← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 141

Sashe 43

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kawai ta shiga fyace majina tana mika masa hannu abin kuka

Mama ta saka dariya tana duban Anna ta ce" Ta aljanna, wannan uwar taki bata tsoron Allah, ji baki ba haƙora zata mana munafu.........."

"Lah mama, mu je ciki ki tayani dauko kayan abinci". Anna ta fada da sauri tana riko hannun mama ta yi kicin da ita

Farhana ta yi murmushi a ranta tana ayyana 'INDAI KUNSAN KUDIN KUKESON SAMU A ONLINE BUSINESS TO KAWAI KUYI JOINING GROUP DIN NAN 👌🏻😅KUNSAN bani kawo abun banza
💃🏻https://chat.whatsapp.com/L64v3OVQ52pJqtMT51yL2x

25

Farhana ta yi murmushi a ranta tana ayyana ' Dadin abin kema da mai tona maki asiri, kuma bata da hankali bale ace ta maki rashin kunya....ku ga mata sai yamutsa take yi kukan ya ki zuwa, Allah dai ya kar da Giwa ko na walala....."

Zaunar da ita ya yi da kyau saman abin zamanta mai laushi sannan ya rike hannayen ta yana dubanta a tausashe ya ce" Yi hakuri da kukan haka mana, kar ki hadasawa kanki ciwon kai Inna"

Inna ta ɗan janye rufar da ta rufe gaban idannuwanta tana dubansa ta ce" yaya ba zan yi kuka ba, na zata sai na mutu ka zo ka birne Ni, tun ina tunanin na ganka har na dauke tsamani na zubawa sarautar Allah ido ......., yanzu fa a kadan ka kai wata tara baka zo kasar nan ba......, idan ka tashi tafiya da Ni zaka je dan wallahi idan ka barni a nan kashe Ni zasu yi, ka ga babu mai tausaya min, babu mai jin kan tsufana, a gidan nan kadan suke jira in yi magana a ƙaryatani , Bama kamar wancen matar Malan din, da hankalinta ras kawai Ni ce ta tsana, ba mai zuwa inda nake , du sun tsane ni, mahaifiyarka a gabana ta zabi wannan kanwar taka, saboda Ni na fada mata kar ta shiga harkar ta tunda bata jin magana, Ama mahaifiyarka ke tafiya da ita makaranta salon ta zubar mana da mutuncin ahali........kai ba dan tawakali da hakurina ba ai da sai dai ka tardo gawata...., yanzu ina matarka take????"

Farhana ta sauke ajiyar zuciya a ranta ta ayyana ' Yau Ni na ga jaraba, matar nan da ba Anna ta haifi wannan bawan Allahn ba da ta da ya kore mu, ji yadda take hada d'a da uwarsa, dadin abin dan halal ne akoy biyayya ba zai taba yarda da maganar gigitaciyar tsohuwa ba, Allah ya Allah ka shafe tunanin sunana a bakin matar nan kar ta ja min balaki!'

Murmushi yayi yana dubanta, a ransa yana Ayyana irin shekarunta a yanzu.....duda rigimar ba karamin yawa ta yi ba, Ama yakan hade hakan harda shekarun da suka kai yanzu a tare da ita, inda Allah ya taimake shi bata yada carbi ba, bata bar sallah ba bata bar addini ba, babu abinda ta manta, tana sane da komai haka kuma har yanzu da kanta take tafiya sai sandar da take tokarawa wani lokacin, itama ba wai kullum ba

A tausashe ya ce" Tana lafiya, yaya sauƙin jikin ki ne???"

Ta karkata kai tana buɗe bakinta ta nuna masa cen cikin bakin ta ce" Ina, ba sauki, duba ka ga bakin nan nawa bai zama Cancer ba kuwa????"

Farhana ta gyada kai tana juyar da kai a ranta ta ayyana ' Ciwon Arne kenan, matar nan ko dai ta yada shahada ne? Ke kullum jikinki ba sauki? Ba sauƙin ne baki mutu ba kike nan kina gana min azaba????'

IMAD kuwa ya dan zaro ido yana dubanta ya ce" dukan tsanani yana tare da sauki ina, ki ce da sauki kin ji???"

Inna ta fashe da kuka tana murzar ido ta ce" Ni ai karya ce bana son yi, Ni kadai na san markadeb da ake min a jikin nan nawa, yadda ka san na je yaki kulun idan na kwonta da kyar nake iya tashi, bakin nan nawa kuwa ban isa in sha sanyi ba , yanzu zai dau ciwo kamar in mutu"

IMAD ya ce" Asha, asha, ki yi hakuri kin ji? In sha Allah zan kai ki asibitin a sake duba ki....."

Sai kuma ya kalli Farhana inda ta tsuguna ya ce" Auta tashi mana ki zauna da kyau, wai ina su JAUHARA ne? Ban gansu ba"

Inna ta dubi Farhana da ta mike kai a kasa ta ce" bari in leko su yaya"

Sumui sumui ta nufi elevator

Inna ta gyada kai tana dan riko hannunsa ta ce" Dan rike min hannu, tabbas ana daf da hada baki da yan kidmashin su sace maka Ni, ji wata jaraba yarinyar nan fa nan take min yawo da karamin wando yadda ka san ta cire ta yar ......, Ama yanzu da yake munafuka ce tunda ka zo take yawo da hijab, dan Allah ka aurar da ita ko na huta a gidan nan ka ji????"

