Sashe 63
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maman yara ranta bace ta Dube ta ta ce" Rahama, to sai me dan kin daina ganin mutuncina kin zage ni? Ai ba yau kike zagin nawa ba, .....to sai ki fadawa wanda ya san wata hanyar sama da ke a gidan nan, ke da dama ba shi ne mijinki na farko ba? Malan ai saka aka yi ya aura, wa ya san me ya auro min?, to ki ji da kyau, daga ke har shi nima ina da tabbacin tawa y'ar tasa ce, Malama da har zaki zo mana da mugwayan kalamai a nan na cewar wai a je a yi awo, awon me da ya wuce rantsuwar dan musulmai?, zan iya rantsewa Malan da du abinda yake so a duniya cewar A'isha yarsa ce, aikin banza aikin wofi, munafurcin banza munafurcin wofi, har Ni za'a kawowa zancen banza cewar y'ar nan ba ta Malan bace? A gidan nan wa ya kaita nutsuwa ne? A gidan nan waye ya kai yarinyar nan NUTSUWA nace?"
Sai kuma ta fashe da kuka tana ta kale kalen mutanen wajen, a dole so take yi ta wannan yanayin a gane ita ce wace ta fi kowa gaskiya ciki harda auntyn yara
Ta dubi Malan ta ce" Dama na san tun daga danginsa har abokinsa mafi kusanci ya tsane Ni, da ba dan haka ba da ba zaku janyo masa aure da karfi da yaji kan sai ya min kishiya ba, yanzu bayan tsayin shekarun nan ne kuma za'a bi Ni da shari? Ni ba mazinaciya bace!"
Malan rai bace ya nunawa mama yatsa ya ce" Ke ta Ahmadu ki fita idonna in rufe, ki kiyayeni a nan!, daga fadin magana kin bi kin hayayako min me kike nufi da Ni?, aikin banza aikin wofi, to kuwa ki ji da kyau da kunnen basira magana karya kike ta tsaya a iya rantsuwarki, rantsuwa? Allah na tuba Ni zaki ajiye ki ce zaki rantse in yarda? Sai dai ki yiwa mijinki wannan shashancin ba Ni ba, kai Ahmadu ka fada min da ta yi goyon ciki ka ga motsin ciki a jikinta? Idan matarka nada ciki dai ai kai ne mafi kusancin sanin hakan......, ku ji gaba dayanku daga ke har ke, idan har ya tabbatar min kwarai ya rayu da motsin cikinku a idannuwansa da jikinsa sai ku kawo min takardun awon cikin yayanku, daga nan idan su din ma na yarda sai mu je asibitin da kuka haihu, idan ma a gida ne sai na nemo ingozomar da ta amshi haihuwar, idan shi din ma kun tabbatar min da abinda nake tunani sai in daukaka maganar zuwa gwajin, dan kuwa ku ji da kyau na yarda da komai banda batun SULAIMANA da A'ISHA jini daya ne, da niyar zama a gidan nan adadin shekarun da ya dace har gaskiya ta bayyana na zo, Ni da ku gagarare ya ci kaniya tai! Aikin banza!"
Ya karashe yana nuno su da mugun fadan da dama suka sanshi da shi, da zage zage
Sulaimana da kansa ke ƙasa cike da tsoron bacin ran mahaifiyarsa wanda ya tsaye masa a rai fiye da kulun ne ya dago a tausashe ya ce" Baba, dan Allah ka yi hakuri ka bar maganar nan, Ni fa tunda na tashi na san A'isha yar babanmu ce, nima kuma na yarda cewa Ni dan babanmu ne, dan Allah ka bar maganar hakanan mu je kawai, Ni maganar cen ma kwarai shaye shayena ne ya haifar min da haka , ka yi hakuri"
Malan ya saka hannu ya dungure shi da mugun karfi yana fido ido ya ce" Ka zata maganar a iya kai ta tsaya? To ko ubanka bai isa ya raba Ni da matansa ba sai gaskiya ta bayyana!, kai yanzu ka daina jin son nata a ranka ko yaya?"
A hankali ya saci kallon A'isha da ta dunkule ita da IMTEE waje daya kanta a saman hannun IMTEE jikinta na mugun rawa......
Tausayinta mai girman gaske ya kama shi, da wata irin soyayyar ta wace ya ji kamar ya rikota ya tabbatar mata shi fa sonta ne yake yi, kuma in sha Allah shi zai zama gatanta a nan gidan duniya
A hankali ya soke kai, hakan ya sa baban yara kaiwa tsugunne shima yana kallon su maman yara
Gannin haka ya sa auntyn yara fashewa da kuka saboda kirjinta ya mugun rike mata sannan ta nufi dakin ta da mugun sauri
Maman yara da jikinta ke rawa ta ce" Ahaf, ai marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, aikin banza kya fito ki fadi uban Sulaimana waye!"
Tana fada tana share gumi ne, IMTEE ta sake rungume A'isha a jikinta tana kallon mama, hawaye ya cika mata ido taf, hankalinta a mugun tashe take bin mama da wani kallo mai cike da tarin ma'anoni
Ko minti biyu auntyn yara bata yi ba ta fito da wata jaka bak'a ta duka a nan ta zazage duk wani abin dake cikin jakar mai mahimmanci wanda ke dauke da duk wani abin da ya shafi asibiti mai daraja tun haihuwar ƴaƴanta har zuwa yau!
