Sashe 51
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari su IMTEE sun sake zuwa makaranta, haka aka tashi suka dawo gida yau ma ba tare da Imtee ta ga Anna ba
A yanzu kam ta gama yanke hukuncin zata sanarwa babansu yau idan ya zo dan Allah ya taimaka A'isha ta rakata gidan cen na baya ta dubo Anna, kai Walahi ita ko me zai same ta zata je ta ga Anna, gaba daya hankalinta ya kasa tsayawa waje daya da tunanin shin Anna lafiya take kuwa? Ta gaza yarda cewar ma wai dan wani d'anta ya zo ne ta dauki kwanakin nan bata zo makaranta ba, haba a irin yadda aikin ginin nan ya zo karshe ace lafiya kalau Anna bata nan? Aiki ya kai wajen da zuwa yanzu kawai abinda ya rage kadan ne, dan kuwa penti ne kawai shima yau an fara shafawa gaba daya makarantar tamkar ba ita ba, domin a yau ma fasalin da aka saka suka yi karatu acn sa biyu, to wai yaya za'a ce Anna tana gari kuma tana kalau zuwa ne kawai bata yi ba??, zata je ita ta ganta, harma ta tambayeta to wai wa ta barawa ita bayan ita ta yi alkawarin tsaya mata har sai ta kai matakin da idan an tashi Tantancewa za'a zabe ta kai tsaye? Yaya take so ta yi da rayuwarta ne wai???????????
Sunna shiga gida suka tarar da wani tashin hankali
Tashin hankali mana, mahaifiyar su Fa'iza ce da wata kawarta a cikin gidan nasu suna dauki ba dadi da mamansu da kuma kawar maman nasu wace ita ma bata jima da zuwa ba......., INNALILAHI Maman yara tamkar zata yada zani sai zage zage suke ita da matar nan da cin alwashi kala kala, auntyn yara na tsaye a kofar dakin ta ta zuba musu ido zuciyarta ta mata nauyi
Shigowar su ya sa maman su Fa'iza nuno Nur ta ce" Ai kin ga yarinyar fa, a kan wannan abar ce Anas ke neman kashe kansa da tashin hankali, to ko me ya gani? Aikin banza macen da tun kafin ka aureta take hada maka fitina a waje idan ta shigo gidan ka ai sai ta nemi ran ka, ke irinsu ne ke kashe maza na rantse maki!"
Kawar maman su Fa'iza kuwa harda zagaye NUR
Aunty na ganin haka ta dago ta karaso ta kama hannun Nur dake tsaye jikinta na son daukan rawa na bacin rai
Hanya ta nuna mata ita da A'isha ta ce" Ku wuce ciki!"
Sumui sumui suka dauki hanyar dakin na aunty, sai kin Muryar kawar mamansu tana fadin" Ke A'isha, wuce dakin mahaifiyarki, nan din da zaki je ai ba dakin mamanki bane ko????"
Maman yara da sauri ta ce" Wai wace, wancen? Karma ta zo min dakina, in fada maki ai da wancen sai a hadu a kashe Ni, wuce ku je, karma in ga kafarki a dakina!"
Jiki ba karfi A'isha ta juya ta yi ciki, Nur kuwa ta shiga kwabewa dan bilahilazi sai dai a kwashi yan kallo, in ta yarda an zagar mata iyaye su ce da ita shegiya marar uba, babu mai basu zane ba wanda ya isa ya karkada musu datin dan kwali!
Kawar maman su Fa'iza ta dubi maman su Fa'iza ta ce" Ke kuwa huwaila ya kike neman abinda ya gani bayan ga duwawu dima dima kamar na wace ta haifi ya'ya goma duwawu suka bude? Kin fa san mazan nan in dai wajen nan zai zo musu yadda suke so ya ishe su rayuwar duniya, tarbiyyar ma da usuli ba damun su zai yi ba, to usulin me ga uban usuli a ajiye a gadon su????"
Turus NUR ta yi, cike da matsananciyar kunya ta yi baya ta koma ciki ta karasa inda A'isha take tsaye tana hanata fita ta tsaya hadi ta fadi kasa kasa cewa" A'isha, gwara kar Na fitan, mutanen nan ashe ƙaruwar harshe ne da su???"
A'isha ta zaro ido zata bata amsa suka jiyo Muryar aunty , yanzu kam muryarta a dake, haka kuma sama ta yadda dole zasu saurareta ta ce" Ai ba NUR ko uwar Nur zaku yiwa kashedin rabuwa da shi ba, shine namiji shi zaki yankawa iyaka da NUR, idan har ya dauke kafa in kin sake ganin Nur ko a hanyar da zata kai gidanku ne ki ce ba Ni RAHAMA na haifeta da cikina ba!, kina ji ki ja kawar ki ku wuce daga gidan nan, Ni ai na zata yaro dan gidan manya ne, ashe ba haka ba?, ki je kawai ki yi kokarin hana yaronki zuwa neman iri, Ni kuwa na maki alkawarin yayi kadan NUR ta bi bayansa.....ku je kawai tun muna sheda junna!"
