Sashe 22
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maman yara ta tabe baki, duda bata so yin maganar a gaban auntyn yara ba, haka ta jure da kula ta ce" Baban yara, dama magana ce a kan y'ata, wato imteena"
Baban yara ya fuskance ta da kyau , hakama auntyn yara sai ta samu kanta da dubanta a tsanake
Maman yara ta ce" Dazu abin alkairi ya same Ni gidan nan, yaron nan yayan kawarta FA'IZA ne ya zo da mamansa cewar yana roko a bashi dama ya fara zuwa zance wajenta , shine nace ai dama kam an bashi, Ama idan ka zo zan sake sanar maka wannan gagarumin abin alkhairin da ya same mu"
A hankali auntyn yara ta sada kanta, baban yara kuwa ya zubawa maman yara ido cike da sake sake da mamakinta
Murya a daure ya ce" Wai, kina nufin imteen ce aka zo neman zance gidan nan, kuma aka zauna da ke harma kika bada damar eh kin amince?"
Maman yara ta Dube shi da yanayin bata gane ba
Baban yara ya ce" To ai Ni ba shashasha bane da zai zamo ina raye, ace ke ce zaki bada damar a zo zance wajen y'ata....., ke ko bana raye ai sai kaf dangina sun kare, sulaimana ya rasu sannan abin zai zo hannun ki, !"
Da bacin rai maman yara ta katse shi tana fadin" Malan ka fadi haka ne dan ba Ni na haifi IMTEE ba?, iyakata zaka nuna min a kan yarinyar da na kwashe yarintata na zubar a kanta?"
Malan ya dubeta da mamaki ya ce" Au, yau kuma a su nuna maki iyakar taki harda Ni kenan? To du abinda kike tunani haka din ne, ama ki sani ko A'isha ce ba zan taba lamunta ki shige min gaba a kan lamarin da ya shafi aurenta ba, gaba daya y'ayana sai na yi bincike a kan mahadin rayuwarsu kafin in lamunce, bayan wannan ma Ni ba zan yarda da wani zance na munafurci ba, meye ba'a haifarwa a tsugunne tsugunnen zancen?, idan lokacin aurenta ne ya yi ba wani zance da zata min da ya wuce zama uku na gaisuwa da fahimtar juna da amanan zama da juna, idan na kai ta dakinta sa yi zancen, kin dai ji abinda na fada maki!"
Daga haka ya mike ya kwashi takalmansa ya nufi zaure ya zamo daga maman yara sai auntyn yara
Auntyn yara ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina kai, to ita ai bata ga lokacin da wasu suka zo gidan nan ba, sai dai in a fitar Tata suka yi maganar a kofar gida, bayan wannan ma lalle maman yara da karfin hali take, shikenan dan tana mata kara har magana mai karfi irin wannan ta ratso da ta shafi Nur Ama ba zata sanar mata ba?, madallah da aka yi haka, yanzu kuma sai ta ga abinda zata yi......matar nan na matukar bata mamaki, tun da jan sawu ake kishin nan Gayanan yanzu du suna daf da yaye namijin a rayuwarsu dan tsufa ba ta nan yake ba, Ama ba zata daina abubuwan nan ba? ALLAH ya kyauta
Mikewa ta yi zata yi tafiyarta, maman yara ta ja tsaki kasa kasa ta ce" To ai ko wani abu kika yi dan ki hana abin nan baki isa ba, in sha Allahu Ni ce zan yi nasara a kan ki, ki jira ki gani!"
Auntyn yara ta dakata, ta juyo kasa kasa sosai ta ce" Maman yara kenan, ai tsakanina da ke ba jayayya, Allah na bari ya min komai!"
Daga haka ta yi shigewarta domin sai da maman yara ta zabura tana dafe kirji tana kallonta
Maman yara ta jima a nan kafin ta mike ta shige dakin itama ta yada mayafinta ta kwonta dan bata da lokacin nemawa kanta wani abin shinfida, da wahala ta iya rintsawa yau saboda malan na son bude mata wata kafa ta tashin hankali, wace ba zata taba lamunta ba.
Washe gari sai da ta bari A'isha ta shige wanka ta zauna kasa kasa ta ce" Kina ji imteena, abinda nake so da ke ki ringa yin zancen da yaron nan a Boye, ko a makarantar, ko a bayan layi ko kuma a gidan su har in shawo kan babanku, kin ga matar nan da nake fada maki kiyayarta a kanki mai girma ce kin ga aure ya nufo ki Ama so take yi shi din ma ta ture shi, dan jiya kiri kiri ta zage Ni ta uwa ta uba ta nuna min ba fa zan yi wani takama da ke ba, ke ba dan tsabar soyayyar da nake maki ba da ba zan taba iya kallon matar nan da ke ba, Ama ba komai Ni na san rabona na wajen Allah, du inda yace ku hadu ki je ku yi firar ku, ki sani yaron nan kwarai yana son ki, da ace baya son kare da ba zai taba baki dukiyarsa ba, maza yi wanka ki zo in baki yan kudin kashewa idan an fito da ku hutun cin abinci"
IMTEE cike da tausayin Mama ta mike itama ta kai ruwan wankan zuciyarta fal da tunani da tashin hankali, kai da ta shige wanka har kuka ta yi sosai na irin yadda zuciyarta ke damunta da maganar aunty, du idan ta ga aunty ta yi mata wani abin dake munin irin yadda ta tsaneta sai ta ji gaba daya duniyar na juya mata, komai ya mata zafi..... innalilahi wa Inna ilaihi raj'une.
