadin" Hatta tantancewar ina nan za'a yi, Anna, ina so makarantar nan ta zama ta farkon da za'a iya zuwa Daga wata ƙasa ma dan a yi karatu a cikin ta, ina so daliban makarantar nan su zama daban koda karatun shekara daya suka yi a cikin ta......, "

Ya dan kai dubansa bangaren da sam bai san a nan yarinyar nan take ba, sai dai yana kaiwar suka sake yin ido hudu da ita a lokacin da ya ce" Bama bukatar wanda bashi da kokari Anna........"

A hankali ya dauke idannuwansa yana lumshe su sakamakon sake dokawa da zuciyarsa ta yi ya dubi Anna a tausashe ya idasa da fadin" Du Wanda ba zai amshi second chance din da zan bashi ba........ba zaki dauke shi matsayin bata garin ɗaliban ki ba Anna"

A hankali ya kai hannunsa saman agogonsa ya shiga murzawa yana sauke ajiyar zuciya cike da tunanin tabasss shi ne ya dace ya je ya ga likita, bashi da lafiya......kwarai bashi da lafiya.........

Anna na murmushi ta ce" In sha Allah du zasu maida hankali, in sha Allah zasu kara dagewa......."

Ta kai dubanta kan Nur da A'isha ta ce" To ku tashi mu dauki kayanmu mu tafi gida"

Mayar da litafin Nur ta yi zuciyarta cike da tunani ta mike ta kama jakar computan da FARHANA ta miko mata , su kuwa suka dauki wasu kayan, suka nufi waje , a lokacin ne shi kuma ya kama Anna yana rike da ita a hankali ta ce" Andadi zan iya tafiya da kaina fa"

Murmushi yayi ya gyada kai, sai dai bai sake tan ba, yana rike da ita har suka fito wajen su ma

A lokacin da suka fito, sai kawai idannuwansa suka sauka a kan yarinyar nan, Anas ya bude mata gaban mota tana saka computer , domin ita ta saka daga karshe bayan su Farhana sun saka nasu kayan na hannayensu , ya zamo da ta saka din ta rike hannun motar tana kallon Anas bayan ta ɗan shagwabe fuskarta ta ce" Ya dace ka fada min abinda yake damunka, domin yanzu ya zama abinda yake damu na"

Anas ya dube ta, a hankali ya ce" zan zo gida, ko idan muka je yanzu in ba wani aike zan yi kiran FARHANA ta fada maki ki fito , sai in sanar maki, kwarai ina so mu yi maganar dan abin na neman daga min hankali"

Ikon Allah kawai Aliyu yake kallo , domin har ga Allah gani yayi yaron nan ya raina masa wayo.....

Shin ba yanzu ya gama masa magana ba? Ko dai bashi da hankali??????

Kai Nur ta gyada sannan ta dakata saboda yau Farhana ta rigayeta shigewa karshen mota, wato zaman tsakiya ya kama ta dole......haka kuma zasu dan matse saboda an saka kaya a kujerar gaba, kaya ne masu mahimmancin da ba za'a saka su Boot ba, harda wayoyin yaran da du Anna zata nemi iyayensu a cikin wata jaka.... A ganinsu kayan ba zasu shiga Boot ba shi yasa du suka ajiye kayan a kujerar gaba kawai.........., Ama Anna bata san da haka ba

Dakatawa ta yi kadan, ta ɗan sada dubanta a lokacin da ya karaso wajen motar, ya zamo Aliyu ya iso ya bude, sai ta ɗan matso dan ta shiga tsakiya kafin Anna din ta shige , a nan ne ya ga to ai su biyu ne a bayan, idan biyu suka karu sun zama hudu, duda ba rasa wajen zama zasu yi ba, ana iya dan takura kafin a isa gidan

A hankali ya riko Anna a tausashe ya ce" Wajen ya muku kadan"

Anna ta dubi motar, sai ta dubi yan matan ta ce" Au, Nur ke shiga gaba ko? Sai mu wadatu........."

Da girmamawa Anas ya ce" Yauwa bari in mayar da kayan Boot"

Aliyu ya dube shi ya ce" A'a, ka bar su, ba za'a tsayar da su ba har a mayar da kaya Boot, ita ta shiga wancen motar sai mu tafi"

Dubansa IMAD ya yi da dan saurin da bai san ya yi ba, kafin ya sake riƙe hannun Anna a hankali ya ce" Anna, mu je"

Ita da kanta Nur sai ta ji wani sanyi ya ratsa ta saboda har ta Tsorata wallahi, haka kawai bata son abinda zai hada ta da mutumen nan domin ba zata so ace ta yi wata rashin kunya ba, bayan idannuwanta na gane mata kamar kyamar ta yake yi

Aliyu a dole ya bar motar ya karasa ya bude IMAD ya saka Anna a nan kafin ya shige shi ma
Chapter 84 · 0% Book details