Maman su Fa'iza ta dubi Aminiyarta , ita ma ta dubeta, tana dan zarro ido ta ce" To fah, dama ba wancen dake zaginmu daga cen ba ce ta haifeta, cabdijan to ai yarinya ashe daga tsatson yan girman kai ba'a tara ko sisi aka fito ba?????, lalle kuwa kawata kin hadu da jafa'i!"
Auntyn yara ta nufi wajen Babar tukunyarta ta warto marfin ta yiwo kansu gadan gadan
Da gudu suka nufi kofa suna ihun fadin da mahaukaciya ce?
Su mama ma da gudu suka yi dakin maman ita da kawarta sunna leken auntyn yara
Auntynsu na yara ta wurgar da marfin rai bace ta ce" Kika ce ke wata marar kunya ce! Aikin banza Dan kawai na zama Shara kowa ma sai ya kawon dati ya zuba min? Idan na cinye wulakancin ta gidan nan saboda mijina na kyale karya ne in kyale wasu a waje, Nur kuwa ba zata kyale d'an naki ba , idan har ya zo kofar gidan nan sai ta kula shi, aikin banza aikin wofi!"
Ta nufi dakin ta tana fada
Ido kawar maman yara ta zaro tana dubanta ƙasa kasa ta ce" Ke, dama matar nan mahaukaciya ce? Dama idan kuna fada rido ki take yi ?"
Maman yara ta sauke wata uwar ajiyar zuciya ta ce" Ke kin san dama Mutun ce mai rigima, son Malam da shegen son yi masa biyayya ya sa bata iya daga kai a duk abinda zai mata, kin san na fi fakewa ta kansa ya wulakanta min ita yadda nake so, to kwanakin nan fa ya rage yi mata, ke idan nace ga abinda ta min yanzu zaunar da mu yake yi a yi yar kuraya, idan ya gane abinda na fada ba haka bane a gabana a gabanta yake min tatas, shi yasa yanzu a hankali a hankali take iya min rashin kunya nima, Ni yanzu abinda ke bani haushi irin yadda take wani cika da hobara wai ita y'arta ta samu miji ko? Ai da gangan na sake dudurawa uwar saurayin zagi ta yadda zata tsine masa idan ya dawo inda yarinyar nan take!"
Kawar maman yara ta girgiza kai ta ce" Ke kam kina son gardama wallahi, kin ga ki je ki sa a maki abinda yar zata ringa bin maza ita kuwa wannan mai neman warto mutanen kawai ki sa a mayar da ita mahaukaciyar Shikenan su Bara maki gidan ki!"
Maman yara ta girgiza kai ta ce" Wai Ni? Ai karyar boka ya ci kudina, ke Ni fa ba zan bi malami ba, da kisa har fadan duniya an hada bale na gida talaka irin malan......, yanzu haka abinda ke raina na gaba shi ne in sa yar da kanta ta nuna masa in dai yana son ta ya so yayarta, shi yasa har yanzu nake kara hakura tana rabar inda nake, dan kuwa so nake yi ta Kore shi da kanta, in kuwa ya nace sai dai ya dawo kan A'isha idan ya so in ga cika da hobara ta iskanci wa zata ma,....."
Ta ajiye zancen kafin ta fitar da huci ta ce" Hum, in ba rashin tunani irin na matar nan ba yanzu har tunani take ina raye zan bari HALLAH ta yi aure? Lalle!"
kawarta ta girgiza kai ta ce" Lalle kina ganin Abu, Ni fa ba zan jure haka ba, zuciyata ba zata jure ba, shi yasa da asirin nan ya karye na kori Malam, dan ba zan iya ba, ace a gidana kake kuna min iskanci kai da matarka da yayanka, ai tunda ya mayar da gidan nan da sunana nace to a tashi a tashi, gwara in ci gaba da cin kasuwata a kofar gidana hankali kwonce, Ama ba zan iya wulakancin namiji da wata macen ba...., ke kina ganin bariki a gidanki!, Ama kin ga abinda uwar yaron nan ta fada da kawarta ko? Ina da yakinin abinda zai sa yaron nan ya ki zuwa gidan nan ba karami bane, haka kuma abinda zai sa ya yarda ta zo masa da maganar ya barta ita ya dauki A'ishan nan naki kamar an daurawa tabarya zani har ya yarda ba karami bane....., to dan iska ne shi hala?"
Maman yara ta dubeta ta ce" Kin ga tashi mu je in raka ki, kar aje matar nan wajen Malan suka nufa ya tardo ki gidan nan in shiga uku, ba zaki gane ba, IMTEE na min biyayar da bata yiwa kowa a duniya, Ni nake da hanyoyin da nake sakawa ta min biyayya ta ji tausayina ba tare da ta san ma ta yi ba, tashi mu je!"
Mikewa ta yi ta dauki hijabinta ta saka, sannan ta shiga cokala kafarta saboda gurguwa ce, kafarta ta dama a dan shanye take, idan zamanin sanyi ya zo ma dai ta saka sanda dan a haka bata iya taka kafar, ama a haka take ta fitina da mutane.......( Astagfrullah).
Ai kuwa suna fitowa sun dauki hanya da nufin tafiya me Muryar Malan ta sa Mama dakatawa da karfi zuciyarta na bugawa ta juyo da sauri a lokacin da malan dake dubansu da mamaki ya ce"*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE
MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????