Sashe 107
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ficewa ta yi ta rufe mata dakin ta barta nan tsaye tana kallon hanyar da ta bi ta fita cike da tsoron kalaman da ta fada mata, bayan ta san tsagwaron gaskiya ce , kuma ita da kanta ta san cewar mijinta kwarai ya yi mata hakuri domin shi ba sanin takamaiman ciwon dake damunta yayi ba, shi dai abinda ya sani kawai ba zata iya hvng sex da shi a yanzu ba, kuma ta ki ya kaita waje likita da kansa, ama kuma yana ta binta yana mata uzuri......, to kuwa tabas ya zama wajibi ta yi gaggawar duba halin da take ciki.......
Idan AKOY abinda ke saka ta dana sani in ta duba yanayin jikinta ne, sai ta ringa kwana tana tashi da dana sani fiye da tunanin bawa.............., takan ji inama ace ana iya maida mata komai nata? Da ta je ta amso ta mayar a jikinta ta ci gaba da kula da mijinta yadda ya kamata, saboda idan har tana da ƙwaƙwalwa mai kyau ko da tsokana bai taba yi mata tsokanar yannayin halittar jikinta ba.
A yau din ma, likitanta dai ta yi ta kira, wanda a yau ya ki dagawa , domin shi kam abin ya ishe shi.
Kwarai abin ya kai masa inda yake jin an mugun takura masa, saboda aiki dai irin wannan ba yau ba ya fara, Ama da aka zo kanta komai ke neman wuce misali......., ta ki ta bi ka'idojin da ya dora mata, tana nan tana ta yawo bayan tun tafiyar da zata yi ta farko sai da ya sanar mata jikinta bai yi sauƙin da zata yi tafiya haka ba, sai tace ai ba nisa tafiyar, kuma ya jaddada mata komai banda wannan, ta je ta aikata wannan din, Gayanan ta dawo ya nuna mata zai riketa a wajensa kusan wata ko sama da haka sai ta je ta idasa warkewa a gida, nan ma ta kiya ta saka masa pression din da ya haɗa ta da antibiotique ya salameta, shi fa a gaskiya idan aikinta ya zo da gardama ba daga shi bane, gaskiya ba daga shi bane, yayi du yadda ya dace ya yi, itace ta ki bada hadin kai a komai ta yadda zata samu sauki yadda ya kamata........, shi bai gayyato ta ba, ita ta kawo kanta, aiki kuwa na jikin dan Adam na neman lafiya ma na kai mutun kabari bale na neman kyau, an ci Sa'a an yi komai lafiya lau ta ki bari ta samu sauki yadda ya dace, bashi da wata matsala da lamarinta sai tata, idan tana so ta dawo ta sake neman ganinsa ta hanyar da ta dace kawai su sake dogon bincike ta yi hakurin warkewa yadda ya dace kawai..........
Wannan rashin daga wayar ya kusan haukatata
Da ace ya daga, da ta ji shin yanzu dai tana iya ba mijinta kanta ko?, sai dai cikin ikon Allah ya ki dagawar hakan ya sa ta ringa sunturi da wayar a hannunta har zuciya ta kai mata makura ta buga wayar da jikin tiles ta duke jikin gadonta ta fashe da wani kukan cike da tashin hankali da tsoro, domin ita da kanta tana jin a yanzun ma bata shirya bashi kanta ba, dan ko yunkurin kukan nan da take yi tana ji har cikin ranta irin radadin dake tafe a jikinta.
.......................wannan kenan........
Mutalab kam ya cika dare yana fira da yan uwansa cike da zumudin jin zasu taso karfe uku na dare ne su da kanin mahaifinsu dan zuwa su nemi auren FARHANA, kuma zasu yiwa IMAD zuwan ba zata ne dan kuwa kwana biyu kenan bai basu time dinsa sun yi fira ba, nan ne ya shiga labarta musu abinda su suke gani a lamarin Imad, wanda ya sanar musu wanda ya faru yau wanda ALIYU ya sanar masa
Kwarai sun yi mamaki, kwarai lamarin ya basu mamaki mai girman gaske......, kuma sun cika da zumudin son isowa dan idannuwansu su gane musu abinda yake faruwa, Bama kamar Abdul bassit dake murmushi ya ce" Mutalab, kace fatan da nake in ga lokacin da zai yi soyayya mai suna soyayya abin a kusa ma? Kuma mai zafin da shi da kansa ya kasa ganewa?, good kace a gidan take yarinyar ko????, "
Mutalab na murmushi ya tabbatar masa
Abdul bassit ya ringa shafa kansa ya ce" Ka turo min sunanta da komai na whatsup, dan so nake yi in fara idasa haukata shi......, Ni idan na zo zan ce a bani ita, zan ga iya gudun ruwansa?"
Abdul Fatah ya zaro ido yana girgiza kai yace" lalalallaa, abada, ka ga kai fa matsalarka girma gare ta, kai kowace yarinya muka so sai ka nuna kaima kana so? Ka yi ramin kanka mana dan Allah ?"