MAZNA
Sai kusan karfe shida na safe na Nijar ta sauka a kasar Turkiyya, inda yake karfe tara nasu a irin wannan lokacin
Tana sauka asibiti ta wuce wajen likitanta dake yau yana aiki kuma ya san da zuwanta sai bata sha wahala ba bayan ta karasa ta samu ganinsa ta zauna tana jira layinta ya zo ta shiga
Wayar da kaninta ya zo mata da ita ne ta kunna da sabon layi ta shiga WHATSUP suka shiga magana da shi, inda take tabbatar masa ya ba kanwarta wayarta idan IMAD yayi kira ta sanar masa tana barcin gajiya ne na tafiyar da ta yi jidah to Niamey, sannan ta ce daga haka su kashe wayar in sha Allah ba zata jima ba zata juyo dan likitan kawai zata gani.
Mutun biyu kawai da ya gani sai ita ta shiga
Tana shiga suka gaisa da likitan sannan ta zauna a kujerar dake gabansa ya shiga yi mata tambayoyi kamar yadda aikinsa yake
Bayan tambayoyin mikewa ta yi ta tube zigidir sannan ta karasa saman doguwar kujera ta kwonta shi kuwa ya saka Safar hannu da zai dubata da shi sannan ya karasa ya shiga aunata da mafi munin awo, wato lungu da sako na jikinta sai da hannunsa ya kai, yatsarsa ta shiga, idannuwansa suka kala harta maman nata sai da ya luguiguita su sosai du a cikin awon ne da son gane idan komai ya yi dai-dai yanda ake so sannan ta mike ya shiga duba duwawun saboda kukan da ta kawo masa da bayanin da ta masa wanda yake son gane hanyar da zai bi dan ya gaggauta sama mata saukin da take bukata kafin mijinta ya zo
Da kula sosai bayan ya gama komai ya ce" Mrs IMAD, dole sai mun rike ki na kwana uku a asibitin nan ta yadda zamu yi maki duk abinda ya dace kafin mu sakeki, ki tafi Nijar, idan kin je sai mu jona da baki antibiotiques na karin ruwa har na sati biyu idan ya so sai a lalaba a idasa samun lafiya, da ace mun san girman jikin mijinki da mun auna irin risk din da kike iya shiga idan ya zo maki, ama tunda kin ki maganar nan fine, abinda zan fada maki shi ne kar ki yarda ya zo maki da karfi, du abinda zai yi ya yi a hankali kawai, dan kar ya kuma lalata mana aiki, kin fahimta?"
MAZNA ta amsa lokaci daya tana afkawa tunanin yadda za'a yi ta dauki kwana uku basu yi magana da shi ba, wace karya zata kirkiro wace zai iya kyaleta har kwana uku bai ji ta ba? Idan har tace bata da lafiya a nan ne ma zai iya yi mata kira biyu a wuni dan ya ji yaya sauƙin jikin ta, idan kuma aka bi shi da gajiya har kwana uku yaya hankalinsa zai dauka bayan tafiye tafiye ba yau suka fara ba, kuma ya san me take iya jurewa............
Da kyar ta iya samun idea, nan da nan ta danawa kanwarta kira ko karanta bata idasa sakawa ba ta kara a kunnenta tana jira ta daga.......
Tana dagawa bata tsaya sun wani gaisa Bama ta ce" Jauhara, kina ji, ki dauko jirgi ki taho nan , ki zo wayana, Ama kafin ki zo ina wannan mai kula da harkar communication din mu? Yaron chef din....."
Jauhara ta ce" Eh wannan da yace yana so na?"
Yayar Tata ta ce" Yauwa, plz ki same shi, ko me zaki iya masa ki yi dan ki yi convncre dinsa ya cire duk wata hanya da Akul ke iya gane a inda nake, saboda sai na yi kwana uku a nan kafin su iya bani damar tafiya............."
Jauhara ta yi wani dan tsai, dan ita ai wukalanci ta masa na kirki harda zagi tace ina ita ina shi......?
A yangance ta ce" Ni fa babu wani abu da zai shiga tsakanina da shi, dan kauye ne fa, kawai big bro ne da taimako ya bashi aikin nan fa har yake ganin shima ya zama wani shegen da zai iya dubana ya ce......"
"Kina ji, ba wannan na tambayeki ba, kin san waye IMAD!, kin kuma san me yake iya yi idan ya ji abinda na yi, ki rufawa kanki asiri ki taimaki kanki, kar ki rasa abinda kike takamar da shi JAUHARA IMAD! Kin ji abinda na fada maki? Ina jiran ki, zan tura maki dakin da aka bani ta msg!"
Daga haka ta katse kiranta da haushi haushi ta kalli likitan da nufin yin magana sai ta ga mamanta kawai yake kallo da wani kallo irin wanda ba zata so ace ya mata ba