← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 141

Sashe 113

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rikice Anna ta waiga , ta waiga ta ga ba wanda zai iya rike mata shi ko ita, gasu a kicin kar ta kai Andadi bango Ya hurma mata wuka ma a shiga uku, sai kawai ta yi hanyar waje tana duban Nur wace ita kadai ke nan da karfi ta ce" Nur, dan Allah rike ta kafin in kira abokinsa ya fitar da shi ya tafi da shi, rike ta kar ta je inda yake, JAUHARA ku kama yarinyar nan wallahi bata san waye mijinta idan ya kai wannan matakin a bacin rai ba, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une!"

Nur sai ta rasa me zata yi, domin Jauhara a rikice ta shiga kiran dan uwansu dan shi ne namiji shi zai iya kinkimar yayarsu ya fito da ita......, ya zamo Nur din ce kawai ta iya bin bayanta da dan gudu , ta hange shi tsaye wajen pampo ya sa kansa kasan ruwa , ruwa na sauka a jikinsa....................., ya zamo MAZNA ta sake nufarsa,

Tana daf da kiran sunanta dan ta juyo su fita, ta ga ya juyo da jalabiyar nan tasa da ta jike, lokaci daya ya kama rigar zai sauke...............

A haukace Nur ta shige ta karasa inda yake ta rike hannunsa da hananyenta biyu a rikice tana girgiza kai zata yi magana MAZNA ta karasa ita ma a dagule ta kama hannun NUR ta sauke da karfi rai bace ta nuna mata yatsa ta ce"

Mun higa uku me zai yi a nan a gaban Nur?😭😭🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️Kisan mummuke page 71

Rai nace Mazna ta ce" Ki daina gigin kai hannunki jikin mijina, ke wai dole sai kin gwada min karuwa ce ke?"

Gaban Nur sai da ya fara yankewa ya fadi, kafin ta dubi Mazna a tsorace, sai kuma ta dubi IMAD da ya zarro ido yana dubanta

Lokaci daya ta ɗan ja baya kafin ta juya da nufin tafiya, sai kuma ta juyo tana dubanta a hankali ta ce" Na zata kina da hankali, na zata kina da girma kamar yadda mijinki yake da shi.......har na so girmama ki, Ni na zata kina da daraja fa......, har na so darajaki....., abinda ya faru da Ni da ke Wancen lokacin na zata rashin fahimta ta da kika yi tunanin mutum mai daraja irin mijinki, da ake girmama shi saboda addininsa da kiyaye dokokin Allah zai iya rungumar wace ba muharamarsa ba dan jin dadi, a waje mai daraja irin cikin gidan mahaifiyarsa, a waje mai kiman da bai fi taku uku zuwa dakin mahaifiyarsa ba......walahi na ajiye haka a matsayin tarin kishi irin na wasu matan ne ya sa har kika yi tunanin mijinki zai aikata maki irin wannan danyen aikin.......ashe baki da hankali ne? Ashe sam ke baki da tunani ne?????....."

Bata gajiya ba ta Dube shi , sam bata damu da yanayin da girarakinsa suka yi na mamakin jin kalamai na mai hankali daga bakin kandalar Anna ba, ta ɗora da fadin" Kar ka wulakanta kanka saboda bacin rai, me kake son yi in ka cire riga a nan? Kowani banza ya ganka ba suturar da ya saba ganinka?, idan ita horata zaka yi , mahaifiyarka fa? Ko ita ma laifin ta maka fa zaka horata ta hanyar aikata wani abin da zai sa ta ringa jin kunyarka tun a duniya?....., ba laifi zaka aikata ba dan ka aikata, saboda matarka ce ai......ama kuma AKOY kunya, AKOY yakna, AKOY girmama manya a cikin tarihin mu.........., kar ka yi abinda zuciyar mai hakuri da kawar da kai zata girgiza mana....., kar ka Bara mana abinda zai sa mu fara ganin daidai kake da mu, saboda yaro aka sani da aikin ganganci ba baba ba ko......"

Tana gama fada ta cire idannuwanta daga kansa ta dake duban MAZNA dake girgiza tana dubanta ta ce" Ke har kin isa ki fada min abinda ya dace da wanda bai dace ba da lamarin mijina?, wace ke da zaki ma mijina wa'azi ko ki ce zaki koya masa rayuwa?, in me yayi niyar yi da ni a inda yayi niyar yi na bashi kaina dari bisa dari, in ba karuwar bace ke , a ina kika san abinda yake da niyar yi da Ni a yanzu har ranki ke bacewa kina fakewa da nufin zaki hana shi yi saboda Anna? Kishi kike yi dan mijina zai kwonta da Ni.........?"

Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, yanzu kam a hasale Ya juyo da nufin dauke fuskar Mazna da marin da zai da ta dawo hayacinta.....

Sai dai bai kai ga yi din ba, Nur ta dawo a haukace ido rufe ta kaiwa bakin MAZNA dukan da ya da ta kwala kara ta duka ta rarumi takalminta mai dan tudu ta yi kan NUR.....itama ta yi kanta gadan gadan rai bace tana fadin" Kina tunanin tsoranki nake yi hala? Ni zaki kira da karuwa? Da uban wa kika kamani ina karuwancin???????.."........