Abdul bassit ya ce" Kai sai an so tan, ai ba zai yiwu a barku ku kadai ku yi yaki a gaban ya'yan mutane ba, dole a samu mai iya gwarawa da ku daidai da ajinku, dan ku san darajar matan, kwarai ya dage ko in dage, dan nima ina son in makale irin na Mutalab "
Kyale shi suka yi da halinsa, Ama kuma du wani kwatancen yadda nur take sai da Mutalab ya musu sannan suka yi Salama suna mai sanar masa nan da awa biyu jirgin su zai tashi, du inda karfe goma na safe ya kai zasu iya sauka dan haka su zo su dauke su ana kar su sanarwa IMAD
Shi ma yana murmushi yace " shi ma zai kai karfe goma kafin ya fito in sha Allah "
Daga haka suka yi Salama
Abdul Fatah ne ya yi kiran kampaninsu na gold a nutse yace" Du abinda ya sa a saka daya a saka masa biyu"
Abdul bassit yayi murmushi ya ce" To an baku ne da har zaka tanadi kyauta irin na wace aka baku? Ka bari mana mu je ta yiwu mu zaku ma kyautar ko?"
Abdul fatar ya girgiza kai ya mike ya ce" Bari in gano matata Ni, Allah ya shirye ka"
Murmushi yayi yana girgiza kai, shi kadai ya san irin jinin da zai haudawa IMAD, shi ba kullum idan aka yi maganar abinda ya shafi zuciya kallon shashanci yake musu ba?, ya yiwa kansa alkawarin sai ya sa yayi bayani da dukan yaran da yake da a bakinsa.
_______________________________
Kwana IMAD yayi bai samu barcin kirki ba,
Ciwon mara ya yi masa mugun tashin da bai taba tunanin zai kai haka karfi a tare da shi ba
Yayi du abinda ya dace ace yayi Ama abin ya gagara, domin ko sallar asubahi a dadafe ya samu yayi a dakinsa ya kuma kudundunewa a nan saman dardumar idannuwansa rintse, jikinsa tamkar rushi dan zafi, a yau ko leka su Anna bai yi ba kamar yadda ya saba, wanda hakan ya sa Anna din sai kallon kofar shigowa take yi, haka ma Inna da ta sauko yau da wuri saboda Nur na biye da ita ta taya ta kimtsawa ta kamata ta saukota kasa sannan ta koma ta shige dakin su FARHANA ta shige wanka abinta tana daga musu kai irin in sun hana mata kwonciya a karshen gadon nan ita a wanda ta kwana ita daya ta kwana abinta ga dadin barci kamar ba gobe.
Ganin karfe goma har da minti talatin ta gota ya sa MAZNA nufar dakinsa a darare dan ta tabbata kam ba fita ce yayi ba bata sani ba, fitowa ce ma bai yi ba daga dakinsa , bayan shi ba mutun ne mai zaunewa a daki irin haka ba...................
A darare ta kama kofar zata bude ta ji ana konkwasa kofar falo hadi da dana sonore din dake sheda mutun bako na son shigowa, domin idan wanda ba bako bane ya san yadda zai yi ya shigo kansa tsaye bangaren nasu
Dakatawa ta yi ta juyo tana son zuwa ta bude ta ga Jauhara ta fito tana tambayar baki ba zasu yi?
Kai ta girgiza ta ce" Ban san ko waye ba, plz bude ina zuwa....."
Daga haka ta kama kofar dakin nasa ta bude ta shiga da Salama a bakinta
Jauhara kuwa sai ta nufi inda ake ta neman agajin a bude ta bude dakin idannuwanta suka sauka a kan tsayayun larabawannda idannuwanta suka sauka a kansu ya sa ta saki baki tana musu kallon da kamar bata taɓa ganin irinsu ba, bayan a zuwan da suka yi ma ta gansu kuma ta san su.
Murmushi Abdul bassit yayi ya waiga inda Mutalab ke tsaye bayansu ya ce" Garin nan AKOY mata yaro, ita fa wannan?"
Mutalab ya dauke kai bai ce masa komai ba, Abdul Fatah kuwa bai yi mata kallon da ya wuce shara'a ba, domin bata da wani hijab a jikinta ya furta" Asalamu alaiki"
Kiris ya rage Jauhara rikicewa MAZNA ta fito a gigice tana fadin" Jauhara, Jauhara, ki min kiran Aliyu, yi min kiran Aliyu, Akul bashi da lafiya ne ashe , innalilahi wa Inna ilaihi raj'une......"
Da sauri JAUHARA ta juya tana dubanta, kafin ta juyo ta ratse gefensu da nufin yin nisa dan kiran Aliyu, sai ta ganshi a nan,
Kasancewar Aliyu zata yiwa magana a dole ta yi ta da turanci ta ce" Aliyu, kana ji ka je wai Yaya IMAD bashi da lafiya"
A tare suka Dube ta, hakan ya sa suka dubi juna a birkice kafin Abdul Fatah ya ce" Ki cewa matarsa ta bamu damar shiga plz"
Da sauri MAZNA ta nufo hanyar, dama shiga ta yi ɗakinta da gudu ta sako abaya da nikaf ta kuma dawowa, a rikice ta ce" Wai ina Aliyun?, su wanene a bakin kofar? , mtsss JAUHARA bari in zo ni in kirayeshi tunda ke komai baki iya yi da kaza kaza ba!"
Kasa hakura Abdul bassit yayi kawai ya tura kofar gaba daya , sai dai gannin shigar ta mai kyau ce sai ya zamo suna kokarin rigayar juna wajen nufar dakinsa kowane hankalinsa tashe
Abdul Fatah ne ya fara shiga , yayi Salama hadi da son ganin inda zai ganshi