Sashe 127
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ya sada yana hana kansa fitar da hawayen dake ta kokarin zubo masa, a tausashe ya ce" Auta, ai kin san dole wata rana zan maki aure ko? Kuma kin san dole a kai ki dakinki ko?, ki kwontar da hankalinki, ina nan, ko yaushe kike son ganina ki fada zan zo kin ji? , ki daina kukan hakanan ki tafi dakin ki, Allah ya muku albarka baki daya"
Kin sakin kafar tasa ta yi, sai da Mama ta kamata a hankali tana ta bata baki sannan ta bambareta daga kafar tasa, inda A'isha ke waje rukunkume da auntynsu tana nata kukan itama kamar zata mutu dan kuwa sai yanzu ta kara yarda wai aure fa aka musu, tafiya zasu yi, da kyar aka rabata da ita, ita din ma Mama ta shigar da ita motar, ya zamo auntynsu ta yi bangarensu da sauri tana fashewa da kuka irin na rabuwa da ya'yanta ce ke da jin ƙatuwar kewa hadi da binsu da addu'ar sabuwar rayuwa mai cike da kalubale kala kala, domin kuwa du abinda aka ce ibada tabbas yana tafe da abubuwan da zuciya zata motsa dole.
Mama ce ja gaban motar da amaren uku ke ciki, wace ALIYU ke ja........., wanda wasu motocin ke rakiya dauke da ma'aikatan tsaro da na gidan baki daya, ya zamo harda manyan samarin dake aiki ƙarƙashin kampanin ogan nasu, ya zamo ana ta daukan vidio masu ɗorawa na ɗorawa dan tabbatar da daurin auren sir IMAD wa masu karyatawa........hakan ya sa zamanin media ɗauka, har labari ya kai idannuwan tsohon saurayin FARHANA, wanda yake ciki fafutukar neman hanyar dawowa wajenta tun bayan barinta kofar gidan su, inda aurensa daya ya lalace dayan kuwa ake zama tamkar zaman yan bariki, domin a zaune da yake da matarsa shi ne mai yi mata biyayya, dan kuwa tunda zama yayi zama tsanar junna da rashin mutunta juna yayi karfi har rayuwar ta zama sai a hankali, ta fita lokacin da ta so, ta dawo lokacin da ta so, kamar yadda shi ma yake tasa rayuwar frreee tamkar ba mai aure ba, sai dai ya kasa komawa dan ya san ƴaƴanta na kasar, kuma layinta da ya sani ya gagara samun ta da kowace lamba, kamar an rufe layin ne gaba daya......sai gashi ya fada a page din da aka nuna fitowa da su da shigewa da su motar dake parker.....kuma ya ga zahirin sojan da zai ja motar ya gane ko waye, harma ya karanta caption a nan ya kara ganin cewar a auren harda FARHANA kuma da mijin da ta aura....wanda hakan ya saka shi kifa kai zuciyarsa na radadi, dan kuwa shi bai ma gane yana sonta ba sai yau................, wannan fushi da ya shiga ya da shi da matarsa kwana suna masifa kamar zasu kashe junna da kyar ya bar mata gidan cikin talatainin dare ya dauki hanyar club......dan kuwa kwarai a yau dole ya je ya kora abinda ke dauke masa kewa ke raba shi da fushi kamar yadda rayuwarsa take......!.
Get ne baba tun farkon shigowar anguwar gidajen........, sannan gidaje ne masu kama daya, a anguwar komai da komai
Gidaje ne da wani gawurtacen mai kudi ya fantsama, ya zamo idan ka kai kake siya, du yawanci irinsa ne suka sayi gidan domin bayan tsaruwa da kyau, an zuba abubuwan da sai ka kai zaka iya tayawa
Tsarin shiga City din ma da masu tsaro, har zuwa kowani get dauke yake da masu tsaronsa masu farar hula da masu kaki, iya abinda zaka iya ba kanka, iya abinda zaka samu
Aliyu ne ke fita, yana fara yiwa masu tsaron magana, sannan a shige a kai wace aka kawo gidanta, ya zamo shi kadai ke shigar da motar, mama kuwa ta kama wace aka zo nata ta fitar da ita bayan ta zare musu ido domin a nan ma so suka yi su daga mata hankali, sai dai ta ki Basu damar hakan ta yiwa kowace rakiya har dakinta hadi da kara yin rarashi mai daraja sannan ta kai Nur wace ita ce ta karshe a cikin WA'INDA ta kai, saboda nata gidan ne cen ciki
Ta jima a wajen NUR, tana rungume da ita..........., tana rarashinta hadi da sanar mata ko me take so da mutane a gidan zata iya yiwa wani magana kafin mijinta ya zo, sai dai irin yadda jikinta ke da dan dumi har yanzu ya sa ta zauna wajenta sai da ta sa ta yi wanka ta sake shan magani hadi da shan madara sannan ta lalabata ta kwonta, ta kuna mata karatu hadi da ajiye mai tsaron ta ɗan dole, domin ta san a yanzu angunan basu taho ba tukunan....ita kuma ko waya bata da shi bale ta ɗan dauke mata kewa, a haka dai ta silale ta barta cikin halin kadaici da rikicin zuciya...............
