← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 141

Sashe 44

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ya dan girgiza ya mayar da dubansa kan Inna wace ke kara duban MAZNA dan har dan kara matso gilashinta ta yi da kyau tana dubanta

Kasa kasa ya ce" Magani ta sha suka rage"

Inna ta Dube shi da mamaki ta ce" Kai kar ka daukeni shashasha mana, a gidan uban wa aka yi maganin dake mayar da tulun nono yan tsuwat???, to ko haihuwa ta yi ta shayar suka zama uwa slifasss ba tudu akoy matarin nono wanda in ta tare za'a ga cikarsu bale Tun barin da ta yi Ni dai ban ji ta haihu ba, ANNA Ko ta haihu baki sanar min ba? Ko an sanar min na manta????"

Zuwa yanzu hannayen MAZNA rawa suke yi sosai, wanda hakan ya sa IMAD dan zuba mata ido da mamakin yannayinta..........

Abinda ya sa ya yi mamakin yannayinta ai ba yau Inna ta saba sakota a gaba ba

Kai a lokacin da ya ringa kwatanta mata Inna sai da ya ganar da ita cewa hatta mahaifiyarsa bata bari ba kafin ta gane ta ba kanta lafiya da wasu halayar na Inna........

Kwarai ya san cewa ko me Inna zata fada ba zai taba razana MAZNA ba.....Ama hannayanta na yanzu ya bashi mamaki ainun

Inna ta mayar da mayafinta baya ta tabe baki tana dauke kai ta ce" Ta yiwu kuma lalatar da ta shigo duniya da akace ana yi ta yi, tunda ya'yan yanzu ba abinda ya gagare su, Allah ya da ba zuwa kika yi aka cire nonon ba, nono ai alkhairi ne , ba zaki san dadinsu ba sai kin haihu, tsayin nan nasu zai sa kina sha'anin gabanki yaro na sha ba wata damuwa, Ama idan har taba su aka yi aka mayar da su kananu ke kam ai kin yi asara ko Yarona????"

Abarbar da take kara gyarawa da yar karamar wuka ce ta wuce mata ta yanke kanta da yanka mai girman gaske domin nan da nan jini ya bale mata

Da sauri JAUHARA dake ji kamar ta ja sunan Inna ta yi mata na maguzawa ta mike tana nufar auntynta tana fadin" Subahanalah aunty kin yanke"

A lokacin ne Anna ta dubo inda take da sauri tana mikewa ta furta" Subahanalah, ya aka yi?, Subahanalah kai kamar baba ne fa? Ajiye ajiye maza mu je ciki a wanke a daure ajiye wukar"

Wukar ta saki tana mikewa ta kai dubanta kan IMAD, wanda ya yi alamun tashi, sai dai ganin Anna ta rikota ya koma yana dubanta a hankali ya furta" Sanu"

Sai kawai ta dauke dubanta idannuwanta na cika da kwallah Anna ta yi elevator da ita dan su je ta wanke mata ta daure mata idan kuwa abin yayi yawa sosai a nemi likita.

Sunna shiga ya dubi Inna ya ce" Kin ga, idan kika ci gaba da zagar min mata zan tashi in yi tafiyata, yaya zaki ce wai ta yi surgry? "

Inna ta Dube shi tana kame haba, ta dubi FARHANA ta ce" Ke Farha kin ji da kunnenki nace matarsa ta yi surgry?"

Farhana ta sada kai ba tare da tace komai ba a ranta tana ayyana ' Ni kar ki saka ni a masifa, ama dan Surgry kam matarsa ta aikata , dan Walahi duwawun nan ba nata bane, kan uba, dole ma mu yi soyayya da Fu'ad dan in ji komai sala sala, ama kuwa lalle idan haka ne MAZNA ta fi Ni BALAKI, sai in shafa mata lafiya kai.......'

Ya jiyyar da kai yana daure fuska ya ce" tashi ki goge wajen nan kuma ki zuba mana abinci"

Da sauri farhana ta mike tana furta" To yaya"

Dan kuwa ta san a nan dai ai ba zai tasar da maman babansa ba ta yi aikin nan, da ita dai yake ita baiwar Allah, to ta yayama wannan matar zata iya aikin nan? Hum ita dai a rufa mata asiri a barta ta kara gaba, ba zata taba iya rayuwa a wajen da Inna take da ƴaƴanta ba, idan akace sai ta rayu a haka wata rana kasheta zasu yi tabasssss

Da kula Anna ke ta bin MAZNA da sannu, iman da ta zo saukowa ta hadu da su ta bi bayansu tana tsaye itama tana yi mata sanun har Anna ta daure mata yatsar da kula ta ce" Sannu MAZNA, Allah ya tsare gaba, zaki sauka ne ko .......ko sai Inna ta hayo??"

MAZNA ta rasa me zata ce, zuciyarta har bugawa take yi idan ta tuna tsohuwar nan, ita har ga Allah bata san cewa matar nan da hankalinta har yanzu ba, da bata yarda ta fito da abayar nan mai iya nuna yannayinta a yanzu ba dan ta san halinta sarai, kadan ma ta mata da ta tsaya a haka

A hankali ta ce" Zan sauka Anna, na gode"

Anna ta yi murmushi ta juya tana fadin" Idan kin dan huta sai ki taho, iman zauna a wajen ta sai ku zo tare"

Daga haka ta fice ta barta zaune saman kujera a falon dakinta

Bayan Anna ta fita dakin ta bi da kallo

A lokacin da aka gama ginin nan aka zuba kaya da suka zo suna bin dakuna wannan dakin ta yi zaton nata ne...

