← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 141

Sashe 30

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Tallah tallah tallah

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data
*17*

A hankali IMTEE ta rike itama tana dubanta ta ce" ki sakar min wuya , kin san dokar makarantar nan, ki sakar min wuya!"

Na'ima ta sake shake mata wuya ta ce" Idan na ki sakar makin fa? Munafuka algunguma kin san baki da wata power kike son shiga filin dagar manya?, sai me? Doka ai taku ce ya'yan talakawa ba mu ba, ki fada da bakinki cewar kin bar min mijina har gaban abada idan ba haka ba Walahi sai na sumar da ke a nan kuma in adabi rayuwar ki kin ji na fada maki!"

A'isha da sauri ta mikawa Fa'iza litafinta ta kwashe hijabinta zata fada fadan IMTEE ta daga murya ta ce" Kar ki saki ki shiga, ba na hana ki shigar min fada ba????????"

Ta saka hannayanta ita din ma da karfin ta kwace wuyanta kafin ta maye nata hannayen a wuyan Na'ima

Matse mata wuya ta yi tana ruko mata idanu ta ce" Shi din banza na bi shi? Ya isa ma na bi shi? Ki je ki ce masa kar ya kuma bi na ki ga idan zai isheni kallo, karya namiji yake in bi shi ɗan ubans......................"

Hango Malan jaharu tafe da sauri da bulala tare da wasu tare da shi ya sa IMTEE sakin wuyan Na'ima, wace ta shige jikin Imtee tana ihun sai ta kashe IMTEE, ita kuwa ta bata damar kai mata dukan da ya sa ta duka tana rike kirjinta dan kuwa kulli ta sakar mata a kirji mai zafin gaske.......

Karasowar malamai ya da Na'ima ja tana huci tana murza hannayanta, dan irin zafin da suke mata ita kadai ta sani

Malama Rukaya ce ta furta" Ikon Allah, da girmanku kuke mana dambe a filin makaranta?, ku wuce mu je office , oya ku wuce"

A'isha ta kama IMTEE ta mikar da ita a hankali, sai dai IMTEE ta cure waje guda kirjinta na yi mata zafi sosai, dan ita fa kanta bata san dukan zai yi zafi har haka ba

Ganin haka ya sa Malama ta kama mata ita suka nufi office din Hajiya , sai Malan baki mai horo da ya mara musu baya fuskarsa a tanke sosai

Sun samu Anna na ziga shayinta tana video call da yaronta suna zantawa, gefe kuwa Farhana ce ke zaune kanta kasa ta mugun nutsu kamar ba ita ba.

Bayan an basu damar shigowa ne Anna ta mike tana furta" Subahanalah, lafiya? Me ya sameta?"

Sam ta manta bata kashe computer ba, shima kuma bai kashe din ba , sai ma yayi connctn din call din da camarar office din, saboda duk wata camara na anfani da wayarsa a duk inda ya so hakan ya sa ya dan zuba ido dan ganin abinda ya sa Anna ta mike haka.

Kwontar da ita suka yi saman doguwar kujerar dake office din, Anna na dubansu ta ce" Farhana, yi maza ki kira mana likita, idan ba zata iya zuwa da gaggawa ba a mikata asibiti...., Hallah menene?"

HALLAH ta ɗora hannun Anna a kirjinta tana fitar da nishi dan har ga Allah ta ji dukan, Ama zuwa yanzu ya fara sakinta fa, kawai dai tana ta tunani ne, shin yarda zata yi a gane ya sake ta gaba daya ta yaɗa ta tabbata ana iya korar ta a makarantar nan dan sun taka doka mai mahimmancin gaske ko kuwa a haka zata zauna su dauki punichment din da ya dace da su, idan ya so a waje zata rama abinda aka yi mata? Dan kuwa Walahi bata tunanin in har zata iya yafewa wannan yarinya dukan da ta mata a kirji dan ta ga ta sake ta, ta zata tsoronta take ji ko???????

"Wai ba zaki yi bayanin abinda ya haɗa ku fada ba? Ana tambayarki?" Malama Rukaya ta fada da tsawa tana duban Na'ima

Na'ima ta fashe da kuka tana murzar hannayanta ta ce" Malama, su ne suka tare Ni suke zagina!"

Fa'iza ta yi gaggawar fadin" Astagfrullah, ki ji tsoron Allah Na'ima ki fadi gaskiya"

Anna ta zuba musu ido tana kallo bayan ta ɗorawa Hallah ruwa mai sanyi a kirjinta haka kuma tana shafa kanta bayan ta ja hijabinta baya kadan

Malama Rukaya ta juya wajen Malam baki ta ce" Malan Bismillah, bani dorinar nan!"

Dana Malama akoy saurin hannu, haka kuma bata daukan raini ko kadan, a makarantar tana cikin malaman da idan zasu koyar ake taka tsantsan ake kiyaye duk wani abin da zai sa ranta ya bace......

