← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 141

Sashe 108

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutalab da ya ganshi kwonce yayi ruf da ciki a saman tiles gaba dayansa ya sauka daga saman dardumar ma dan azabar da yake sha ne ya nufe shi a sukwane yana duban Aliyu dake bakin kofar kansa a kasa ya ce"

Page 65_66

Morning allllPage 67 and 68

Da dan karfi ya ce" ALIYU ka shigo mana"

A hankali ya bude idannuwansa, lokaci daya kuma yana janyo hannunsa daga wajen mararsa hadi da sake dane jikinsa ta yadda ba zai basu damar ganin yannayinsa ba, cen kasa ya furta " No, kar ya shigo......"

Abdul Bassit ne da ya fahimci halin da yake ciki, domin ko a cen ya taba samun kansa cikin wannan halin har sau biyu ya dubi Abdul Fatah ya kwatanta masa cikin kokarin Boye sirin

Abdul Fatah ya Dube shi da mamaki, sannan ya dubi hanyar da MAZNA ke tsaye ya sake dubansa da wani mamakin kafin ya sauke ajiyar zuciya yana duban Aliyu ya ce" Aliyu ka je kawai"

Juyawa Aliyu ya yi ya fita hankalinsa du a tashe, ya rage su hudu kadai sai MAZNA dake nesa da su kadan

Ajiyar zuciya Abdul Fatah ya sauke kafin ya juya da sauri ya fita ya nufi masaukinsa, domin in dai ba ya manta ba a jakar nan da aka shirya masa kayansa a cikinta AKOY maganin da ya taba sakawa saboda wata tafiya da suka taba yi suka dauki lokaci, domin shi ma mutun ne mai makamanciyar fitina irin ta IMAD, kuma shi matarsa in dai zai matsa nan da nan to fa sai ta ringa daga masa hankali ta waya ba dare ba rana, sai dai idan basu yi vidio call ba, wani lokacin sai ya ji kamar zai yi hauka, shi yasa in dai zai jima yakan jefa maganin nan a cikin akwatin da za'a shirya masa

Abdul bassit kansa ya gama daurewa, kuma sun yi sun yi dan su kama shi su mayar da shi saman bed Ama ya kiya, karshe ma sai ya hana kowa taba shi saboda yana matukar jin nauyin su ganshi a yadda yake a haka.

Abdul bassit ne ya yiwa Mutalab alamun ya mike ya fita

Da farko da mamaki yake kallonsa ya ce" In fita fa kake nufi?"

Abdul bassit ya tsare shi da duban da a dole ya tashi ya fita ya je ya zauna a falon yanayinsa du a takure saboda hankalinsa ba a kwonce ba

Dawowar Abdul Fatah ya shigo da Salama ya karasa yana bude karamin goron ruwan da ya riko ya lalubi hannun IMAD ya saka masa maganin kasa kasa ya furta" Ka sha, wanda na taba baka ne"

Hakan ya sa IMAD jimke maganin yana jin zuciyarsa na karbar abin, a hankali ya dago kansa ya sha maganin sannan ya dan dafe goshinsa yana murzawa a hankali a hankali yana ta addu'ar da yake ta yi tun jiya har zuwa yanzu ta samun sauki , a hankali a hankali har ya ringa jin nutsuwa na sandarsa, a hankali abinda yake jin ya masa jikaka a jini ya dan CENZA

Cikin dabara Abdul Fatah ya nufi wajen kofar nan ya yiwa MAZNA dan murmushi hadi da yi mata nunin zai rufe kofar, cikin nutsuwa ya kama kofar dakin nasa ya rufe harda murza ky

Abdul bassit ya Dube shi da mamaki ya ce" Ya zaka rufe matarsa na tsaye bayan ka san itace maganin damuwarsa? Ko Ba abinda nake tunani yake damunsa ba?"

Abdul Fatah ya sauke ajiyar zuciya ya karasa inda yake kwoncen yana duba time domin maganin yana da saurin kama mutun, in ya jima minti goma, idan ya auna lokacin da ya bashi ya hadiye zuwa yanzu kuwa ya kai minti goma da wani abin, hakan ya sa a tausashe ya ce" Ko mu je asibiti ne?"

IMAD ya rintse ido saboda abinda yake ji mai tsananin girma na rufe masa idannuwansa, wato matsananciyar kunya da nauyin aminansa, Duda ya hadu da mamakin ganinsu a irin wannan lokacin, dan bai san da zuwansu ba, sai ya kasa mikewa ya nuna hakan dan tarin kunya

Murmushi Abdul Fatah yayi, ya mike ya je inda Abdul bassit yake ya kama shi ya juyar da shi ya ce" Mun juya ka tashi"

Sai a yanzu ya dafa ya mike a hankali ya wuce bayi, hakan ya sa shi Abdul bassit zuwa wajen suturunsa ya bude ya ciro masa jalabiya da gajeran wando sannan ya saka musu turaren ruwa mai kauri sama sama ya je ya tsaya bakin bayin yana kallon Abdul Fatah da ya zauna saman kujera cike da mamakin lamarin nan

Ya jima a ciki, sai da yayi wanka da ruwa mai dumi sosai har ya busar da gashinsa Sannan ya dauro tawul ya bude kofar bayin

Amsar kayan yayi ya mayar da kofar ya rufe ya saka tufafin sannan ya bude ya fito daga dakin yana daure fuska ya je ya wajen karamin frij din dake jone ya bude ya cire madarar holandia ya dawo ya zauna ya bude a nutse yayi Bismillah ya kafa kai ya sha sannan ya ajiye yana lumshe idannuwansa hadi da shafa wajen mararsa........

