Sashe 40
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashin yaya Anas yayi yana kallon baba, wato ANAS bai taba samun kansa a irin wannan tashin hankalin ba, tunda ALLAH ya halicce shi , shi bai san ya bi mace ba, bai san ya nunawa mace so ta ki shi ba, bai san Yaren da IMTEE ke koyar da shi a yanzu ba, shi yasa abin ya zo masa da mugun karfin da yake jin yana iya mutuwa shi idan bai samu IMTEE ba, kuma a halin da yake ciki yanzu ko ne aka ce zai iya yi saboda ya damu Imtee, ya riga ya gane kuma cewar idan har ba dama iyayenta suka bashi ba ba fa zata taba sauraronsa ba, dab haka gwara kawai ya bi hanyar da ta dace dan samun abinda yake so.
A tausashe Aban yara ya ce" Zan yi mata magana, in sha Allah jibi ka dawo ku zanta kai da ita , Allah ya tabbatar mana da alkhairin dake tare da ku, ya kade duk wani shari....., yaro a kula, a kiyaye hakkokin musulunci a kuma kiyaye amanar Allah ka ji? ALLAH ya muku albarka "
Wani irin dadi ya ringa ratsa yaya Anas, ya kara rage tsayinsa yana yiwa Aban yara godiya sannan ya juya ya shige motarsa ya tafi
Aban yara ma murmushi yayi ya shige cikin gida ya rufe ko'ina sannan ya karasa bangaren auntyn yara, dan yau a nan yake dan ya amshi abincinsa ...., a yanzu da SULaimana baya nan ma a cikinsu ya zamo suna tarda shi turaka ne, ko ace auntyn yara na zuwa, shi fa rabonsa da maman yara har ya manta, gama daya ta saukewa kanta rigimar nan bata gabanta, a zuciyarsa kuwa ya kudurce da safe idan Allah ya nuna mana zai sanar musu , su iyayen sai su sanar mata, idan ya so sai a bi komai a hankali a gani.
Yaya Anas da ya dawo gida ya tardo mahaifiyarsa bata kwonta ba, tana zaune tana kallon TV, dan bata iya kwonci idan bai shigo gidan ba, bale yau da ta ga shigarsa ta san in ya dawo alkhairai zata samu ba na wasan yaro ba sai kawai ta yi jiransa
Zaunawa yayi bayan ya cire rigar yana murmushi yana amsa sannu da zuwan da take masa kafin ta ce" A baka abinci ne????"
Kai ya girgiza yana doka murmushin nan ya ce" A koshe nake ai mama, ki tayani murna mahaifin Imtee yace ya bani dama in dawo jibi in zauna da IMTEE a gidan su, burinki ya kusa cika, na kusa yin aure mama....."
Daga haka ya mike yana murna ya nufi dakinsa
Da ido ta raka shi zuciyarta na cinkushewa
Subahanalah, dama shigar nan da yayi ta gidan matsiyatan cen ce? Yanzu dama du irin wulakancin da yake fada mata da bakinsa yarinyar nan na masa ta ki sauraronsa saboda laifin da ba shi ya yi mata ba, kuma a gabanta ya hukunta wace ta masan ama bai yi zuciya ya bar yarinyar nan ba?, wai dama yana nan a kan bakansa a kan lamarin da ya shafi yarinyar nan? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, to wai ita yaya za'a yi tana ji tana gani ta bar wannan abin ya faru da ita? Ta ina zata fara yarda da wannan abin?, yaya za'a yi ga yarinya nutsatsiya yar gidan masu mutunci tana son sa ya nacewa wace baya gabanta? Yarinyar nan idan ya aureta ba zata taba mutunta shi ba, ta yiwu ma sai ta raba shi da kowa saboda a bayane yake shi yake son ta ba ita take sonsa ba!, ai kuwa wallahi ba zata yarda ba, sai dai idan abin fin karfin ya yi, zata yi iya yinta dan ganin ta kwatowa kanta yanci, ba zata taba iya zuba ido abin nan ya cin mata ba!
Da wani takaici ta mike ta kashe tvn ta yi dakinsu ita da Fa'iza ta kwonta ranta na kuna, dan har cikin zuciyarta take ji cewar ba zata taba bari abin nan ya tabbata ba, yo hauka ake yi? Haka kawai?????? Mtsssss.
Washe gari da safe , bayan yara sun gaishe da iyayensu sun koma daki dan su tatare kamar yadda auntynsu ta dora musu dokar nan ne baban yara yayi kiran su maman yara da auntyn yara dakinsa na zaure
Bayan sun sake gaisawa da kowace ne ya Dube su da kula ya ce" Maman yara, bayan dogon nazari da kuma sake zuwa da yaron nan yayi mai neman yarinyar ki, a jiya mun zanta da shi kuma na bashi damar ya zo gobe su gana, shi ne nace zan sanar muku dan ki sanar mata , ai ke kika ce ta yarda cewa tana son sa ko???"
Daburcewa maman yara ta yi da farko, dan gaba daya tashin hankalin da ya kuno mata na sabon abin da take gani a idannuwanta a yanzu tsakanin yaran da auntynsu ya da har ta manta batun yaron nan, innalilahi mene??????