A gidan Anna kuwa, a hankali taron dake falon ma ya watse, ya rage daga Anna sai IMAD da ya dawo bayan ya bi bayan sauran sun je bangaren baƙi
A hankali ya karasa inda take zaune ya zauna daf da ita sosai kafin ya kamo hannayen ta ya rike yana duban fuskarta a tausashe ya ce" Anna, kamar ranki du a bace....., me yake damunki ne? Ko kin fi so a dawo da su ne? Idan haka kike so sai a dawo da su ba tare da Inna ta sani Bama, idan ya so lokacin da kika ji a ranki kin shirya sai su tare .......?"
A hankali Anna ta girgiza kanta tana rike da hannayensa a tausashe ta ce" Ina cikin farin ciki sosai, ina cikin farin ciki fiye da tunanin ka....., kuma kima ne, daraja ne ace sun tare a dakunan su a yau........., kawai ina tuna Nur ne, saboda har aka tafi da ita bata cikin nutsuwarta......., Andadi A'isha na son Sulaimane, ta san da maganarta da shi......., FARHANA ta amshi maganar Mutalab......, ama NUR....sam ba'a bata damar fahimtar komai ba, an dora Mata abu mai girma da daraja.....iyayenta kuwa sun nuna min kara da kawaici ko a jikinsu basu ja ta ba bale su sake fahimtar da ita abinda yake faruwa da ita..............., shi yasa na so ace an bara min ita koda na kwana biyu ne in zauna da ita sosai dan ta fahimci komai, ta Kuma aminta da komai......"
Fuskar Anna yake kallo, kafin yayi murmushi, a hankali ya ce" Haka ne, Anna kina so a dawo maki da ita ne?"
Anna ta Dube shi, kafin ta girgiza kai ta ce" AA, ina so ka rike ta ne da hannu biyu....., ina so ka yi mata uzuri a dukan abinda zaka gani a zamantakewar ku, ina so ka koya mata yadda kake son ganinta a hankali har ta gane, na tabbata yarinya ce mai biyayya, ba zata taba bijire mana ba.......ama dan Allah ka kara hakuri da ita ka ji?"
Kai ya gyada yana sake yin murmushi, a tausashe ya furta" In sha Allah, zan yi yadda kika ce Anna "
Anna ta yi murmushi tana duban fuskarsa , a hankali ta dan shafa gefen fuskarsa ta ce" Allah ya sanyawa aurenku albarka, Allah ya baku zaman lafiya, ubangiji ya baka ikon yin adalci a tsakanin matanka......."
Idannuwansa ya lumshe yana kai hannayenta wajen kirjinsa dake bugawa
A hankali Anna ta furta" Ka yi hakuri......, ka yi hakuri, ka yafe mata......, ka yi hakuri ka sake duban ta, ka yi hakuri ka sake bata dama......, ka yafe mata ko dan kannanta, na san abu ne da ya matukar girgizaka, na san an tabo darajar ka......, sai dai zan shiga alfarmarka na roka mata yafiyarka......."
Idannuwansa dake lumshe ya bude a hankali yana jan numfashi
Anna ta sake riƙe hannun nasa ta ce" Na sani, na san du abinda kake tunani,na san abinda kake ji, kuma na san zaka iya, zaka iya yafe mata, zaka iya mantawa......ka dauki lokacin da zaka ji zuciyarka ta saku, in sha Allah nan da sati daya idan na gama bincike a kan lafiyarta da komai Ni zan rakata ganin likita, za'a cire komai , zamu kiyaye du abinda aka dora ta a kai, zata yi jinya har ta warke.......ina so ka yafe mata ANDADI "
Ajiyar zuciya yake saukewa , a hankali ya ce" Anna yaya zan iya zama da ita?"
A tausashe Anna ta ce" zaka iya, aiki ta yi maka na mata, babu abinda Bama iya yi a cikin karancin tunaninmu, ta yi ne dan kawai ta burge ka, bata je ta aikata aikin da zai hana ka zaman da ita , kai ka san ba zata aikata wancen din ba....., kuma ka dan tana son ka....., ka yi mata uzuri, ka ture komai"
Ya jima yana duban fuskar Anna, kafin a tausashe ya ce" Na san kin san abinda nake iyawa, da wanda ba zan iya ba....., zan kamanta Ama idan ta daidaita kanta, Anna wannan karron ba zaki hana Ni sako ki a farkon hujar da zata iya sakani gazawa......idan har tana son zama da Ni sai ta gyara....ba rantse rantsenta nake so ba, a aikace zan gani......idan har ta san darajar ki......, sannan dukan abinda ta saka ta cire shi .....a nan ne zan iya duba yiwuwar zamana da ita"
Anna na kallonsa bata iya cewa komai ba,
Yayi murmushi ya ce" Su ne abinda nake so farko...."
Anna ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" In sha Allah zata gyara "
Kai ya gyada kafin ya duba time a tausashe ya ce" Mu je in raka ki"
Anna ta girgiza kai ta ce" A'a, ka yi tafiyarka sai mamanka ta dawo zan shige....., ba zaka yi mata Salama ba?"
Mikewa yayi, ya yi murmushi kafin ya ce" Allah ya tashe mu lafiya"
Daga haka ya juya ya fice ya nufi bangarensa na cikin gidan
Wani wankan yayi, ya shirya kansa cikin shiga mai kyau sannan ya saka turare na kirki a jikinsa da tufafinsa kafin ya duba sakon Aliyu ta WHATSUP da akwatunan da ya turo masa da hotunan turarukan da ya daukar masa da komai ya tabbatar masa suna cen gidan
Murmushi kawai yayi ya fito da ky din bangarensa