Ba wai sakuwa ta yi
Gaba daya ba, ta dai sassauta masa radadin da yake ji mai zafin gaske............, ama a kule take tamau .

A nutse ya sake dubansu yana sake daure fuska ya ce" Menene wai"

Abdul bassit ya girgiza kai yana sake hade girarakinsa ya ce" Me hakan yake nufi? Me ya haɗa ka da ciwon nan kai magidanci?, hala fada kuka yi ka kasa amsar abinda ka san ita kadai ke rike da shi ɗan samun nutsuwar ka?"

Ya girgiza kai ya dora da fadin" Shi yasa Ni bana fushi idan dare yayi, du fadan da muka yi dare na yi nake turewa in dauki halaya irin na Musulunci da yayi hani da gaba in fara yi mata magana mu shirya, kun ga na samu ladan fara neman sulhu, kuma na samu romon dake tafe da sulhu......, ana fada da mace sosai da sosai, Ama irin fadanka da mace gaskiya na rashin sanin ciwon kai ne, yaya ma za'a yi in yi duhun kai har haka? Ai duk rintsi za'a shirya ta yadda zan samu abinda yake nawa!"

Shirun da ya musu ya sa Abdul Fatah karasawa kusa da shi ya zauna, a nutse yana fuskantarsa ya ce" Ya dace ka fada mana damuwarka "

IMAD ya sake yi musu shiru

Abdul Fatah ya ce" Sirin da bai dace mu ji bane? Ina nufin sirin da iya kai da ita ya shafa? Na fanin fayyace mana zaman aurenku?, wato lamarin.....lamarin.........."

Abdul bassit ya ce" Lamarin da ya shafi sex din ku?, bata iyawa da kai ne? Ko ka daina jin sha'warta?, bata gamsar da kai ne? Ko hana maka take yi?"

Abdul Fatah sai kawai ya bi Abdul bassit da kallo.....domin shi nauyi kalaman suka yi masa, Ama da yake a cikinsu dama Abdul bassit du ya fi su iya shege ya karasa maganganun

Ajiyar zuciya Imad ya sauke yana gyara zamansa ya dauko karamar wayarsa dake ajiye ya dana wasu numbobi ha kara a kunnensa

Ringin din farko aka daga kiran, da girmamawa Aliyu ya furta" SIR Barka da warhaka"

A tausashe Imad ya ce" Barka, ka je aéroport da passeport din Madame......, a duba min tafiye tafiyenta na shekarar nan .........and......"

Ya dan dakata ya ce" And ka sa a duba min call din ta....., ka je zan tura maka hoton passeport din ta WHATSUP "

Daga haka ya ajiye wayar yana dafe gaban goshinsa cike da jin wani irin tukuki a cikin zuciyar tasa

Abdul Fatah dake dubansa da kula yace" Bincike zaka sa a yi mata bayan ka san ba kyau?"

Abdul bassit ya ce" Me yake faruwa! Ba zaka bude bakinka ka fada mana abinda yake faruwa bane wai? Ko dai kana cikin mazan nan da idan suka hada waje da matansu basa yi musu da dadi wajen zamantakewar yau da gobe?"

IMAD ya Dube su, da idannuwansa da du suka CENZA yannayi ya ce" Me kuke son ji? Wanda Ni ma ban sanshi ba!..........., abinda na sani shi ne abinda nake ta gudun zurfafawa a binciken abinda yake faruwa da matata sai na zurfafa saboda na kai wajen da na fara tunani sosai da sosai a kan lafiyarta............"

Ya yi shiru yana sake sauke ajiyar zuciya cike da takaicin gardama irin na MAZNA da irin yadda take so lalle lalle sai ya kureta

Abdul Fatah ya furta" Subahanalah, me yake faruwa ne?"

IMAD ya Dube shi....., a dole ya ce" Rabona da MAZNA Tun watan jully da ya wuce......"

Ido Abdul bassit ya fitar ya ce" What? Ban gane ba, wani irin tun jully da ya wuce kusan shekara guda?"

IMAD ya dan dage kafadu ya Dube shi, a tausashe ya ce" ba zan kara maka wani magana a kan wannan ba"

Abdul Fatah ya mike yana kai kawo, ya dake duban IMAD a tausashe ya ce" AKOY damuwa, kuma gaskiya dole a samu mafita, ......., ba zan takuraka sai ka fadi sirinka ba, ama ba zan taba yarda lafiyarka ta cutu ba..........."

IMAD ya sake sauke ajiyar zuciya ya mike ya je wajen wardrob dinsa ya bude bangaren takardunsu ya ciro nata ya dauki hoto ya turawa ALIYU, ya san zai samo masa information din da yake so saboda zai bi ta sama ne, wato zai yi anfani da kakin dake jikinsa ya samo informations din da suke so cikin sauki,

Tura masa yayi hoton ya mayar yana dafe gaban goshinsa ya ce" gaba daya ba matar da na aura bace....., komai nata an cenza mata....., ta ce gyara ta yi ta hade da sport....du yadda nake son yarda ta karfi zuwa yanzu na kasa......"

Abdul Fatah da gabansa ke faduwa da daurewar kai a kan lamarin ya ce" Kar dai shigury ta yi?"
Chapter 108 · 0% Book details