"Maman yara?" Aban yara ya fada yana sake dubanta da kula
Maman yara ta ce" Eh, ita tace tana son sa"
Baban yara yayi murmushi ya ce" To shiKenan, zan basu damar sabawa da juna na dan lokaci kafin in bashi damar Turi iyayensa, Ama kafin a kai cen sai na yi bincike sosai a kansa, dan Allah ku kula, ku yi mata nasiha sosai da sosai, ta kiyaye, kuma zance ita da shi kar a saki a wuce minti talatin, sannan a yi shi daga cikin gida ba kofar gida ba, ba kuma cikin motarsa ba kun fahimta???"
Auntyn yara kanta a kasa yake, haka kawai take jin kunya na lulubeta, ita kuwa maman yara so take ta yi ta fita daga dakin, dan kuwa Malan na cewa zaku iya tafiya ta mike fitttt ta fice daga dakin
Malan na kallon auntyn yara yadda ta mike kanta a kasa ta ki kallonsa ma, hakan ya sa ya ce" Rahama, lafiya kuwa????"
Auntyn yara ta ɗan daga, tana murmushi ta gyada kai kafin ta fice da sauri
Malan ya tafa hannu yana Binta da kallo ya ce" Allah sarki, au kunya ce??????, ikon Allah su ayntyn yara da sirikai......, to Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Maman yara kuwa dakin ta shige kawai ta zuba musu ido su biyun tana kallon su, har ta ga lokacin makaranta ya kusa dan haka ta ce" Ke A'isha je ki fara shiga wanka lokacin makaranta ya kusa "
A'isha ta kalli mahaifiyarta da dan mamakin ganin yau ita ke cewa su je islamiyya ?, farin ciki ta ji a ranta da godiyar Allah da tunanin ai dama komai na iya cenzawa a duniya, Allah ya sa mamanta ta cenza wasu halayarta mararsa dadi
Ciki ta shige ta dauki zanin wankanta ta daura ta ɗora hijabi ta wuce
Tana fita maman yara ta dubi Nur ta ce" Imteena zo nan"
Nur ta dubi maman yara, duba irin na jin dari dari, domin rabonta da ta ji ta kirayeta da imteenta har ta manta....., gaba daya yanzun babu wani shakuwa tsakaninta da mama, a dakin maman suke kwana, Ama sai su kwana su tashi ko gaisuwarsu maman bata amsawa......, ya zamo kamar maman haushin su take ji, sai ma idan sun kama aikace aikacen cikin gidan haka mama zata ringa bin su da harare kamar ta kashe su da idannuwanta
Zuwa ta yi ta duka dan nesa kadan da maman
Maman yara ta sake dubanta ta ce" IMTEE yanzu Bakya so na ko?, du wahalar da na sha a kanki, saboda ke Malan ya tsane Ni a gidan nan saboda ina kare ki, saboda ke mamanki ta tsane Ni saboda ina hanata neman dukan ki, Ama shine yanzu kika tsane Ni ko?"
Da sauri NUR ta girgiza kai ta ce" A'a mama, wallahi ban tsane ki ba, ba zan taba tsanarki ba mama"
Maman yara ta girgiza kai ta ce" Ni na san da Bakya so na, Ama Ni ba zan taba kin ki ba a duniya, haka kuma du abinda na san kina so zan dage har sai na ga kin same shi , yanzu haka yau na sake yiwa babanki maganar yaron nan, ANAS , yace kuma ya amince, ya yarda da soyayyar ku, du abinda zai faru ke da yaron a yanzu ba wata damuwa , mahaifinki ya yarda da alakar ku, ina fata kin ji dadin haka????"
Nur ta ɗan zarro ido, a hankali ta ce" Mama, kina nufin babanmu ya yarda yaya Anas ya ringa zuwa gidan nan......?"
Maman yara ta kirkiro murmushin dole ta ce" Yaya zai yi tunda na dage? Yace da Ni tabbas soyayyar da nake maki na bashi mamaki sosai, kuma ya yarda da Ni, haka kuma ya yarda da mai son aurenki dan haka daga yau du abinda kike so da Anas ki yi kanki tsaye kin ji?"
Murmushi NUR ta yi a hankali ta ce" Na gode Mama "
Maman yara ta ce" Tashi maza ki yi wanka, ki fesa turaran nan nawa, idan kun hadu ku yi zancen ku , ki tabbatar da kin masa kalaman soyayya, kin fa gani sarai yan mata na son sa, kar ki yarda wata ta kwace maki shi kin ji???"
Nur ta gyada kai, kafin ta mike ta shige ciki dan tara ruwan wankan itama
Da wata irin harara maman yara ta rakata da kallo, a ranta tana ayyana ' sai na ga bayan uwarki da ke kanki, yanzu haka ai basu san inda yayanki yayi na, saura ke, sai kin yi yawon duniya da kafafuwanki!'
Bayan sun shirya suka yiwa mahaifinsu Salama suka nufi makaranta, bakin Nur cike da magana, sai dai latin da suka yi ya da ta hadiye maganar ta har su tashi.
Bayan an fido su hutun cin abinci da sallah ta nufi office din Anna kanta tsaye, sai dai tana zuwa ta samu office din a rufe,
Waje ta samu ta zauna ta ciro litafinta na koyon larabci a hankali ta bude ta ringa bitar abinda suka yi da Anna har lokaci ya so shigewa......
A dole ta mike jiki ba karfi ta nufi wajen Masallaci dan ta yi sallah ta koma aji, domin ta gane cewar Anna ta yi nisan kiwo ne