← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 141

Sashe 93

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anna ta girgiza kai, tana dubansa da kula ta ce" Ko daya, ba wanda ke takura min, tun farko ya dace ace na sanar maka bai dace ka haɗa Ni zama da matarka ba, saboda sirikata ce, sam bai dace ace an hada zama sirikai ba, saboda ina iya zamowa takura a gare ta, ba dan ta nuna min ba ko ta min rashin kunya, a'a, ko daya, kawai lokaci yayi da ya dace ace ba gidanmu guda da matarka ba Andadi......, ku yi zamanku a nan, mu sai mu koma wani wajen, ko ku komawar ku plateau mu sia mu zauna a nan, ka ga sai mu ringa ziyartar juna"

Kasa ya kala, kafin ya sake duban Anna

A tausashe sosai ya ce" Anna, wace irin takurata, mu da ba falon mu daya ba, tsakanin nan da cen tafiya ce ba karama ba, .....?, Anna wace irin takura ce da yarinyar da sai ta yi kwana biyu baku haɗu ba ma?, yanzu hakan ai ziyartar taku ne take kawowa ba yar gidan bace saboda ina gani sai ta dau lokaci bata zo nan ba ko.....?, kuma Anna takura ? Anna yaya zaki ce da takura bayan ke , ke ce kike kula da Inna tun muna yara har zuwa yanzu? Ke bata takura ki ba????"

Anna ta zuba masa, sai kuma ta dauke kai ta ce" Ka ga, Ni ba wannan na tambayeka ba, haba yaya za'a yi ace ana jan magana da kai da girmanka? Inna ai Ni mamana ce, ba zata taba takurani ba!"

Yanzu ma wani mamakin ne ya kama shi........, ita Inna mahaifiyarta ce?, to ita MAZNA ba y'arta bace????

Sai dai yayi shiru, hasalima bayan yayi shirun ma sada kai yayi bai dago ba

A tausashe Anna ta ce" ka fahimce Ni, ina da bukatar ka kai matarka wani wajen , inda zata fi sakewa, kuma ba na fada maka haka bane dan ina nufin wani abu , ko ina nufin ta min wani abu, haka na tsara, plz ka kai ta plateau, idan kuwa cen ya mata kadan Ni sai in koma cen, zan iya hakura da nan din sai mu ringa zuwa wajen aiki muna komawa....."

Idannuwansa ya lumshe yana hadiye duk wata damuwar da yake ji a cikin ransa

A hankali ya kalli Anna , a tausashe ya ce" Anna, akoy wani abu da MAZNA ke yi na rashin da'a a gare ki?"

Anna ta yi gaggawar girgiza masa kai ta ce" Ba nace maka ba dan komai na fadi haka ba? Ra'ayi ne fa kawai"

Kai ya gyada a tausashe ya furta" shiKenan, in sha Allah zan duba........., "

Anna ta yi murmushi ta ce" Na gode sosai....., Allah ya maka albarka"

Murmushin yayi shi ma, wanda bai kai zuciyarsa ba ko kadan, sannan suka ci gaba da yin dan shirun har dai ya mike yana fadin" Anna bari in samu Aba da maganar, dan in sanar masa , kafin mu je mu samu shi saurayin nata"

Anna ta gyada kai ta furta" Hakan yayi, ni ma bari in je in dan huta, sai ka shigo"

Daga haka Anna ta nufi elevator, hakan ya sa ya zuba mata ido har ta shige ya rufe kafin ya koma ya zauna a nutse yana dafe gaban goshinsa da ya dau zafi

Abubuwa ne sun zo masa a tare suna neman daga masa hankali

Ya rasa me zai ce da maganar nan........

Maganar da ta zama ta burin zamansu tare a daf da shi ita da Inna?

Inna kan cewa ina so har in mutu ina ganin ka gefen mahaifiyarka ina so ka samawa mahaifiyarka sanyin idanniyar da zata kula da ita kamar yadda ta kula da Ni
Idan Inna ta zauna daga ita sai shi, takan ce ina da burin ganin macen da zata so mahaifiyarka kamar yadda take so na, ta hidimta mata kamar yadda take hidimta min....., idan yace to ba ga MAZNA ba? Sai tace hum, MAZNA ? Ai a kullum bakuwa take a gidan nan, MAZNA? Matar da ka zaba ce kai, Ama ina maka fatan zabin Allah......

Yaman ajiye haka a matsayin abinda Inna ta tsana fa kullum cikin hamaya take da shi......sai dai a yau hankalinsa na neman yi masa wani irin tashin da hankali ba zai dauka ba

To ai ko a lokacin da yake nesa da ita zuciyarsa na da nutsuwa da tunanin MAZNA na daf da ita, zata share mata kuka, yata rarasheta, zasu yi hakurin rashinsa a kusa da su a tare......

A hankali ya duba time a wayarsa kafin ya mike ya nufi bangaren Mama dan ya ga jikinta sanan ya fadawa Malan abinda yake faruwa kafin sallar la'asar kuma su fita shi da Aliyu Dan zuwa inda yaron nan yake.

