← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 141

Sashe 76

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anas ya Dube shi da mamakin dan sir zai shiga ciki ne zai kore shi?, shi fa shi yasa wannan mutumen ke bashi haushi irin yadda yake nuna ya fi kowa kusanci da sir ciki harda shi???, mtssssssssss

Sai kawai ya juya ya fice daga wajen yana rage tsayi ya gaishe da IMAD wanda ya ɗan sake binsa da kallo bayan ya tafi kafin ya sake duban inda ta mike daga gaban Anna tana dariyar maganar da Anna ta yi cewar wai Farhana ce da sa mutun gyaran gashi, eh lalle bari dai a samu nutsuwa zata kai su Saloon ne dan ita bata wani yarda da wannan wankin kan ba

Shiga yayi , wanda shigar tasa ta sa Anna bashi hankalinta da kula sosai a lokacin da yace da ita likita ke masa magana ta mike tana fadin" Ko ta farka ne??"

Bai ce komai ba ya nufi office din likitan, wanda hakan ya sa Anna bin bayansa da sauri

Sunna shiga kuwa likitan ya sanar musu cewar ta farka, likita je ciki wanda ya shafi psychologue yana dubata da yi mata dukan bayanan da suka samu komai da komai har abinda ya faru yanzu, sannan ya sanar musu likitan ne yace yarinyar ta zo kusa da dakin da an bada dama a shiga da ita...........

Bayan ya ji bayanan ya juya ya koma inda su Nur ke zaune, daga ita sai A'isha, sai sojan nan dake tsaye kamar du Wanda ya taho ma dakatar da shi yake yi, su duka sun hankalta da haka sai suka dauka ai dan ogansa na nan ne yake tsarewar nan......

Basu ga tahowarsa ba, domin ba karan tafiya takalminsa yake yi ba, sai da ya tsaya a gaban su, ya zuba musu ido su duka, kafin ya dubi agogon nan na hannunsa ya sake sauke dubansa a kan fuskar Nur yana jin wani haushin yarinyar a cikin ransa ya dauke dubansa a nutse ya kalli Anna da ta karaso ita ma tana kokarin son yi masa magana, sai dai ta dakata tana jira ta ga abinda zai yi

A hankali ya ce" Wani yare kuka fi ganewa?"

Shiru suka yi, dan su sam basu gane inda tambayar tasa ta dosa ba, har sai da Anna ta Dube shi a tausashe ta ce" HAUSA suka fi ganewa" sannan suka gane yana son ya gane da wani yare zai musu magana ko me????

Kai ya gyada a nutse ya ce" Ban san ko kun gane abinda yake faruwa ba, ban san ko kun san abinda yake faruwa ba, ban ma san ko hakan nada mahimmanci a wajenku ba..........., dan ban ga alama ko daya a tare da kowace a cikin ku ba......."
Ya karashe yana nuna su su dukansu, wanda hakan ya sa A'isha sake sada kanta zuciyarta na ta bugawa, domin du wannan abin da take yi kokari take yi ta ture komai a ranta dan kar abin ya zame mata damuwa................, sai dai a yanzu da bawan Allahn nan dake yi mata kwarjini matuka ya tsaya a gabansu cikin shiga ta kamala kansa dauke da hula madaidaiciya sai dan karamin carbi a yatsarsa fari kal kamar jalabiyar jikinsa tamkar yau ya fara amfani da su ma, ga kanshin da ya gama cika musu wajen sai tsoro da firgicin da take ta gujewa ya nemi dawo mata sabo dal........., ita kuwa yaya za'a yi ta iya yafewa mama a duniya? Ta ina zata bi ta iya yafewa mama??????

Anna a tausashe ta ɗan daga hannunsa ta ce" Andadi"

A hankali ya Dube ta ya ce" Anna......,ina so in san anya yaran nan sun gane girman abinda ya shigo rayuwarsu a yau? Saboda tunda abin ya faru banda yarinta ban ga komai a tare da su ba............, rayuwar mamana ake magana"

A hankali Nur ta sake riƙe hannun A'isha, zuciyarta na tsalle fiye da kima... ..............

Maganar da yake yi, na fama mata abinda take danewa dan kar yar uwarta ta yi tunanin bata taya ta farin ciki da samun wannan labari mai daɗi a wajen ta ba, domin ta sani cewa A'isha zata iya yin farin cikin wayar gari ta ji cewar ba mama ce mahaifiyarta ba, kwarai ta san da wannan, shi yasa take yi kamar bata san ciwon kanta ba, kamar abin nan bai gigita mata rayuwa ba, har ma ta kasa yarda su yi baban zama ɗan tana tsoron ta ga fuskar abansu, bata san me zata iya gani a fuskar abansu ba, bata san abinda zata gani dangane da abinda ya faru in har zuciyarta zata iya kuma dauka ba, tana yin du abin nan ne dan ta taya yar uwarta fuskantar abinda ya tunkaro su..................

A nutse ya sake duban su ya ce" Ta samu attaque ne, saboda chok din abin da ta rayu cikinsa......., ita din Mutun ce mai mahimmanci mai daraja sosai....., a yanzu likita ya bada damar ta shiga, ina so in gane kun san darajar abinda take ciki ko yarintar nan ta fi damun ku.....???"

