Sashe 60
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya sake duban auntyn yara ya ce" Sai dai duda haka, ki kara janyo yaran nan a jikin ki, ki kara nuna musu gudun abin hannun wani, sannan ki kara yi musu hannunka mai sanda da shigewa mutumen da bai ja su a jiki ba, ke ko janyo su aka yi a jikin su bi a hankali saboda rayuwa Allah kadai ke iyawa bawa........., su guji kwadayi, su guji munafurci, su guji hada husuma a wajen wanda ya janyo su jikinsa kin ji???"
Auntyn yara ta gyada kai ta ce" In sha Allah, zan kara nusar da su"
Aba yayi murmushi ya sake dubanta ya ce" To madallah"
Auntyn yara ta ɗan Dube shi, bai fi minti goma da shigowa ba, ya kasa ya tsare a kofar dakin ta , mama bata nan, yaran basa nan, kuma sai da ya garkamawa gidan sakata ma, ko me Aban yara ke nema a gida da ranar gari ? Oho
A tausashe ta ce" Ka aminta ta kai sun kenan?"
Aban yara ya Dube ta, da murmushi ya ce" Ko ke kika ga kamalar matar nan da wahala ki iya ce mata a'a kai tsaye, kin ga ba kowani mai hannu da shuni ke mutunta talaka ba, a zamanin nan kuma wanda ya fito maka a bayyane bashi da niyar cutar da kai, sai dai wani nufi na Allah........, Eh na bata dama, idan ta kai su nima zan yi iya yina gaba in baki ki kai su, dama ina cewa ya dace a fasa asusun nan fa a yiwa yaran nan sababin surutu ko kuwa?"
Auntyn yara ta dube shi da mamaki ta ce" Malan asusun da kake tara kudin da idan wata bukata baba ta tashi a yi? Ga ma harkar makarantar nan tasu da alamu suka nuna kudi za'a nema masu daraja????"
Malan ya gyada kai ya ce" To kuma ai ba wanda zai hana wani, jiya da kuka yi wanki sai na ga kayan du sun mutu, kawai dauka za'a yi a yi anfanin da ya dace, idan ya so sai in dora wani..... Allah ya kara mana kasuwa , in sha Allah koda makarantar ta fi karfina sai in sama musu ta dai-dai karfina......, kin ga auntyn yara, ki zo mu dan gaisa mana kafin gidan ya dauki mutane?????????, Ni kam hala ji kuke na buga ne da kuke mantawa da lamarina a gidan nan????"
Auntyn yara ta zaro ido, ta Dube shi da sauri ta bi furfurar dake kansa da kallo kafin ta kalli sararin samaniya...........hasken rana kwal a gari jama'a,
Sai kawai kunya ta kamata, mai girman gaske....., Ama kuma shi rai a bashi dadi kawai, bale yanzu da abin ya zama kusan sai shekara Shekara......?, kai ta boye a mayafi ta yi dakinta cike da jin kunya, Aban yara kuwa yana washe baki ya bi bayanta ya sake zuga sakata a nan........
Wato rabonsa da ya ji irin alamun nan a ransa fa tunda ya baro wajen Malan.....
Gaba daya Malan na son saka shi a kaka naka yin rayuwa da zulumi mai karfin gaske saboda fitina da neman a yi zai ce a cikin ya'yansa ajiya wanda ba nashi ba? Yaya zai daga masa hankali ta wannan sigar ne?, shi dai ya yarda da cewa ya'ya duka nasa ne, kuma in sha Allah hakan zai tabbata idan ya dawo da SULaimana su hadu su masa shegen duka su dawo da shi hayacinsa, karyar shaye shaye ce ke raya masa magana irin wannan!..........
A bangaren yan makaranta a lokacin da suka tashi daga islamiyar Nur ta rigayi A'isha ma daukan hanyar fita, dan ta yi niyar ta je ta yi jiranta a hanya ne
Sai dai a lokacin da ta zo ficewa idannuwanta suka kai kan ANAS dake duke , hannayensa biyu zai karfi wata farar takarda da wani ky daga hannun d'an Anna da ya zo daga saudiyar nan
Haka kawai ta samu kanta da dan tsayawa ta zuba musu ido, a cen cikin zuciyarta cike da tunanin menene ya sa ya duka har haka? Duda ta ga mutumen da dayan hannunsa yana yi masa alamun ya mike sannan ya dora yatsarsa saman lebensa alamun kar yayi masa surutu ne ko meye oho, sai dai cikin ikon Allah sai ta ga yaya Anas na kuka, kuka fa, kukan gaske, hakan ya sa ta zarro ido gaba daya da mugun mamaki tana dubansa kafin ta juya ta fice da dan sauri saboda wani irin takaici da ya rike mata zuciya da jin haushin mutumen!
