← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 141

Sashe 26

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AUNTYN yara ta lumshe idannuwanta, nauyin da kirjinta ya mata a hankali ya ringa raguwa......saboda ta zata wannan fitinar da aka tada da irin abinda sulaimana ya yi idan ran Malam ya kiya sai ta raina kanta, sai ta ga abin ya zo da sauki ma

Da kula Malan ya ce" Su kuma kayan nan na menene?"

Sai yanzu Imtee ta iya budar baki muryarta a raunane ainun ta ce" Baba, Babar malamar mu ce ta bani, mai makarantar nan......"
Nan ta kwashe dukan abinda ya faru ta sanar masa

Da mamaki ya ringa duba kayan karatun daya bayan daya harda jakar

Ya dubi AUNTYN yara, itama ta Dube shi kafin ya hade ya zuba a jakar ya ce" Allah ya saka mata da alkhairi, Ama ba zan baki ba, sai na je na ji abinda yake faruwa, idan ba wata damuwa shiKenan sai in baki, kuma kafin in baki sai na tara na siyawa y'ar uwarki irin su, kin ga sai kowa ya yi anfani da nasa"

Kai suka gyada su duka, kafin ya dubi bangaren dakin maman yara ya sake duban su

Sosai yake son cewa Imtee ta je dakin mahaifiyarta, sai dai bai sani ba, yin hakan ko daidai ne? Domin kuwa ji yake yi a ransa kamar ba'a kyautawa maman yara ba, duda ta bashi mamaki ta bata masa rai ainun, Ama a kan Imtee kam sai a mata uzuri, shi da kansa ya san tana son yarinyar, kawai ita dai bata iya bacin rai bane maman yara

A tausashe ya ce" Ku tashi ku je wajen mamanku, ku bata hakuri ku rarasheta kun ji? ALLAH ya muku albarka"

Mikewa suka yi su duka, AUNTYN yara kuwa lokaci daya ta ji kirjinta ya sake daukan zafi

A hankali ta mike ta nufi dakin ta ta silale ta fashe da wani kukan

Jiki na karfi baban yara ya bi bayanta

Yana shiga ya karasa ya duka inda ta kwonta ya kama hannunta ya ce" Subahanalah, Subahanalah AUNTYN yara, ya Allah, dan Allah ki yi hakuri, na san cewa ba'a kyauta maki, na san cewa kema mutun ce kuma kina da zuciya a kirjinki, na san cewa sam maman yara bata kyautawa kanta bale ke a maganganun ta, Ama dan Allah ki yi hakuri, ki mata uzuri, dan Allah ki yi hakuri, shine kawai abinda zan iya cewa saboda ko Ni ta daga min hankali yau, maganganun ta sun bani mamaki, Ama kin sani dama ita idan ranta ya bace komai fadi take yi, ɗan Allah ki gafarta min kin ji?"

A hankali AUNTYN yara ta ringa jin nutsuwa na dan ratsa mata zuciya, ba dan komai ba sai ganin yau da gobe yau har baban yara ke fadin cewa matarsa bata da kirki idan ta bude baki? Hakan na nufin wata rana idan da rai da lafiya gaskiya zata yi hakinta? Ai kuwa a hankali ta budi baki ta ce" Ba wannan nake yiwa kuka ba baban yara, abinda ke damuna Sulaimana ne, ka duba ka ga a yanayin da yake yau fa, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, baban yara dan Allah ko kauye zaka mayar da shi ne inda ba zai ga abin bugarwar ba?????"

Malan ya sauke ajiyar zuciya cike da tausayinta ya ce" Ai na raba ki da kauye, a cen din ma akoy, kawai lokacin in jajirce da nema masa taimako ne yayi inaga, saboda ga dukkan alamu fada da tsarewa ba zata yi ba, kin ga ko'ina zan je muna tare fa, ba dare ba rana, Ama yanzu kam na fahimci lalle dole in nemi taimako wajen masana, ki yi hakuri ki yi hakuri in sha Allah zai bari,"

AUNTYN yara ta gyada kai tana sauke ajiyar zuciya

A hankali malan ya ce" Kin amince a yi bincike kan mai neman auren nan na yarinyar nan?, ko kuwa kawai in dakatar da shi idan bai maki ba?"

Mamaki ya kama AUNTYN yara, cabdijan Iyeah?????, eh lalle ,

A hankali ta ce" Malan, na yarda cewa babu wanda ya isa ya gane wanda ya dace da NUR sama da kai, idan ka ga shi ya dace da ita Allah ya tabbatar mana da alkhairi kawai......"

Malan ya yi murmushi ya mike yana fadin" Amen, Iyeah su AUNTYN yara da sirikai....."

Ai kuwa da sauri ta sada kai cike da jin kunya, shi kuwa ya fice yana dariyar kunya irin ta aunty yara ga kuma rigima.

