Sashe 103
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da hannu ya nuna mata wajen zaman direban kafin ya shige inda ta tashi ya zauna yana dafe kansa......
Da sauri ta zagaya ta shige gaban ta rufe motar a hankali ta saka belt, kasa kasa ta saci kallonsa , sannan ta dora kafarta ta dane wajen birki, da dayar kafar ta dan dora saman accélérateur, sannan ta duba wajen giyar, kafin ta daga birkin hannun da ya ja ya tsayar da motar kansa tsaye ta daga shi a hankali ta dage kafarta dake kasa wajen birkin sannan ta shafa wajen karin gudu ta dauki hanyar gidan cikin maida hankalinta kan tukin kamar yau take gabatar da tuki gaban iko dan amsar takardar shedar ta iya tuka mota
Hankalin Anna a kansa, du hankalinta a kansa , har suka iso, masu tarbar su suka bude musu , du suka fito daga motar , ya zamo yana fita sai ya juya da nufin tafiya bangarensa ba tare da ya biya kan kowa ba......
Da dan sauri bayan Anna ta ba FARHANA umarnin su je gatanan zuwa, ta bi bayansa a lokacin da yake taka matakalar bangarensa ya haye ta furta" Andadi......"
Dakatawa yayi, sannan ya juyo ya sauke dubansa a kan Anna
Alamun lokacin sallar isha'i ya gabato ta waiga ta waiga sannan ta Dube shi a tausashe ta ce" Jikin ne?, baka da lafiya ne???"
Dawo da ƙafarsa yayi daf da Anna, ya kama hannun Anna ya shiga fadin" Sam bata da hankali, bata da nutsuwa, bata da kamun kai, bata kiyaye du wani abin da zai iya dagawa mutane hankali, bata da komai sai neman fitina, ta yiwu ma aljana ce, saboda ita kadai ce idan na gani nake palpitation, du in na ganta sai raina ya bace, ita ce ke bata min rai, tana daga min hankali........., ta da ba zama mutun mai taba hannunta dan in kiyaye bacin ranki, ta sa du idan zata fito sai gabana ya fadi da tunanin kar aje ta fito ba sutura a jikinta ki gani ranki ya bace...... Anna ki yi gaggawar cire ta a rayuwana, idan har zaki ci gaba da nuna mata damuwa a dukan abinda take yi , Ni ma zan damu da ita a duk motsinta, hakan na nufin zan ci gaba da zama hankalina a tashe....., i i cnt lv like.....like....."
"Andadinine......?" Anna ta fada a mugun tausashen da ya sa ya tsura mata ido a hankali kafin ya shiga dawowa hayacinsa da tuna abinda ya fada hadi da son gane dalilinsa na fadin haka
A tausashe Anna ta ce" Menene? Wacece ke bata maka ran har haka????"
A hankali ya lumshe idannuwansa, kwarai ko a yanayin da ya rike hannayenta jikinsa da zafi......, wanda ke nunin abinda yake fada ba wasa yake yi ba, ba kuma daga fatar bakinsa kawai batun ya tsaya ba
A tausashe Anna ta ce" Andadinine, yi min magana, menene?"
A hankali ya sake bude idannuwansa ya sauke a kan fuskar ta............
A tausashe ya iya budar bakinsa ya furta" Ba kowa......, zan je in yi wanka dan in samu sallah a kan time, sai na shigo"
Bai iya tsayawa ya ji amsar Anna ba ya juya saboda yadda kansa ke sake daukar caji saboda tunanin da ya gama hadewa a kwakwaluwarsa.......
Anna ta jima a tsaye, tamkar an dasa ta, zuciyarta na bugawa, hankalinta na neman tashin ita ma
A hankali ta juyi saboda shigowar mota bangaren wace ta tabbata Aliyu ne kawai ke iya yin haka bayan shi IMAD din
Saukowa ta yi da dan sauri ta karasa inda ALIYU ya fito yana kokarin ida rufe motar
Yana gannin Anna ya juyo da girmamawa ya yi mata sanu da karasowa gida
Anna na dubansa ta ce" Aliyu, me yake damunsa?, na san ko me yake ciki ka fi kowa sani, wani lokacin kana rigayarsa gane abinda yake ciki......., tl me, wacece wannan? Me ya haɗa su?, me aka yi? Me yasa yake tunanin wasu maganganun daban da na kasa ganewa inda suka dosa??????, Aliyu????"
Aliyu da kansa ke ƙasa, a hankali ya dago dubansa ya sake duban Anna , a hankali ya fitar da numfashi kasa kasa ya ce" Anna, yana rasa abinda zai yi du idan tana waje, in muryarta ya ji ko me yake yi zai ajiye ya Dube ta koda a Boye ne......, yana labewa a bayan cewar kawar FARHANA ce, y'arki ce, kenan ita ma kanwarsa ce yana gaggawar daukan fushi da ita , yana saurin tare du wani abin da ya nufe ta, .........Anna a tarihin du wani abu da na yarda cewar yana so har ransa ban taba ganin wanda yake yiwa irin wannan kulawar mai tafe da tsananin tsoron rasawa idan ya nuna din kamar yarinyar nan........, a yanzu zan iya ce maki ya kai matakin da nake tsananin gudun ya kai, saboda a yanzu ya kai wajen da idan ta yi kuka zuciyarsa ke yin kuka......."