Anna ce ta dawo dauke da plate shake da fruitssss, sai da ta zubawa mama sosai da dabara ta bude mata kofar kicin ta baya ta ce ta je ta kaiwa Malan nasa, ta tafi sannan ta gyara nasu ta fito da shi , ba dan komai ba sai dan ta san mama da ina basa taba zama a waje daya ko na minti biyu ne, dan kuwa ina na fara zage zagenta irin idan tace an bata mata ran nan mama ke neman bigeta, dan har ce mata take yi mana shiru yi mana shiru a nan , ko kai tsaye tace da Inna karyar banza, hakan ya sa Inna ta tsaneta sosai, itama kuma da ta ga Inna a waje sai du ta shirya ko ta kwanan nan, shi yasa idan yana nan take kwatanta masa ya kiyaye du zaman da za'a yi da Inna yace Mama ta zo, dan lamarin mama ya riga ya zama sai da hakuri sosai, kwarai tana iya yin doguwar fira irin ta hankali, Ama kadan maganar yaya ta shigo zata birkice, kadan ta samu kanta a mugun farin ciki zata birkice, yanzu haka ta tabbata ganinsa ya da ta rikice din nan, da ya kwana biyu a garin ya zamo zuciyarta ta yarda yana nan abin zai yi sauki sosai, hakama Malan ta tabbata yanzu zai karra dagewa da rubutu, kuma sosai ake ganin kyan abin......., rabonta ma da irin haka tunda Farhana ta sanar mata a almajiran Malan akoy masu tsokanar Mama, ita fa kanta ta samu Malan da batun, gana daya ma dai ya soke shigowar almajiran nasa bayan ya musu fada sosai da alkawarin ganin bacin ransa ga duk wanda ya ci gaba da dauko mata maganar da aka san tana fitar da ita a hayacinta, dan ko jiya rass suka rabu da ta kawo mata tuwon da ta tuka na dare, domin idan ta yi girkin tuwon laushi takan zubowa annan ta kawo mata, domin Anna nada son tuwo irin na gargajiya sosai.

Farhana bata jima sosai ba ta dawo dan ta sanar masa Jauhara bata nan sai iman gatanan saukowa, dama a kaf kannan MAZNA da Imam kadai suke shiri, dan yarinyar bata da wata damuwa, idan tana nan takan shiga cikin su sosai, danma yayarta ce bata cika son barinta a wajen su ba.

Tana karasawa ta zauna kasa daf da kafar Anna, a irin lokacin ne kuma Jauhara ta bude kofar ta taya auntynta kinkimar abinda suka jero basket din dake dauke da kayan abincin har zuwa kan shayinsa sannan ta ci gaba da turowa da Salama a bakinta hadi da sakin fuskarta sosai ta iso da abin tana duban Jauhara ta ce" Je kicin ki ga idan akoy leda ki dauko mu shinfida"

Sannan ta dubi su Anna da girmamawa ta duka tana fadin " Barka da safiya Anna"

.sai kuma ta kai dubanta kan Inna da dari dari ta ce " Barka da safiya Inna "

Inna ta zarro ido tana dubanta kafin ta juya ta kalli IMAD,

kasa kasa sosai ta ce" Kai wai hala MAZNA ce?"

IMAD ya dubi Inna kafin ya gyada kai

Inna ta sake shafa gilass dinta tana bin MAZNA da kallo, wace ta waye kamar wace ta saba shiga cikin su, ta yi watsi da irin kallon mamakin da Farhana ke yi mata, saboda tsakani da Allah a jiya bata ga komai a tare da ita ba irin na yau, Anna kuwa dama babu wani abin da ta gani, bata ma kure mata waje da kallo ba bale har ta ga wani abin.....kai gaba daya ita kallo daya ta mata ta kawar da dubanta.

Farhana ta gyada kai a ranta ta ayyana ' Kan uba, matar nan kuwa yaya aka yi ta yi duwawu haka? Ina ruguza ruguzan nonuwan da kumatun????'

Inna ta rage murya sosai ta ce" To wai Ni kamar ba haka na santa ba, ina dima diman nonuwan nata da su kake fara gani da ka ganta????"

IMAD ya dubi Inna, kasa kasa take maganar sosai, ya dan dubi MAZNA, sai yayi kamar bai ji me Inna tace ba, dan ai a ganinsa wannan din ba firar da ya dace ace sun yi shi da Inna bane ko????

Inna ta Dube shi da mamaki kafin ta dubi Anna ta ce" Anna Ni shekaruna nawa yanzu???"

Anna ta dubi Inna kafin ta yi murmushi ta ce" tamanin ba daya Inna"

Inna ta gyada kai ta ce" Nima haka nace a raina, hakan na nufin ban shirufce ba, ban kuma manta komai ba, Ama ke dubi yarinyar nan tsakanin ki da wanda ya halicce ki haka nonuwanta suke a da ma???"

Farhana ta zaro ido da karfi ta furta" Innalilahi "

MAZNA ta dago da sauri gabanta na faduwa........., Anna kuwa bata ce komai ba, hasalima bata kalli maznar ba dan ai wannan kamar zata shiga wani abin da bai dace bane a ganinta........

A nutse ya dubi FARHANA, lokaci daya ta koma ta zauna tana sakin hannayen da ta daga sama, dan wallahi ita bata idasa yarda da abinda zuciyarta ke hasaso mata ba dai da Inna ta fadi abinda yake ranta, wato ina dukiyar Fulanin matar ƴaƴanta suka je, to dai a karshe dai zata iya cewa Inna bata wani haukace ba, kwarai idannuwanta na fada mata gaskiya sai dai mugun hali!
Chapter 43 · 0% Book details