Sashe 133
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Likitar ce ta gama komai ta mike tana musu Salama saboda ta fadi nata sakon yanzu saura nasu, ta fita ba tare da ya kara dagowa ya dubeta Bama bale har ya gane ta tafi
Hankalin Nur ne ya fara alamun tashi
Lokaci daya babu irin tunanin da bai shiga kanta ba
Harta irin shekarun da ya dauka da matarsa da irin yadda baya maganar haihuwa da ita ma, duda basu wani jima ba tare, ama haka kawai ta samu zuciyarta da bugawa har ma ta kasa zaunawa ko dukawa ta zuba masa ido ........tunani take yi, to ko haihuwa ce baya so ya sa basu haihu da matarsa ba? ...............
Kwonkwasar da aka yi ya sa ta juya tana kallon kofar shigowar, kafin ta je ta bude hadi da bada hanya
MUTALAB din ne ya shigo da Salama hadi da dan dakatawa ya dubeta, sannan ya kai dubansa inda yake zaune
Kai ta sada, bata motsa ba har sai da ya karasa inda IMAD yake ya zauna yana kama sunansa hadi da kai hannunsa dan ya sauke nasa hannun ne ta juya ta nufi dakin ta da dan sauri hadi da zaunawa bakin gado cike da tsoron yanayinsa hadi da tunanin in kuwa haka ne bata ga mai rabata da cikinta ba, wallahi in haihuwa ce baya so ya da ransa ya bace da aka fada masa cewar ta samu juna biyu sai dai du abinda zai faru ya faru, Ama bata tunanin AKOY wanda zai rabata da cikin nan sai wanda ya bata shi!
Dago hannunsa da yayi ya saka shi Tsorata da gannin tarin hawaye a cikin idannuwansa, haka kuma fuskar tasa ta dauki jajajir
A tsorace MUTALAB ya ce" Subahanalah, me yake faruwa? Jikin na Nur ne? Me yake damunta ? Ko asibiti zamu je? Me Likitar tace? To ai ko me ta gani ba zata gane a nan ba sai mun je likita, bari in kirawo Nur din, ka tashi yaya ka tashi ........"
Firgigit yayi, ya shiga sauke numfashi da gaggawa hadi da riko hannun MUTALAB dake son mikewa ya je dakin Nur
Falon ya bi da kallo, kafin ya ce" Ina Nur?" Ina HALLAH?"
MUTALAB ya Dube shi, sai kuma ya juya ya nuna masa inda ya ga ta shiga, wato dakinta
Mikewa yayi da sauri ya fara nufar dakin, sai kuma ya juyo da sauri ya kama hannun MUTALAB ya jimke hadi da lumshe idannuwansa muryarsa na harhadewa ya ce" Ashe zan haihu ?, ashe zan samu baby?.......Nur ciki....ciki......" Sai kuma ya sake shi murmushi na mamaye fuskarsa ya duka ya kai sujada kansa a kasa ya dago a yanzu hawayen ya shiga bin gefen fuskarsa kafin ya mike da sauri ya nufi dakin
MUTALAB kam tuni ya ringa dirka rawa cike da farin ciki yana zagaye kafin ya fita da gudu ya nufi nasa gidan , yana ciro wayarsa ya fara kiran Anna, wace tana dagawa bai tsaya wata wata ba ya sanar mata labarin hadi da sanar mata haka likita tace, sannan ya kashe bai wani tsaya ba ya shiga lalubar numbobin yan uwansa yana fada musu labarin da ya sa suka ringa Kabara , har ya karasa bangarensa ya samu Farhana na cikin mopping, domin kuwa du yadda masu aiki zasu musu basa yarda su taba musu dakunansu da na mazansu........., yana zuwa ya sureta yana dariya ya ce" Albishirin ki"
FARHANA na zarro ido ta rike shi da karfi dan kar ya sakota ta ce" Goro"
A kunnenta ya rada mata, wanda hakan ya sa ta daka tsalle hadi da saka ihu ta rukunkume shi, sai kuma ta sake shi da gudu ta nufi wajen kayanta ta warto katon hijab ta juyo tana ihun ta ce" Wayo Allahna, alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah ashe zan zama momy?????? Wayo dadi"
Rikota yayi yana dubanta ya ce" Ke ina zaki je to?"
Hanya ta nuna masa ta ce" Zuwa zan yi in rungume Nur, zuwa zan yi mu yi farin ciki"
Rikota yayi ya rungume a jikinsa yana girgiza kai ya ce" Ba lalle ki sameta ba yanzu gaskiya, saboda shi ogan ya shige dakin , kuma ga dukan alamu aiki ya fi Ni yi, zo mu kara gwada Sa'a ta yiwu kema ki bani ladan aikina ko?"
Dariya ta yi tana boye fuskarta saboda lamarin MUTALAB kam sai addu'a, sam baya daga kafa, idan safiya ta yi fa Tsayuwa IMAD ke yi a kofar gidansu yace ya bashi second goma, shi da SULaimana wanda yake nan cikin haɗa haɗar bude nasa kanfanin wanda Imad ya bashi damar zaban abinda yake ganin zai gyara shi na kasuwanci wanda yake ganin ya fi ganewa, shine yace yana da jari sosai, yana so ya fara harkar cenji sosai da sosai, sai harkar kayan abinci, wanda hakan ya dadada ran IMAD din, domin yana yaba kokarin Sulaimana da jajircewarsa, har ma ya sa aka sake saka baki kafin ya amince a fara girka nasa harkar neman bisa yarjejeniyar sai idan za'a ringa amsar zubinsa du wata har ya zuba abinda aka zuba masa, domin sam sulaimana baya son abinda za'a bashi kyauta, sai da Anna tace ba damuwa an yarda da hakan sannan ya saki jiki sosai ya maida hankali................, ya zamo daukansu suke yi, kowane su ajiye shi a wajen nasa neman kafin shi ma ya karasa wajen nasa neman, matansu kuwa dama idan yau sun hadu sun wuni a wannan gidan , gobe sai su hade a wani.......zumuncinsu na nan, duda Nur bata cika lafiya ba , haka suke haduwa basa barinta zama ita kadai a gidan.
