Sashe 27
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ta kama habar zani ta shiga goge hawaye
Har ya so ficewa ya dakata sakamakon hango mamansa da Na'ima sunna leke daga ciki, ya tabbata kukan da matar take to daga ciki ta fito da shi
A dole ya dakata yana fadin " Subahanalah, Malama lafiya dai ? Wani abu ya faru ne ?"
Maman yara ta sake jan hanci ta dube shi ta ce" Kwarai baban IMTEE yana da gaskiya, ba abinda aka yi yaro, Allah ya baku hakuri"
Gabansa ne ya fadi, da sauri ya kalli mahaifiyarsa da ta taho da hijab din ta da sauri
Ransa ne ya fara neman ɓaci hadi da tsoro ya ce" Subahanalah, mama, me yake faruwa ne? Me ya faru? Me baban ya ce? Me Imtee ta ce????"
Maman yara ta kalli mahaifiyarsa sannan ta dube shi ta ce" Dangane da maganar kana so manya su san da kai a lamarin neman amincewar IMTEE, kai ne ka fada ko konge aka yi maka?"
Zuwa lokacin Na'ima ta iso itama , hakama Fa'iza ta yi Salama rike da leda jiki jiki da kaya a ciki ta yi turus da mamakin ganin maman gidan su Imtee a nan
Du irin yadda ya ji tausayin Na'ima da irin kallon da take masa ji yayi ba zai taba iya bari maman IMTEE ta fita a haka ba, haka kuma duda shi a saninsa maganar bata yi nisan haka ba, wato har iyaye su san da maganar da zafi zafi haka, ba zai ture ba, dan har ga Allah har ransa yarinyar ta gama tafiya da duk wani kutsari nasa
Da sauri ya ce" Eh mama, Ni ne na fada, dan Allah mu koma ciki ki zauna ki daina kukan nan"
Maman yara ta girgiza kai ta ce" Salon a sake min kallon mahaukaciya matalauciya?, abinda ya kawo Ni nan ba wani bane sai dan in sanar maka mahaifinta yace shi ba zai taba yarda ya tsayar da kai matsayin manemin aurenta ba bayan bai ga wani shakiki namiji naka ba, shine nace bari in sanar idan da gasken ake a san abin yi, ashe ashe Malan wulakanci ya gudar min Ni kuwa na kawo kaina? Allah ya sawwaka"
Daga haka ta fuzga ta nufi waje
Hannayensa ya dora saman kai, da gudu ya bi bayanta,
Mamansa ta zarro ido da karfi ta ce" Anas, ina zaka je? Kai Anas?,"
Na'ima ta ɗora nata hannayen itama a saman kanta ta fashe da kuka tana silalewa a nan ......
Fa'iza du ta rikice, ta zubar da ledojin ta kama Na'ima a tsorace tana fadin" Innalilahi, wannan fa Bama maman nata bace, kishiyar maman nata ce, itace maman A'isha ama ba ita ta haifi IMTEE ba, Subahanalah me yake faruwa haka, kin ga Na'ima tashi tashi kar ki bata jikinki dan Allah, tashi......."
Su suke wannan bidirin, a kofar gida kuwa maman yara ta ja ta tsaya sai yiwa Anas take yi da fadin cewa da bai nuna yana son yarinya ba ai da ba'a neme shi ba da ta rikice tace ita sai an bata dama ta bashi dama ya fara zuwa zance idan ba haka ba komai na iya samun ta ciki harda guduwa daga gidan, to kuwa ya san yadda zai yi tun wuri ya sama mata hanyar da zata ringa ganinsa kafin mahaifinta ya aminta da maganar soyayyar , dan ita ba zata taba kyalewa yarinyarta na kuka saboda shi ba
Maman su Fa'iza kifawa ne kawai bata yi ba daga tsayen da take, jikinta kuwa sai rawa yake yi da tarin tsoron wannan jarabar
A raunane sosai Anas ya ce" In sha Allah mama babu abinda zai samu Imtee, Ni mai sonta ne kuma zan yi du abinda ya dace dan in hana wani abu ya same ta, yanzu haka zan sanar da bafana ya je ya samu baban , in Allah ya yarda komai zai daidaita!"
Maman yara ta zuba masa ido, to fah, meye haka kuma, me zai daidaita kuma?, ..........
Anas ya ciro makulin mota ya ce" Mu je in kai ki gida mama, mu je"
Maman yara ta wani cira kai ta fita ta kuwa shige gaba abinta , shima ya shige ya tada ya dauki hanya, domin sai da suka fara tafiya ta ce da shi anguwa zata je ba gida ba, shi kuwa kamar an kuno shi haka ya juya ya kai ta har kofar gidan kawarta, wace ke kofa zaune ta kasa kayayyakin saidawa
A lokacin da mama zata fita daga motar ya jimko kudade masu yawan gaske ya miko da biyayya ya ce" Mama ga wannan a yi abin hawa idan aka tashi"
Mama ta saka hannu ta karɓe tana fadin" Au, harda wahala,? To Allah anfana, dan Allah ka hana mamanka zuwa gidan mu fa, dan kar tace zata je ta yi wata fitinar da ba anfani dan Malam na iya janye maganar gaba daya ma ya haramta maka Imtee"
Da sauri ya gyada kai yana tada motar, dan ya san wace tasa mahaifiyar shima, sam ba kanwar lasa bace, ba lalle ne ta tsaya wani abu ya cin mata ba, sai inda karfinta ya kare in ba shi ne ya dakatar da ita ba.
