Sashe 62
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fada baban yara na masa alamun yayi a hankali domin sun karaso, Sulaima kamar zai bige ANAS, suka karaso da ƙatuwar akwati, jijikekiya ce , ga iyayen ledoji bakake manya shake da kayan, kansa a kasa ya ce" yauwa Aba, na akwatin nata ne, na ledojin kuwa na yar uwarta ne da mama....zan wuce, na gode Allah ya kara lafiya"
Malan na murmushi yana gyada kai yana furta" Amen amen yaro amen, a gaishe da gida"
Daga haka ANAS ya koma cike da farin cikin amsar kayan nan da aka yi, shi kam ai ya godewa Allah da ya samu alwalinta, tabatuwar an gama sanin sa .......idan ya kawo mamansa kawai ta sanar da maganar za'a turo shiKenan zance ya kare.
Ƙatuwar fitilar dake hannun Malan wace a zuwansu ya siye ta saboda abinda yake son yi a cikin gidan nan ya kara kunawa ya ga irin yadda ta haske kofar gidan kafin ya kashe ya dubi Aban yara da yayi tsuru tsuru jikinsa a mace murus ya ce" Kai sule, dauki kayan nan mika min dakin ka, sai na gama da matan gidan nan an mika musu......."
Sai da SULaimana ya shiga mika kayan sannan Malan ya dubi Aban yara ya ce" Hakuri zaka yi, ba zan taba iya kawar da kaina ba fa, hakuri zaka yi, wata biyu ba kwana uku a kan yaron nan nake, duk wani abu da nake son sani na sani, ka ga wannan yaron? Naka ne gaba da baya, yanzun abinda zan gani cikin biyun dake ciki wadda ba taka ba, dan Ni ba shashasha bane, na rantse maka Allah ba zai bari sulaimana ya so jininsa ba, me ka ratse? Auren uwarsa ne baka yi ba ko na uwar gidan ka?, idan har bawa na tsare iyakokin Allah, yana yiwa Ubangiji biyayya , Allah ba zai jarabce shi da mugun abin tashin hankali irin wannan ba.........., baka taba zina ba, baka taba shirka ba, a iliminka na san ka kiyaye fadawa gonar ka ba da addu'ar saduwa da iyali ba......, kana sallah kana azumi kana sadaka gwargwadon karfin ka, kai kuwa du jarabawa nan tsaftatatu irin su shaye shaye da yaron nan ya taba su ne kai zai dauka mana ko? Ama yaya kake son ka ce min iya shege ne irin na sulaimana da yanzu ya sake tabbatar mana eh shi yana son A'isha? Yanzu fa ya fada har ka gwaru da kofar nan dan jiri ko?, ka ga ai ba a maye yake ba, ko daga suturar jikinsa kuma kai ka san an samu ci gaba ko? To ka ji da kyau sulaimana shanuwa na siyar na saka masa kudi a hannu , yanzu haka a Magarya sunansa mai saukar baki domin du wani dan motar Kano Kano ta hannunsa yake bi, ina tsaye a kansa ina biye da shi hakama yayansu na cen a kansa ba dare ba rana, idan suka fita nema ina biye da su, ina musu dirar mikiya, a cen din ina kai masa du wani taimakon da zai sa ko sigari aka busa a inda yake zai gudu, ina kafa kafa da shi , duk wani abin alkairi da ka sani Sulaimana ya nuna min, azumi yake yi kullum ta Allah sai na jajirce yake ajiyewar, tunda muka yi dogon Zama nace da shi sulaimana idan fa rashin jin ka ne ya sa Allah ya jarabeka da y'ar uwarka ai ka shiga uku, sai ya Tsorata fiye da kima......., to dai zuwa muka yi mu tabbatar da lamarin nan, Ni kuwa a yau sai na gane abinda yake faruwa a gidan nan, wuce mu je!"
Malan ya sauke ajiyar zuciya....., yau yau fa ya iya cire damuwar nan har ya samu lokaci mai daraja da maman Sulaimana, yau yau yake jin kansa kamar sabon zakara dan karfi da samun cikakken bukata mai sanyaya zuciya....., har wani karya hula yayi da zai koma kanti dazu yana jin kamar wani dan shekara arba'in a duniya.....ashe mutumen nan na tafe???????
A dole ya fara yin gaba, ya yi Salama saboda ya san su duka sunna filin gida a irin wannan lokacin, dan ma maman yara na kofar dakin ta ne ita kadai saman tabarma tana yamutsa zogalen da ta shigo da shi daga anguwar da ta je , su kuwa sunna saman Babar ledar da auntynsu ke shinfidawa sunna zaune gaba dayan su, aunty na tsefewa A'isha kai, ita kuwa nur tana bitar karatun da aka yiwa su A'isha bata nan yau , aishan na koya mata saboda kar aje ta kasa bada wata hardar ga kuma laifin kin shiga aji Malan ya yi mata fila fila suka jiyo Salamar Malan na Magarya da kuma Muryar Sulaimana
Kusan a tare du suka dago, ciki harda maman yara da Muryar Sulaimana ta kayar mata da gaba da mugun karfin tsiya
Nur na farin cikin jin Muryar baba na Magarya ta dauko kujerar tayani tsuguno ta ajiye , A'isha ma ta daure kanta ta nufi Randa dan ta zubo masa ruwa , auntyn yara kuwa ta gyara abin shinfidar sai marabatarsu take fuskarta dauke da matsanancin farin cikin jin Muryar sulaimana, Ama kuma bata wani nuna ba ko kadan
Hannu Malan ya sa ya janyo Sulaimana kiiiiiiiiiiiii yana fadin" Ina uwar gidan gidan nan ne? Ban ji muryarta ba, Ni anya zan iya hakura har mu gaisa kuwa? A gigice nake, da tashin barakar da ta wurgo Ni nan ba shiri, bisa baban abin da ya haddasa min tashin hankali a kan Sulaimana!"