A dakin Farhana kuwa, bayan sun gama cin abincin hade kwanonin suka yi a basket Farhana ta yi kiran mai aiki ta sauke su kicin ta wanke sannan suka shiga fira

Fira suke ta hankali, fira suke yi ta karuwa, fira ce ta karawa juna ilimi da wayewar duhun kai, wace a cikinsu kowace da kalar baiwar da Allah yayi mata

Farhana ce ta dubi A'isha ta ce" A'isha wai ke waye saurayinki? Ni ban taba ganin ki da saurayi ba"

Nur ta yi murmushi ta ce" Wa ta ba fuska? A rashin ba samarin fuskar da take yi gashi nan sulaimana ya balo mana aiki, Allah ya sa Malan na Magarya ya tafi da shi ai da mun ga fitina "

A'isha ta harareta tana duban FARHANA dake tambayar wai dama ba soyayyar suke yi ba?

Murmushi ta yi tana sada kanta a hankali ta ce" Anya akoy gayen da zan iya so sama da yaya SULaimana?"

HALLAH dake shan ruwa ce ta kware, tsakani da Allah ta kware ta shiga tari da kyar ya tsaya mata tana duban A'isha ido waje ta ce" me kika ce? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, wannan wani irin rashin sanin ciwon kai ne? SULAIMANA? Ke yanzu ko daura maki shi aka yi ai kya kunce ki fita da gudu, gidan duka, namijin dake dukan ki tun a waje zaki ce kike so, ina ke ina SULaimana?"

A'isha ta harareta ta ce" Kin ga bana son neman masifa , kuma wallahi kar ki saki ki zage shi ,kin san ba kyale ki zan ba, tam, kuma maganar wai wani wai mai duka ke da kanki kin san ni baya duka na, ke ce ke masa rashin kunya ya dake ki ke kadai, kar ki saki ki zage shi na fada maki"

Nur ta sake tafa hannu tana karkatar da kai ta ce" shiKenan, Ni kam zuwa yanzu zan fara yi maki addu'ar Allah ya yaye maki wannan damuwar ,saboda gaskiya kina cikin matsala, cabdijan "

FARHANA ta harareta ta ce" ki mana shiru, ke da baki san darajar soyayya na baki da abin fada a nan, ......sis A'isha fada min, wai dama ke ma kina son sa?"

A'isha ta yi murmushi tana sune kai, kafin ta daga ta dubi FARHANA a tausashe ta ce" a da, da nake masa kallon yayana, ban taba kawo haka a raina ba, sai soyayar yan uwantaka wace a kullum nake fatan Allah ya sa ya rage jin haushin mu ya ja mu a jiki, bale Ni bai taba daga hannunsa a kaina ba Farhana, kin ga mai janyo shi nan kuma mama ta shigar mata su bata masa rai su sa ya bar gidan......., Ama daga bakin lokacin da maganar nan ta fito, sai nake ji a cen karkashin zuciyata Bani da wani da zai iya birge Ni sama da shi a duniya......, ya zamo in dai zan kadaice kaina to tunaninsa zai fi komai yawa a zuciyata "

Nur da karfi ta furta" Astagfrullah, Astagfrullah Astagfrullah Astagfrullah Astagfrullah Astagfrullah!"

FARHANA ta cila mata karamin filon da ta rungume tana harararta,

A'isha kuwa kawai murmushi ta yi dan ba zata iya rikicin nur ba, ta tabbata yanzu da sun yi ido hudu zata ja mata a'uziya, ita kuma iya gaskiyarta ta fada, har tsoron abinda auntynsu tace take yi, da tace su saka mama a addu'a, sannan su yi ta rarashin mama ta nan gidan da yaya wai, dan a saki Mama, ko ba komai mama Maman su ne, tana tsoron mama ta dawo ta hanata auren yaya Sulaimana gaskiya!

Shigowar Anna ya sa suka bi ta da kallo suna yi mata sanu da shigowa

Murmushi yake yi tana bin su da kallo bayan ta zauna a tausashe ta ce" Fira kuke yi?"

FARHANA ta ce" Eh Anna"

Anna ta ce" Masha Allah, a riinga yi ana ƙoƙarin yiwa yata lesson, kafin in samu Aban naku in sanar masa ina so a bani ita na kwana biyu sosai in mata lesson saboda wannan Tantancewa da yayanku zai yi na bani tsoro, domin Fisabililahi shi da larabawa ya saba karatu, da wahala ya kyale min dalibai a cikin nutsuwa

Nur ta rafka tagumi cike da tsoron kar aje ya Koreta

FARHANA ta yi dariya hadi da A'isha

A'isha ta ce" Ai kam Anna, gwara dai ku dage"

Anna ta yi yar dariyar ita ma, a tausashe bayan ta mike ta ce" Ku tashi ku shirya ku je saloon din nan, a yi shigar mutunci idan kun je a wanke kai yau, in yaso in aka kwana biyu sai a koma a yi kitso, ga katina a yi anfani da shi, zan shiga in yi barci sai kun zo"

Godiya suka ringa yi, Anna na fita Nur a hankali ta ce" ku yi maza ku shirya mu je, wallahi yau sai mun samo inda yake mun fada masa sakon Anna, "

Farhana ta zarro ido kasa kasa ta ce" wai da gaske kike? Bakya tsoron asirin mu ya tonu?"

HALLAH ta tabe baki ta ce" Mu je dan Allah, idan Anas na so ya zo ya fadi inda ya kai mu, in ba sai na fasa aurensa ba ubana goma, kuma bayan wannan ai ba yawo zamu je ba, sakon Anna zamu isar tunda mun kasa samunsa a waya"
Chapter 93 · 0% Book details