Gaba daya bata ga dalilin da zai sa ya kore shi a haka a cikin mutane ba, shi kuwa da bashi da zuciya dan ya kore shi ne yake kukan nan? Ita kam ta shiga uku, shin yaya za'a yi ta iya rayuwa da namiji mai saurin kuka? Ita tana so ta samu irin mazan nan da duk rintsi ba zaka ga hawayensu ba!, to wai hawayen su zubo ace na menene? Wani irin mutuwar zuciya ce zata sa ka tsaya kana kuka a gaban mace? Gaba daya haushinsa shi din ma sai ya kama ta, wani takaici ya ishi rayuwarta...., sai ma ta ki tsayawar ta wuce kanta tsaye kawai ta nufi gida, sai da A'isha ta gama nemanta ta gane ta fa yi gida ne ta nufi gidan itama da takaicin ta ki tsaya ta, bata san nata takaicin da ta shako ba ita ma!
Yaya Anas kuwa a lokacin da IMAD ya fito zasu wuce cikin gari da su Aliyu ne ya dakatar da su ya fito da sakon sa ya ja shi gefe sosai nesa da idannuwan kowa ya bashi, sai dai Anas sai ya nemi zubewa kasa dan yin godiya, shi ne fa ya sanar masa idan ya masa wannan abin ransa zai bace, ya mikar da shi yana dubansa da kula ya ce" Anas, abinda ya sa na baka a nan ka san a cen gida ko a ina zan baka gaban mutane ne, kuma an gama saka sunan kowa wanda aka warewa din shi yasa na baka abinka.....ka daina abubuwan nan, ba wani anfani, sai mun hadu a gida"
Daga haka ya karasa ya shige mota suka yi gaba, shi kuwa cikin farin ciki ya kai cikin mota sannan ya sake zuwa ya zauna yana jiran su Anna
Sai da Yama ya dauki su Anna ya kai su gida, ya tabbatar cewa ba zasu fita ba sai kawai ya je inda zai dauki tasa motar ya dauka cike da farin ciki ya nufi gidan su da takardun motar yan hango gidan nasa, domin ya san a jerin gidajen da aka bashi guda, gidaje ne da aka gina masu yawa a wata anguwa guda, kuma du ginin iri daya ne, an saka wasu a kasuwa ne har an kwashe, yan kasuwa da manyan ma'aikata sun siye, ya rage sauran da basu wuce biyar ba, har yana tunanin ta yiwu baki uban gidan nasa zai rinka saukewa a ciki, in ana abinda manyan baki zasu zo ta kowace kasa din nan da ake daukan hayar gidaje na alfarma a saka su din nan....ashe ashe ashe yana da rabon mallakar daya a cikin gidajen nan??????? To shi kam ai IMAD ya gama masa komai , dole zai ci gaba da yin biyayya........
Da wannan farin cikin ya karasa gidan su, ya samu mahaifiyarsa cikin zulumi da tunanin halin da yake ciki domin wuni ta yi tana duban waya da jiran kiransa Ama shiru.
Wannan abin farin cikin ya kawo mata, wanda ya sa ta yi murna ta yi murna sosai ta ringa rangada guda..........
Muryarsa a matukar raunane ya ce" Mama, kin ga ko? A yanzu a duniya abu daya ya rage min, shi ne in mallaki Nur a gidana...., dan Allah Mama ki shirya zan kai ki koda gobe ne ku gaisa da iyayenta a mutunce......., idan ya so sai ki sako maganar kina so a zo tambaya, wato mama idan da hali kawai su bani dama in kai sadakina su bani ita, Mama Nur ita ce cikar burina, ita nake so, ita zuciyata ke so"
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, du irin murnar da maman du Fa'iza ke ciki sai da ta yi wani irin lakwas tana kallon ANAS
Har ga Allah tsoro da firgici suka kama zuciyarta Bama da ta tuna abinda ta je ta aikata a gidan su NUR din nan, sai ta gama tunanin ta ina zata shiga gidan su ta ce me ta zo yi?
Innalilahi wai me yake damun yaronta a kan wannan yarinyar ne?
To a yanzu ai a matakin da ya taka ita ta tabbata ko Na'ima sai ta jira bale wata NUR
A tausashe tana dubansa, bayan ya ba su Fa'iza ky din motar dan su fita su gani suna ta ihun murna ta ce" Haba Anas, haba Anas, wai NUR din me dan Allah?, yarinyar da tun kafin ta shigo gidan ka ta raina ka? Bata sonka fa kai ma ka sani, yarinyar da bata samu tarbiyyar kirki bane kake son aura? Ka duba ka ga tun kafin ka aureta mahaifiyarta ke mana sintiri da wulakanci kala kala a gidan nan, yanzu idan ka auri yarinyar nan ka ce ka auri wa,? Ni na tabbata ko Gara iyayenta ba zasu iya yi muku ba bale a kai ga kayan daki.......irin yarinyar nan fa idan ka aure ta har iyayenta ka aura saboda duk wata diyar iyayenta zata dawo kanka ne......, bayan wannan ka duba ka ga yadda yan mata ke jira ka nuna sha'awar aurensu, da ka auri yarinyar nan ba gwara ace yar gidan kawata ka aura ba? Haba ANAS, kai Ni yadda yarinyar nan ta nuna tana iya bige ni na tabbata kana aurenta zata raba Ni da kai, kawai ka hakura da ita ka nemi auren Na'ima, yarinya yar gidan mutunci da iyayenta suke iya darajaka su baka da dimbin abin alkairi? Haba mana Anas "