Da sauri Nur ta dago idannuwanta da suka yi hulu hulu ta saka a cikin nasa, a karo na ba adadi da irin haka ta faru da su a yau

Ido cikin ido ta furta" Daraja???"

Da sauri A'isha ta rike hannunta a hankali ta ce" Ki yi shiru"

NUR ta bi hannun da kallo, ta sake dubansa.........

Ta mike tana jan hannunta ta zagaye su a hankali da nufin fita............

Har ta kusa ta dakata ba tare da ta juyo ba ta ce"Sanin Daraja da tausayin Uwar da ta rasa y'arta tun a zanin goyo har abin ya zame mata irin halin da take ciki ya sa muka tursasa kanmu, muka zo da kafafuwanmu, muka ture baban abinda ke gigita mana tunani, muka zabi yin murmushi maimakun ihun kuka, har muka zo nan a yanzu ne ya sa zamu kara jajircewa ita ta samu Salama kafin da kokon bara mu....."

"Ki kama bakin ki, ki fita!" Aliyu ya fada yana kiyaye hada idannuwa da ita hadi da kiyaye dubanta baki daya ma

Anna dake cike da gudun haka ta faru ce ta ce" Aliyu, ka barta, ba muguwar magana take son fadawa uban gidan ka ba"

Aliyu ya sada kai cike da girmamawa ya ce" Anna, ki yi hakuri, ta fita!"

Daga haka ya ja hanya ya sake sada kansa ɗan girmamawa a wajen Anna, da kuma hana wata baraka fitowa a garun da yake yiwa kallon ginin bulo ne zai hau kai.

A'isha ma mikewa ta yi da sauri, dan gaba daya sai jikinta ya dauki rawa...tsoro ya kama ta

Anna ta sake duban sa bayan ta rike hannun A'isha, haka kuma ta ce da NUR ta dawo mata, ta ce" Ba ta haka zaka daidaita abin nan ba, ka sani kwarai sun san abinda yake faruwa, ka kuma yi musu uzuri na wani abin , ba kowa ke iya kadaice kansa idan yana cikin tashin hankali ba"

Nur Dake tsaye kanta a kasa a hankali , cikin gargadar murya ta ce" Anna, ki yi hakuri , ina waje"

Da sauri Nur ta fice , wanda hakan ya sa ya dauko idannuwansa da suka masa ja ya sauke a bayan ta a lokacin da ta fice da sauri , a hankali ya shiga murza agogon nan wanda Aliyu ya bi da kallo ya juya da sauri ya bi bayanta shi ma

Anna na duban Nur ta kama hanya ta tafi, kuma Aliyu ya mara mata baya, ta dubi IMAD a tausashe ta ce" Idan ka san ba zaka iya fahimtar yaran nan ba, ka yi hakuri ka barni da su, Ni na san cewa ba zasu taba yin wani abin da zai dagula lamarin ammanka ba"

A'isha ta gyada kai da sauri ta ce" Eh, dan Allah ka yi hakuri Elhaji, Nur bata yi haka dan rashin kunya ba, dan Allah ka yi hakuri"

Dubanta yayi, sau daya, kafin ya dauke kai ya nufi corridor din da dakin da Mama take ciki, hakan ya sa Anna kamata suka nufi wajen a hankali tana rarasarta, dan ba zata so yaran su ji wani abu marar dadi ba, zata so yayi hakuri su fuskanci juna......

Da sauri Nur ke tafiya , tana kokari rike hawayenta........, A lokacin ne Farhana ta hango fitowarta da yannayinta ta taho da sauri tana tarbarta Aliyu na biye da ita shi ma, ya budi baki cikin Yaren turancinsa ya ce" Ta je mota ta zauna"

Motar da ya nuna FARHANA ta kalla, da mamaki ta Dube shi ta ce" Yaya Aliyu lafiya dai ko? Me yasa zata je mota ta zauna? Motar ma ta yaya???"

Aliyu ya Dube ta, ya rasa me zai ce mata matsayin amsa

Ganin haka ya sa Abdallah yi masa tambayar me yake nufi????

Da girmamawa ya ja Abdallah suka yi nesa da su, ganin haka ya sa Farhana kamata da kyau suka nufi kasan rumfar nan suka zauna, tana dubanta da kula ta ce" Nur, me yake damunki ne wai? Me yake faruwa ne haka? Kukan me kike yi kuma???"

Nur ta dubeta ido cikin ido, kafin ta saka hannayanta a tafin fuskarta ta fashe da kuka a birkice ta ce" gaba daya wace irin rayuwa ce na yi Ni?, wace irin rayuwa ce na yi?........., a yanzu wace irin rayuwa ce zan yi?......., na rayu ban san ciwon kaina ba, ban san komai a cikin zaman rayuwa ba, hatta sallah ban tsaida ba, a haka a hannun matar da nake ganin ta fi kowa so na? A yanzu kai tsaye a tafi da ita ba tare da ta bani amsoshin tambayoyina ba?, wai me ta so na zama a duniya? Me ta yi da Ni?????, yaya za'a ce an tafi da ita ban, ban ji me yasa ba? Du yadda nake danewa dan abin ya wuce an fi karfina an sa dole sai na fada????"
Chapter 76 · 0% Book details