Bata tsaya wata wata ba tana wartar bulalar ta zubawa Na'ima, sannan ta sauketa kan A'isha dake tsaye tana cicira ido

Ihun da A'isha ta yi ta shiga burgima ya da HALLAH dane kanta da karfi dariya na kubce mata

Ido FARHANA ta zarro, lokaci daya tana nuno Hallah ta ce" Innalilahi, Anna dariya take yi , Walahi dariya take yi algunguma ba wani ciwo da take ji!"

HALLAH sai kawai ta karashe dariyar da kuka , wanda nan da nan ta riko hannun Anna ta ɗora fuskarta tana kukan bilhaki

Ido IMAD ya dan fitar, a hankali ya janyo hoton da kyau yana kallo

Anna ta harari Farhana ta ce" Ke ba na hana ki nemanta da fada bane?"

Sai kuma ta kalli Malama Rukaya ta ce" A yi hakuri Malama, bari su min bayani"

Ta sake duban su a tausashe ta ce" Wa zai fada min gaskiyar abinda ya faru? Ama gaskiya nake so kun ji???"

A'isha na gyada kai ta ce" Hajiya, kin san abinda ya faru? Muna tafiyarmu zamu je gida ne ta tare mu, ta shiga zage zage a kan saurayinta, shine fa har ta shaki Hallah karshe ta dake ta a kirji"

Anna ta Dube su da mamaki, da kuma yanayin damuwa ta ce" Saurayi? , a kan saurayi ne har kuke dukan juna? Wani irin saurayi? Ku yanzu har samari ne da ku dama????, ke tashi daga min kafa a kan saurayi ne kike fada dama....?"

HALLAH ta dago tana zarro ido, kafin ta ja hijabinta har kusan goshinta ta ce" Anna, Ni fa ba laifina bane, cewa ta yi wai sai na fada mata na kuma rantse mata ba zan kuma bin saurayinta ba, Ni kuma nace mata shi din banza zan bi shi???, shiKenan ta shake ni, ni Bama saurayina bane ba abinda ya haɗa ni da shi!"

Anna ta Dube ta, ta sake duban Na'ima, sannan ta dubi Malama da mamaki ta ce" Ikon Allah, yaya za'a yi ace yan mata na fada har da dukan juna a kan saurayi? Kuma a cikin makaranta?????"

Malama ta ce" ai Hajiya kawai bamu su mu je, zamu nemi iyayensu sannan mu dakatar da su, cen su musu aure tunda shi suka zaba musu ba ilimin ba, aikin banza mu zaku mayar shashashu?, ba wace zamu ba dama ta kuna mata wuta a makaranta, ko wacece zamu iya salamarta!"

Imtee ta sada kai tana murza yan yatsunta tsoro fal ranta, dan abinda zai sa mahaifinta yayi fushi ne bata so ko kadan

Anna ta dubi Na'ima ta ce" ki min bayanin abinda yake faruwa!"

Na'ima ta ce" Hajiya, jiya mamanta ta same mu a gidan su shi saurayin nawa da maganar ta, bayan Ni har gidan mu an san da zancen shi, shi din da kansa ne yace in fada mata ba shi ba ita, shine ɗan na fada mata ta zage Ni ta haɗa da shi ta zaga, shine raina ya bace!"

IMTEE ta zarro ido tana kallonta, wannan ai karya ce, kwarai wannan karya ce ta shirga marar mutuncin banza marar mutuncin wofi! Abinda take ta ayanawa a ranta kenan

Anna kuwa lamarin ya bata mamaki ainun, ta dubi wannan, ta dubi wancen, da kyar ta sauke dubanta a kan Malama a tausashe ta ce" Malama, ki yi hakuri ku je, kwarai zan yi maganin abin"

Malama ta yi godiya suka juya, ba haka ta so ba, ta so a bar mata su ta saka su a hankalinsu dan ba zasu bari wani tsagera ya kawo musu raini ba, Anna kuwa haka kawai take ji a zuciyarta tausayin mahaifin n yaran nan, ya zo Dazu, yannayinsa ya nuna burinsa su yi karatu, kokarinsa da nunawa da yayi ko nawa ne zai nema ya tara ya biya dan su samu ilimi ya matukar birgeta, sai ta ji a ranta yanzu idan dan rashin ji na yarsa ya sa an Koreta an yi kiransa saboda wannan dan abin ai ba'a kyauta masa ba, kai gwara ta yi maganin abin a nan

Hade fuska ta yi sosai ta ce" Abinda kuka yi ya maku? Nace ku da kanku ya birge ku? Darajar ku kenan fada a kan saurayi???"

HALLAH ta sake sada kai kunya na kamata, sai take ganin ai abin kunya ne a ji tana da saurayi ma bale har a kai ga a ji ta yi fada saboda shi

Anna ta ringa musu fada ba ji ba gani kafin ta ce" Idan na kuma ji, sai na sasaba muku, du wace ta yarda ta kuma mana fada a cikin makaranta sai ta dauki hukunci mai tsaurin da zai gigitata kun ji da kyau?????"
Chapter 30 · 0% Book details