Su Hallah da suka samu maman yara a daki du yadda suka so ta sauko ta yi hakuri gagara ta yi, karshe ma sai wrng ta kashe musu cewar su barta ta huta, ba abinda ke bata haushi irin yadda A'isha sam ba zata taba yin fushi idan ta ga ana wulakantata ba, Gayanan yanzun ma kafarta, kafar Imtee......hum!

A dole suka zauna suka yi shiru kamar yadda ta bukata suka bata space,

Tana hankalce da dukan abinda yake faruwa har malan ya fita sannan ta saka hijabinta ta bude ta ciri dubu daya cikin kudin nan na wajen IMTEE ta fice ba tare da kowa ya san inda ta nufa ba

Ba wani shirin kirki, ba wani suturar kirki, ba dan kanshi kanshi ta ringa fakar ido har ta dauki hanyar gidan su Anas, domin gidan su ai ba boyayan wuri bane du an san shi

A lokacin da ta zo gidan ta samu maman su Fa'iza ce kawai da wata budurwa na zaune tana dan dana waya ta sha mak'up a fuskarta , gefen ta kuwa wani kwondo ne dauke da kwanoni masu shegen kyau da kuma fruits

Amsa Salamar maman su Fa'iza ke yi tana zuba ido da son ganin mai shigowar harma da son gane ko wacece dan ita bata wani santa ba

Saman kujera maman yara ta haye tana ta kale kale da jinjinawa a ranta kafin ta sauke dubanta kan maman su Fa'iza da ta fara tunanin ko dai ba lafiya a kwakwalwar Allah ya jefo musu ita? Domin har ta fara alamun yiwa yarinyar nan alamar ta tashi ta shige ciki idan ya so ita sai su karata da mahaukaciyar, dan yarinyar y'ar gidan Elhaji zakari ce yarinya mai kirki da son ANAS, yanzu haka da ta zo sai da ta mata kofarin bata san laifin da ta masa ba yanzun ya zama baya son kula ta, ko a makaranta baya son kula ta, ita kuma tace da ita ta yi hakuri ta yiwu aiki ya masa yawa, ta yi jiransa kawai du inda yake ya kusa shigowa, shine fa ta ba Fa'iza kudi tace ta je ta karbo mata gasashen nama mai yawa da lemon gwongwani, domin ita haka kawai Allah ya saka mata kaunar yarinyar a ranta, ta sani cewar itace ta dace da d'anta ba wannan yar gidan kikitakan anguwar ba.

Mama na washe baki hadi da dan sosa kai ta ce" Hajiya na san baki gane Ni ba, Ni ce maman IMTEE"

Gaban maman Fa'iza sai da ya fadi, lokaci daya ta hade fuska hadi da kallon Budurwar nan ta ga itama maman yara take kallo, hakan ya sa dole in ma meye zata ce zata fada a gabanta dan in tace su fita yarinyar na iya tsarguwa ko ta yi tunanin bata yarda Bama da ita ai

A hade ta ce" Wacece IMTEE?"

Maman yara da mamaki ta Dube ta ta ce" IMTEE fa, ita da A'isha, kawayen yarinyar ki Fa'iza, wace yaron ki ke so din nan!"

'innalilahi gaja, ido da ido yau na ga gaja, janyin jau, wannan din fa????' Maman Fa'iza ke fada a zuciyarta, a bayane kuwa ta yi gaggawar fadin " To fa, ka ji bayani dala dala a bakin mai shi, ai ke ce ma IMTEEn wani suna ba tsari, budurwar ANAS dina ta wuce Na'ima gatanan?"

Ta dubi Na'ima wace ta saki wayarta a jikinta tana kallon maman yara a dan tsorace, dan kuwa wa'inda ta fada din ita ai ta san su idan maman Anas bata san su ba, sai dai bata san maganar soyayya a ciki ba, soyayya?

Maman Fa'iza da niyar bangarar da zancen ta ce"💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

TALLAH, TALLAH..... BISMILLAH

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data
*15*

Maman Fa'iza da niyar bangarar da zancen ta ce " Ke Na'ima ki ji wani shashanci dan Allah, Malama kin ga tashi maza ki Bara min gidana tun kafin in nemo masu iya fitar min da ke su rabani da ke dan alamu sun nuna ba ras kike ba"

Maman yara ta yi tsuru tana kallonta ranta na tafasa, lokaci daya tana jin ta muzanta fiye da kima

Mikewa ta yi ranta bace ta ce" Au, kenan ke ce baki da labari, saboda shi yaron naki shi yake kai kawo ina korarsa, dama na biyo ne dan in sanar masa wata maganar da ta shafe shi mai mahimmanci, tunda lamarin na rashin girma ne ai shiKenan, aikin banza aikin wofi!"

Daga nan maman yara ta dauki hanya ta fice ranta na sake kuna

A filin gidan suka hade da Anas, wanda shi sam bai santa ba, ama leke leke irin na maman yara tana shawo kwana ta gane shi, lokaci daya ta dakata ta ce" sanu da shigowa........"
Chapter 26 · 0% Book details