Tunda ya shige dakin ya rufe kofar ya karasa inda take zaune hawaye ya wanke mata fuska ya zauna gefen gadon yana janyota jikinsa gaba dayanta ya ce" khalb....., kuka kuma? Menene? Ko cikin ke ciwo? Mu je asibiti ne?"
Nur ta Dube shi, jikinta du a mace ta ce" Baka so ko? Baka son haihuwa ko?"
Ido ya zarro, kafin ya riketa a jikinsa da dan karfi ya ce" Haihuwar?, Nur, ina don haihuwa, na nemi haihuwa, na yi ta addu'ar samun haihuwa, har na dangana na yi ta addu'a Allah ya saka min dangana da yawan damuwa a kai........, yaya za'a yi ki ce bannnnn........au, wai dan kin ga na kasa motsawa?????"
Nur ta gyada kai zuciyarta na daukan sanyi
A hankali ya rungumota jikinsa yana murmushi hadi da saka hannunsa wajen cikin ta, a hankali ya ce" Ina farin ciki, ina farin ciki sosai, farin cikin ne ma ya sa na kasa motsawa.............., Hallah cikina ne a nan, cikina ne....Ya Allah......"
A hankali ya ringa kokarin tabbata....., sai dai ringin din wayarsa ya saka shi dakatawa idannuwa tuni sun cenza kala...........
Sai yanzu ta tuna Tata wayar ma ita, gaba daya bata wani damu da waya ba, in ba zata yi kiran abanta ba shi da auntynsu fa sam bata taɓa wayar, tana kiransu kullum da safe ne, haka kuma ta yi kiran Anna da Mama du su gaisa, da dare kuwa Anna ke kiranta su sake gaisawa Shikenan idan ta yar da wayar bata kuma bi ta kai, waya fantsamemiya ama bata wani damu da ita ba....
A hankali ya mika hannunsa da ita a saman kirjinsa ya dauko wayar ya daga, domin daga yannayin kiran ya gane ko wacece
A tausashe yayi Salama, sannan ya furta" Anna"
Anna ta lumshe udannuwanta, tana murmushi a tausashe ta ce" Ina take?"
Murmushi yayi, ya dubi Nur da ta yi pilat a saman kirjinsa, kafin ya mika mata wayar wajen kunnenta kasa kasa ya ce" Anna ce"
So ta yi ta mike daga jikin nasa, ya kiya, a dole ta kara wayar a kunnenta ta yi Salama
Anna ta yi murmushi ta ce" Yaya jikin ki?, me da me kike ji?"
Nur ta zubawa fuskarsa ido, sai kuma ta sune kai cike da jin kunya da tunanin ko dai ta ji???
A tausashe ta ce" Da sauki Anna, bana jin komai"
Anna ta ce" To, Allah ya kara lafiya, ga mamanku"
Amsa mama ta yi muryarta da abin kukan har yanzu bai bari ba ta kara a kunnenta ta ce" Yata?, yaya kike?"
Jin abin kukan ya saka shi bude idannuwansa yana kallon Nur, wace ita ma ta ji hankalinta ya tashi ta ce" Mama mura kike yi? Muryarki kamar kin yi kuka"
Mama ta shiga share hawaye cike da farin ciki ta ce" ya Allah, kukan farin ciki nake yi yarinyata, ina yake? Ina andadin? Dan Allah ya kawo mana ke kusa da mu, ya dawo mana da ke nan, ko kuma Ni a zo a daukeni, domin bana jin kuma zan iya zaunawa a nan, Allah ya Allah ya buda ido lafiya........ Allah ya sauke ki lafiya......"
Ido nur ta zaro kafin ta mika masa wayar ta mike da gudu ta yi bayi, wanda hakan ya saka shi mikewa a hankali ya ce" A'a, a'a fa banda gudu, NUR........."
Sai kuma ya yi dariya yana kai wayar kunnensa yana jiyo lokacin da Anna ta ce" Kar ta yi gudu ta rufa asiri" sai kuma ya jiyo mama na dariya itama tana fadin" Anna kai kai kai, me kika ce?"
Anna ta mike ta yi gaba tana dariya ta ce" Bari in kimtsa in je asibiti, likitan da ta mata aiki yau zata dawo, zuwa an jima na san zata sauka, Allah ya sa ta bamu Salama mu dawo gida baiwar Allan nan ta gaji da zaman asibitin nan, Dan ma ta koyi hakuri yanzun, da da ne Bama zata iya ba ai"
Mama ta gyada kai tana fadin" hello Andadi "
Murmushi yayi ya zauna yana duban hannunsa a tausashe ya ce" Mama, Ni ma ina so ta dawo nan, ina tsoron kar Anna tace ba haka ba, kin ga ina ganin nan da sati za'a gama komai na gidan su Baba, idan suka koma nan din sai in sake mata yanayin ginin sai in dawo da ita nan ko?, plz mama ki saka baki Anna ta bar maganar raba mana gida plz"