Yayi dan shiru kafin ya ɗora da fadin" ki yi hakuri Anna, ta yiwu maganar nan du bai dace na fada maki ba, Ama abu ne serius wanda nake nan ina bi a hankali har ya bani damar da ko tana so, ko bata so zamu rufe mata kofa kuma dole ta yi biyayya............sai dai"
Ya kara yin shiru kafin ya ce" Sai dai shi da kansa bai yarda da abinda yake ciki ba, hasalima ba so yake yi ya ture da karfinsa dan karyatawa yake yi, ....so yake yi ya nuna Bama wani hadin......., sai dai Anna ya riga ya makaro , ya riga ya fada tarkon abinda ba'a isa a iya juyar da shi yadda ake so ba Anna, kuma da ya tashi fadawar ya fada kan wace dukiyarsa......darajar da gare shi a duniya da cikin gidan nan, tsarin da Allah ya masa wanda ke jan ragamar wasu matan sosai dan zuwa inda yake, ita sam bata ma kula ba har yanzu bale har in sa ran ita din ma zata Dube mu........, Anna na fi shi shiga tashin hankalin haduwarsu saboda na san ko yaya muke cikin firar dadi yanzu zai zama kurma har sai ta bar inda yake........"
Anna kam mamaki ya gama kashe ta a tsaye, ita tunanin da ta yi ko wata ce suke fada sai abin ya juye da tunanin nata da tarin mamaki take kallon Aliyu saboda abinda ta gama fahimta dake sake yi mata gardama a kunnanta......m
Dama Akoy wata mace da zai so sama da matarsa ne?
So din ma a kusa kusan nan?
So din ma bayan abinda matarsa ta yi dan ya zamo na ita kadai wanda ita ma ta san cewar shi ne ta yi kawai ba hurumin ta bane ya sa bata yi magana ba saboda da ace yarinyar ta dauketa uwa da tuni ta yi mata wankin baban bargo sanadiyar wannan abin da ta yiwa jikinta saboda namiji?
So din ma, a irin lokacin nan da ba'a tsamaninsa?
So din ma, mai karfin da bata taba ganinsa a irinsa ba?
So din ma da matar da ake nufin baya gabanta??????????!!!!!?!!!!!!!
Wacece? Yar waye? A saudiyan take? Meye tsadar sadakinta? Zinariya? Lu'ulu'u, tsantsan kudi, ko wani hukuncin take tafe da shi mai tsadar da zai fi karfin d'anta?????
Aliyu da kansa ke ƙasa cike da tunanin anya yayi dai-dai da ya fadawa Anna abinda ogansa ma bai yarda cewar a halin da yake ciki kenan ba ??????
"Wacece?, Aliyu wacece?" Anna ta fada tana tsare Aliyu da ido
Aliyu ya zubawa fuskar Anna ido, kafin ya dauke idannuwansa a hankali ya ce"Kisan mummuke page 64
Da girmamawa ya ce" Anna, ai NUR ce"
Da farko Anna kamar bata ji da kyau ba, hakan ya sa ta dan karkatar da kanta ta ce" Na'am?"
Aliyu ya dan shafa kansa ya sake furta" Nur ce "
Anna ta zarro idannuwanta sosai tana waigawa bangarenta ta nuna ta ce" Tsaya, wace Nur? Y'ata?"
Aliyu ya sada kai ya furta" Ita ce...."
Nan da nan abubuwa suka shiga dawowa a kwakwaluwar Anna
Bale abubuwan da Farhana ta fada cewar ko ta rungume shi da ta Tsorata?
Da irin yadda ya so fada mata a wajen kicin ya share
Da irin yadda du idan ta wuce koda da yan sekwani ne sai ya bita da kallo da irin yadda yake dauke duban nasa a kanta kamar an masa dole
Ya rab .....
Aliyu a tausashe ya ce" Anna plz , ki taya Ni, wannan abin nema yake yi ya fi karfina saboda sam ya ki yarda ma, kuma ita din ma so take yi ta saka shi a halin da hankalina ba zai dauka ba, sai wasu kananun samari yake kulawa tana bata masa rai"
Anna ta kara duban Aliyu still a cikin yanayin mamakin nan take, ta nuna da hannunta ta ce" Ni zan taya ku?"
Aliyu ya gyada kai fuska a marairaice
Anna ta sake dubansa kafin ta dafe haba ta yi wani murmushi irin na wayayun datijai ta juya zata yi tafiyarta
Aliyu da sauri ya ce" Anna, baki ce komai ba"
Anna ta juyo ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" ka san me? Gaskiya ku san yadda zaku yi, ama y'ata ban ma gama tunanin da irin abinda zaku bani sadakinta ba, wai idan ma kun yiwa kanku wa'azi kenan kun mike kun karbi abinda kuke so a kan lokaci, domin babu mai hana ta kula mai son ta ko waye, Ni ce nan zan karbe shi ko waye....... Bayan wannan Ni ka Ai ba zan ba y'ata mai mata ba ma, ba zan ba y'ata wanda bai nuna mata so ba, ba zan iya ba y'ata Bama wanda yake mata kallon mahaukaciya, ka yi kokari ka sama masa maganin jirin nan, dan kuwa nan da kake gani na zan taya shi aikin kurumcin da makantar ne."
Daga haka ta yi gaba ta nufi bangaren ta hankali kwonce tana murmushin da ita da kanta idan za'a turke ta a yanzu ace na menene bat da gamsashiyar amsar da zata bada