Yana tafiya maman yara ta juyo suka hada ido ita da kawarta
Bata ce komai ba ta wuce ciki ta shige cen dakin matar ta duka gaban gadonta madaidaici ta hade kai da jikin gadon ta fasa kuka tamkar ranta zai fita
Janyo kofar dakin matar ta yi ta saka sakata ta karasa da sauri tana riko maman yara ya zamo maman yara na kubcewa tana sake rikota har sai da ta yi kukan nan ta ji zuciyarta ta saku sannan ta Dubeta fuska du ta cabe mata ta ce" Ke Labiba ke Labiba wanga kuka haka ai sai zuciyarki ta buga, ke kuwa me ya yi zafi haka ,Malan din ne ya mutu?"
Maman yara ta saki bakinta da ta cije da karfi har ya fara kumbura ta dubi Aminiyarta tun ta yarinta, wace Allah ya sa har yanzu ita bata rasu ba itama suke kuma tare, ya zamo hali ya dan zo daya ta wasu ɓangarori sai zumuncinsu ya dore, bale irin yadda itama take da mugun kishi sai ya zamo lamarinsu ya zo daya ta ce" Na jima ina sa ran a shigo min da gawar malam ana kukan ya mutu, da na rantse maki da Allah ba zan yi kuka ba, saboda tun lokacin da aka ringa rangada guda aka shigo da mace gidana bayan na fara farin cikin mun rabu da kangin wahala Malan ya nuna min shi namiji ne ba dan goye bane shi ya kawo min macen da ta dauki cikin da na jima ina nema ban samu ba na yarda cewa Malan makiyina ne kuma nake harin rayuwarsa kamar yadda yake harin tawa, sai dai alamu nuna min suke yi zan yi in gama ne da wahala in har zan ci ribar wannan kokowa tsakanina da malam da matarsa, saboda kamar du abinda nake tonawa tarar da danshi da ni'ima suke yi idan suka fada........, Ama na rantse maki, koda zan tafi zigidir ne sai na ga kukan malam, sai na ga bugawar zuciyar matarsa, kuma sai na bine Imtee da Sulaimana da hannayena!"
Ajiyar zuciya uwar antu ta sauke kafin ta ce" Wannan kisan mummuke da kike yi, ina tsoron ke kuka fi jigata.....ina matukar tsoron halin da kike ciki sakamakon kisan mummuke da kike yiwa kanki da zuciyarki.......,"
Ta yi dan shiru tana kantso goro ta ɗora da fadin" Ni fa ina tsoron yarinyar nan ko Allah ne ke mata fada ....."
"Allah ita kadai ya halita?, tsabar munafurci ne da bin bokaye ya sa ta haɗa Ni da mijina da jama'ar gari har ake min kallon mahaukaciya " maman yara ta katse ta ranta na sake ɓaci
Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye ta ce" Waye wannan ya kawo ki?"
Maman yara ta zauna da kyau ta ce" Shi ne mai neman auren na IMTEE, hum, wai wannan mai kudin ne zai auri Imtee, Ni tsoro ma nake aje ya yarda ya auretan uwar ta fara daga min kafada a cikin gida"
"Wai yaya za'a yi ta daga maki kafada matar da kika riga jika amshe mata y'ar?, Ni fa gani nake yi ci gabanki ne in ma ya aureta!"
Maman yara ta girgiza kai ta ce" Bama zata yi aure ba, ba zata taba yin aure ba, a irin yadda yaron nan ke son ta itama zan cusa mata shi a zuciya ta yadda sai dai su ringa buya suna dirkawa juna ciki tana haifowa ina goyewa a filin gida, ba zan taba bari a kai ga maganar aure Bama tsakanin ita da shi, muna nan Ni da ke!"
Maman antu ta gyada kai tana jinjina bakar zuciya irin ta aminiyar Tata, kai ita da ta yi bakin kishin ta ga abin ya ki ci ya ki cinyewa hakura ta yi Walahi, Ama lamarin kawarta na bata tsoro ainun....., koda yake dan kanta haka ta ga rayuwa ta mata sai ta yi
Mikewa ta yi tana lalubo wajen kuna panka ta kuna mata ta ce" Bari dai in koma waje har ki idasa sakuwa kya fito mu yi zancen abin arziki dan du idan kika zo a haka din nan ba wani gane komai kike yi ba sai sambatun rahama, ke kam kin yi sake rahama ta gama da nutsuwar zuciyar ki"
Maman yara bata ce mata komai ba har ta fita sai sake kifa kai da ta yi tana ta tunanin hanyoyin da take ganin zata iya bi ɗan sake samun nasarar da ta dace da ita!.
Ganin har yama ta yi maman yara bata shigo ba sai kawai su A'isha suka nemi taimakon AUNTYN yara a lokacin da suka so cin abinci
Cikin hikima da jin sakewar zuciya AUNTYN yara ta ce" Me zai hana mu girka tare?"
A'isha ta kali Imtee, IMTEE ta ɗan sake satar kallon AUNTYN yara