Takardun awon su su biyun ya ciro ta ajiye a gaban Malan, sannan ta ciro takardun haihuwa, ta bude inda ake rubuta kalar jinin mutun......, sannan ta ringa bude takardun har ta ciro wasu biyu da suke hade ta mikawa Malan tana dubansa cikin ido ta ce" Wannan takardun da ka gani na haihuwar sulaimana da Hallah ne, wannan itace wace aka bamu ranar da aka haifi sulaimana ga kuma na Nur wanda shi ne ya koma ya saka sunna bayan sati biyu ya dawo da su......., Wannan takardun biyu da suke hade kuwa shekarar da SULaimana yayi rashin lafiya ce wanda aka rike mu muka yi kwana arba'in da bakwai a asibiti....., dalilin rashin lafiyar ya bukaci jini wanda uban ya je aka masa gwaji aka ce irin jininsu guda aka zuga a nasa aka ba yaron nan ......., idan du basu isa ba bani da ja , a daukaka karar nan inda ake so kwarai zamu je da yaran nan baki daya, Ni ba fasika bace, kuma ban dauki d'an kowa ba, Ni na yi rainon ciki a gidan nan ko kai baka sheda ba????" Ta karashe tana duban baban yara da hawaye ya cika idannuwansa
A raunane ainun ya dubi Malan bayan ya dubi su IMTEE ya ce" Cikin Sulaimana ko na Hallah, kwarai na tabbata motsin su a cikin mahaifiyarsu, kuma Ni na kai ta asibiti a haihuwar nan biyu da ta yi gaba daya ......."
Ya yi shiru, kafin ya sake duban su A'isha ya kamo hannayen A'isha ya matso da ita daf da shi sosai ya rike hannunta daya da karfi ya jimke a nasa hannun, hakan ya sa Nur rarafowa itama ta rike dayan da karfi a nata tana sake shafa bayan A'ishan, yana duban maman yara ya ce" Na A'isha ban ga motsinsa ba, ama na ga tulinsa a jikin ki,......wasu lokutan nakan ce da ke kamar cikinta yayi sama sosai a jikin ki gwara mu je asibiti kar aje wani abin ne? Sai kika ce ke Bakya son harkar asibitin nan, kawai kashin kudi da bata lokaci ne, ....................., wani lokacin kuwa sai in ga yayi kasa sosai har nake ce maki ko dai bakwaini ce? Tunda a haihuwar sulaimana da ta kusa haihuwa cikin sai ya ringa yin kasa kasa kadan, gashi ke a lokacin baki kai haihuwa ba........., Maman yara tun lokacin da na ribaci zama da ke wanda rabon A'isha ya samu baki kara duban kofata ba ko da wasa har kika haihu kika yada wanka da komai baki Dube Ni ba, ban san yaya lamarinki yake ba, na san dai kin ce min kin karu sosai ana maki gashi irin namu na Hausa sai kin samu kanki, a kadan sai da A'isha ta fara rarafe sannan kika san kofar dakina....."
Ya dan ajiye maganar yana kallon fuskar A'isha zuciyarsa na sake tsintsinkewa, irin kallon da take masa da shi mai kuka da kururuwa ne da yayi ko zai ji sanyi a ransa......, kallo ne irin na kamar zata zauce, idan kuma ya kalli Nur sai ya ji duniyar ta masa zafi, yannayin fuskar NUR kamar wace ke cikin firgicin ganin bakuwar halittar da bata taba gani ba, hawaye kuwa wani ke korar wani, bakinta ya bushe dan sam bata iya shiga cikin tashin hankali ba.............................................................
A hankali ya dubi Mama ya ce" Harta haihuwar a'ina sai da kika zarce watannin haihuwar ki, idan kina tune a'i sai da ta shekare a cikin ki, idan nace gaskiya asibiti zamu je sai ki ce in yi hakuri lokaci ne in yayi zaki haihu....., idan kina tune wata ranar Laraba kika fita dan zuwa yawata kafar ki kamar yadda kike yi kullum, a lokacin ne kuma dai haihuwar ta kama ki, Ni dai ina nan sai zuwa kuka yi da baby cikin hijabinki, ke da kawarki kuka ce yanzu kika haihu, a lokacin idan kina tune ke da nace Subahanalah a ina haka? Cewa kika yi a asibitin dabe, ita ce ta ce wai asibiti dan kar in maki fada ne kika ce asibiti, ba a asibiti bane a gidanta ne......na yi na yi mu je a duba min lafiyarki ke da ita kika kiya kika ce ke kalau kike, maman yara da na nemi takardunta dan in kai asibiti in fadi suna a rubuta min cewa kika yi ke kam a barki da fi'ili irin na nasaru, y'arki a gida kika haifa ba sai an yi abubuwan nan ba, kawai a rada mata sunanta shike nan.........., idan har ban manta ba ai haka aka yi ko?"
Maman yara da jikinta ya kara rikicewa da rawa sai kawai ta hau balaki ba ji ba gani, har sai da Malan na Magarya ya mike ya aniya masifanceta fiye da kima
A hankali A'isha ta ɗora kanta a gefen hannun Aban yara, ta fashe da kuka mai zafin gaske
Jikinta na rawa sosai ta ce" Kar dai aje Ni ba y'ar babanmu bace? Na shiga uku na lalace, mama wanene babana ?"