Bai taba tunanin ganin abin nan a gabansa ba sai yau, hakan ya sa kawai zuba musu ido hadi da dafe gaban goshinsa....har sai da Muryar Inna ta sa ya juyo da sauri , ashe ta karaso kicin din tana tafa hannu ta ce" Kar ki yarda sai kin kwaci hakinki jikata , aikin banza yi mata tankadeta mareta ta yadda ko wani ta ji zai zage ki gobe zata Hanna, yau ga wulakanci, a kan me zaki ce da jikata kawura? To uban waye karuwin nata???????"

Sai ya samu kansa da yin tsuru yana kallon Inna da ta nufi wajen muciya tana kokarin daukowa....ko me zata yi da ita ????

Anna kam a lokacin da ta fita a gigice bata kula da su Farhana dake zance a gefe ba, da sauri ta nufi bangaren baki , hakan ya sa su Farhanan bin bayanta saboda yannayinta ba lafiya ba.

Tana karasawa ta samu Abdul Fatah na kai kawo da takardun da Aliyu ya kawo masa, ya kai minti goma da ya dawo, yana zuwa kuwa sai ya ji baya a sadade ya samu Abdul Fatah da Abdul bassit da dukan bayanan da ya samo, harda yaron da ya tura message wanda matse musu lamba da yayi ya da suka masa binciken da suka gano harda tafiyar da shi ya Boye firarta da kanwarta, harta message din da ya tura, dan haka ya maka masa ankwa ya jefa shi bayan mota rai bace ya fara zuwa ya sanar musu komai, da yanayin bacin ran ya sanar musu cewar shi ba zai iya tunkarar ogansa da maganar nan na, magana ce mai girman gaske dake iya fitar da shi a hayacinsa......, ya tuna musu waye Imad a bangaren kare hakkin iyalinsa, ya tuna musu waye shi a bangaren kiyaye dokokin Allah, ya kuma sanar musu kwarai lamarin nan na iya sakawa ya sake ta ma, shi kuwa ba zai so haka ba, kuma idan ransa ya bace yana iya korarsa shi daga inda zasu yi maganar da ita, Ama su suna iya Hanna shi wani baban abin, kuma ko ya kore su suna iya kin tafiya........., wannan maganar suke tattaunawa suna neman mafita, inda Abdul bassit yace Bama za'a bari ya san wanda ya mata aiki ba, za'a sanar masa mata suka yi mata, za'a yi karya dan a rufa mata asiri kuma a gyara aurensu, idan har suka sanar masa namiji ne ya ga matarsa da gani irin wannan sun san waye shi da kyankyamin abinda wani ma ya saka hannu a ciki bale har matarsa ta sunna........

Abdul Fatah na kai kawo dan tunanin mafita ne Anna ta karaso

Yannayinta ba dadi ta ce" Abdul , kun ga ku zo ku kama abokinku ku fitar min da shi a kicin, tunda ita matarsa bata jin magana ku ja abokinku , idan ya huce an zauna da shi, gayacen kicin, kuma na hana ta bin bayansa ta bi din "

Da sauri Abdul bassit ya dira ya fara yin hanyar da gudu,
Abdul Fatah ya bi bayansa yana yiwa Aliyu nuni da ya kama Anna, hakan ya sa Aliyu zuwa ya rike Anna da hannayensa bibiyu suka juya a hankali suka koma ta baya ta inda zasu fi gaggawar karasawa

Sai dai FARHANA du ta fi su isawa da gudun tsiya, hakan ya sa tana shiga Inna na wurgo marfin tukunya wurrrrrrrrrrrrrrrr, Allah ya da ta duke tana zarro ido kafin ta dubi su MAZNA da Nur ta matse jikin katon frij ta ki sakinta ya zama a yanzu ihu ma Mazna ke yi dan neman taimako

Inna ta sake dubansa ta ce" Ba zaka bani hanya ba ko?, ke Farhana kama min kar tsohuwar matar nan ta ilata min jika, ke Nur kama maman nan nata ki dasa mata cizo, yanzu iskar da aka hura masa ta sace, aikin banza duka gefe gefe ki toshe hancinki ki sace iskar duwawun ko ta baki lafiya, jikata zaki cewa karuwa????"

Yanzu kam Farhana ta gama gane cewar a lamarin nan Inna sam bata tsoron Allah

Karasawa ta yi ta shiga kokowar raba su tana kokarin fadin "Ke NUR, sake ta, Ke Mazna sakar mata hannu kin cije ta Bakya ganin jini na fita a hannunta???"

Abdul bassit kam da ya shigo sai ya damu kansa da zarro ido yana dakatawa ya dubi IMAD ya ce" Broth, ka raba su mana, ko sai na dauketa kuma in maka laifi?"

Har ga Allah sai a lokacin ya dubi Abdul bassit da sauri jin furucin bakinsa, har ma ya rasa to wace zai dauka a nan din da zai masa laifin?????

Karasawa yayi inda suka kuma hade da Farhana ya saka hannayensa harda yin Bismillah kamar zai taba aljannu ya damki hannun NUR ya cirata da karfin da sai dai ji ta yi an yi baya da ita, sannan ya shiga tsakaninsu yana duban kowacce, ya rasa bakin budewa bale har ya musu magana

Zuwan su JAUHARA da dan uwanta ya sa JAUHARA karasawa da sauri cike da mamakin abinda yake faruwa
Chapter 113 · 0% Book details