Saboda dakin ya haɗa girma da duk wani abin da zata iya buƙata.......
A dakin dakuna wajen uku ne, kowane da bayinsa......

Kai duk wani mafarkinta a dakin nan ya kare, sai dai suna tasowa ta gane cewar dakin nan fa na mamansa ne, hasalima su nasu bangaren daban, haka kuma nasu na nan din fale daidaya ne sai bayi kawai a ciki, daga nan ginin gidan ya fara bata haushi , a kullum kuma tana jira ta ga ranar da zata zo ta dawo nan da zama!.

Anna na tafiya zuciyarta cike da tsoro da firgici......

Allah yana gani sam bata so saka abin nan a rai ba, Ama lamarin da gigitarwa.......

Kwarai ana gyara harda na mamaki, gyaran da idan aka jajirce ana iya samun sakamako mai kyan gaske, Ama jiki irin na MAZNA , da wahala a shekara daya ma ya dawo irin wannan na yanzu bale a wata biyu kacal, domin rabonta da ta ganta an yi wata biyu, tunda ta zo ta gaishe ta a tsaitsaye ta wuce................

Elevator na budewa ta fito ta karaso ta zauna ta samu sunna taba abinci , ta sauke dubanta kan Farhana da kula ta ce"Anna na duban FARHANA ta ce" Farhana, tashi ki duba min idan yayun naki sun farka mana, dan a kai musu abinci rana na yi fa"

FARHANA ta mike ta ce" To Anna "

Anna ta zauna tana duban dauke kan da Inna ta yi, da kuma hade fuskar da IMAD yayi, ta yi murmushi bata ce komai ba, har sai da suka gama cin abincin sannan ya kamata ya kaita dakinta saboda hutawar da take yi warhaka, ya dan jima ma a wajenta kafin ya sauko kasa yana duba time dan kar aje lokacin sallah yayi bai sani ba

FARHANA kuwa a lokacin da ta zagaya bangaren da bakin suke a wajen shan iska ta samu Yaya Mutalab yana waya da mahaifinsa, murmushi ta yi bayan ta ɗan daga masa hannu saboda ba zata katse masa kiran ba

A tausashe ya yiwa mahaifinsa Salama, dama yana sanar masa cewar shi fa ba yau zai juyo ba, ya kuwa ce ba damuwa ai yana tare da IMAD ne.

Mikewa ya yi da sauri yana kallonta kafin ya yi murmushi da kara ji a ransa eh, da ya zauna bai dauki muguwar décision ba. a tausashe ya ce" FARHANA"

FARHANA ta karasa inda yake da kula, hankali kwonce ya mika masa hannu ta ce" Yah akhee, Barka da hutawa.... Yaya gajiya???"

Hannun yake kallo, kafin ya mayar da dubansa saman fuskarta

Bai kama hannun nata ba, sai ma harde nasa da yayi a kirjinsa ya ce" Barka kadai, ......."

Sai yanzu ta dubi hannun nata, kafin ta janye da sauri tana dan zarro ido,

Baya ta duba da kyau ta tabbatar ƴaƴanta bai biyota ba, ta rage murya sosai ta ce" yaya Mutalab, hannu da na baka dan mu gaisa ne kawai a matsayinka na yayana, ka san mu a nan muna yin haka ba wata damuwa bace, kuma abokin yayan mutun yayansa ne, du wani abu da yaya ke iya yi da kannansa yana iya yi da su shima, du abinda kuma ya haramta to shima ya haramtar masa....."

A yanzu kam shi din ne ya yi wani shiru yana kallonta , shi gaba daya ma sai ta nemi saka shi a halin kaka naka yi

Da sauri ya girgiza kai ya ce" La, ba haka bane, Farhana Ni ba muharaminki bane, ai kin san wannan, ba wani abu da ya danganci taba hannunki da yaya IMAD zai yi ya zamo Ni ma ya halastar min, haka kuma yaya IMAD ba aure tsakanin ki da shi, Ama Ni kin ga ai aurenki zan yi ko????"

Farhana ta Dube shi da sauri saboda furucin da ya yi na karshe...............

A hankali ta ɗan ja baya kadan tana boye hannun nata a bayanta kafin ta Dube shi ta ce" Dama, dama Anna ce tace in zo in gani idan duka kun farka a sake kawo muku abinci"

Ido ya zuba mata , wata yar fargaba na son kama masa zuciya.........saboda koda bai wani yi nutso sosai a harkar soyayya ba, yana iya gane macen da ta karbi kalamai irin wanda ya shigar a gare ta a karron farko, da wace bata karba ba sam

A hankali ya matso takun da ta kara , wato ya cinye su , yana dubanta ya ce" Farhana......., baki ji abinda nace ba?, ..............nace ni zan aureki"

FARHANA ta sake duban fuskarsa mai dauke da cikakken saje kamar ta yayanta,
Chapter 44 · 0% Book details