Sai yanzu maman yara ta mike ta karaso tana murmushi ta ce" To fa, Malan ina sanu da zuwa , jiyo ni ne baka yi ba , shin me ya faru da sulaimanan? Mu fa nan rabonmu da shi an kusa wata uku cifffff, Ni ai na zata ma mutuwa yayi aka boye min, kar dai garin yawon nasa da neman BALAKI ya nemo har aka neme ka da shi? kar dai aje wata jarabar ya janyo maka????"
Fitilar nan Malan ya kuna ta haske uban kowa a filin gidan, da hasken nan mai sakawa ka dan duba kafafuwanka kar aje kama da wanda ka yi burgima a kasa suke......., ai kuwa yana haskewar ya ce" Hum, ke ai da ace wannan ne da da sauki, burbushin balakin da ya nufo Ni ba karami bane ai, wanda ya sa dole ya sa na nufo dan in ji inda aka haihu a ragaya, domin kuwa ba ta yadda za'a yi dan halal dan jini daya a ji lamari irin wannan, ke wai SULaimana ke son a'in gidan nan, soyayya ta Aure, to kuwa ai dole ku sanar min cikin A'I da SULAIMANA wanene ba D'AN AHMADU ba!"
Ina irin tashin hankalin nan da idan ka ji cikin ka ke yin wani irin murdawar da amon kararsa zai sa kowa ya ji ka din nan? Wannan tashin hankalin dake sakawa zaninka kuncewa....., tashin hankalin nan dake saka ka sakin ihu baka shirya ba? Irin tashin hankalin nan dake kunce maka gudawa........, shi ya ziyarci Maman yara a haukace ta bare a kasa saboda kaffafuwanta da suka ko daukan ta lokaci daya tana dafe da kirji da karfin amon Muryar da ta dara ta auntyn yara wace itama a gigice ta dafe nata kirjin da karfi ta sauke dubanta a kan Sulaimana da ya sunkuyar da kai kamar an kama kwarto......, lokaci daya IMTEE ta matso tana dora hannayanta saman kaffafuwanta ta yi irin dukawar nan ta neman karin bayani zuciyarta cike da yarda cewar kwaya ta haukata gayen nan, da kuma A'isha wace ita ta fi ba Aban yara tausayi saboda irin firgicin da ta yi ta juyo tana kallon Malan na Magarya......., lokaci daya amon Muryar maman yara ta doke ta kowa da karfi ta ce"Kisan mummuke 37
A mugun firgice Maman yara ta ce" Wani irin A'isha ba y'arsa bace? Wani irin yana son A'isha?, to ai wannan yaron dama Ni na san shaye shayensa sai ya kai shi ga aikata mugun sabon da kowa sai ya shiga uku, da sauki ma da ba uwar yace yana so ba ai da....."
"Lahaula wala kuwata Ila bilah, maman yara fal yakul khairan au liyas mut......., ki daina munanan kalamai irin wadinan, kar ki saka dan sauran burbushin girman naki da nake gani in saka kafa in take in murje da kaffafuwana....., yara ai gasunan, Ni dai na san ban san wata hanya bayan ta wanda ya ajiyeni a gidan nan ba, idan kuma shi din yana da tantama da haka bani da ja, sai a je du inda za'a bashi haske a kan ya'yan nan a yi masa du irin gwajin da yake so a kan ya'yan nan......, ba zan ja da kowa ba , ba kuma zan ji haushin kowa ba, domin ko Ni ban san abinda ake ciki ba da tuni na samo masa sheda ta kirki da zai daina wannan firgicin, domin kwarai akoy firgici ace d'anka na cikin ka yace yana son y'ar uwarsa.....kwarai sulaimana ka kai Ni wajen da hankalina ba zai kuma sauka da sauke fushina a kanka ba, ka gani ko? Abinda nake hana ka ko?, to Ama Malan Ni na bada dama du inda za'a je a je, ya'yan nan na Malan ne, bani da Dar!" Auntyn yara ta ajiye maganar ta a nutse tana dauke kanta hadi da share kwalar da ta tarun mata a cikin idannuwanta cike da jin tarin tashin hankalin dake nanukarta a zuciya......
Oh dama shi yasa Malan ya dauke shi daga gidan ba tare da kowa ya san inda suka nufa ba?
Shi yasa Malan ya je ya ajiye shi a cen ya dawo ?
Sulaimana rashin jin nasa har cen ya kai?
To ai dama Malan na Magarya bai dawo da shi ba, da ya barshi a cen da sai ya fi mutunci a cen......
Aban yara ya daga kafa zai karasa dan ya musu magana, Malan na Magarya ya saka hannunsa ya mayar da shi baya sannan ya masa alamun ya yi shiru