← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 141

Sashe 72

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FU'AD da ta bashi haushi tun a maganar da ta yi kan FARHANA ne ya ce" Ke ki kama mana bakinki , ke dama zuciya ne da ke a kirjinki? Ke har kin san darajar so? Ke fa du wanda ya aure ki ya shiga uku dan wallahi ba zaki zauna da shi idan bashi da kudi ko sunna a duniya ba, yana talaucewa zaki yi tafiyarki....., ki bar mu, mu da muka san darajar so mu yi abinmu kuma mu kare abinda muke so!"

Baki Jauhara ta tabe ta ci gaba da kallonsu tana karkada kafa, sai dai ta san yayarta na cikin mummunan hali, da ya zamo har sun fada mata maganganu n irin wannan ama bata tanka su ba....., kwarai ta rasa yaya zata yi da zuciyarta ne, bayan ita a bayane take ganin mafitarta Ama ita ta ki ta dauka........., Allah ya rufa mata asiri kar abinda ta fi karfi ya dawo ya fi karfinta.

A falon kasa kuwa su duka da ido suka raka yaran nan, kafin da mamaki auntyn yara ta sada dubanta cike da jin kunyar irin yadda yaran sam basu tsaya sun ba matar nan mahimmanci ba, irin yadda A'isha sam ta ki yarda ta je wajen koda mahaifin nata ne bale mahaifiyar nata, irin yadda Nur ke kutsawa cikin gidan nan tamkar wace ta saba zuwa ko wace take da wata mu'amala da ahalin gidan.......

Kwarai ko a haka a barta an gama gigita mata tarbiyyar ya'ya, Bama kamar NUR

Nur bata tsoron uban kowa a duniyar nan, haka kuma bata shayin yin magana a gaban kowa
Abinda zai sa wani ya ji kunya ko tashin hankali NUR ba zata ji shi ba sai dai ta dauki abin matsayin lafiya lau ne ko ma ta nuna ita ke da gaskiya
Sam ba'a bari Nur ta bambance dai-dai da akasinsa ba, a rayuwa tafiya take gaba gadi ba wani abu dake risinar da ita................., A'isha kuwa dama fa, kamar wace mamansu ke bata tsoro, ki ace tana matukar kiyaye duk wani abin da zai hadata da mamansu mai tsayin gaske........., ko a lokacin da mamansu zata saka kuka idan ta ji motsin Malan in ka bi fuskar A'isha da kallo zaka karanci mamaki ne shinfide a fuskarta tana bin maman nata da kallo, domin wasu lokutan idan ta shigo ta tarar da maman nasu bata nan har ya zamo auntynsu ce kawai ta basu abinci in Nur ta ki ci, takan yi murmushi ta dubi auntyn nasu tace ina mamakin wasu abubuwa a gidan nan......., ina mamakin irin yadda mama ke tsoronki idan abanmu yana nan, idan baya nan kuwa kamar zata iya dukan ki ..........ina mamakin yadda mama ke cewa Imtee zaki iya kashe ta, bayan ko kwari bamu ga kin kashe a gidan nan ba........, sai dai ta yi murmushi kawai ta bi A'ishan da kallo.......sam ba wata babbar shakuwa tsakanin ta da mamansu, ko kwanakin nan da maman nasu ke koro nur ta nuna ai itama ta haifa ga A'isha nan ba ubanda ya isa ya lalata mata zuciya saboda haihuwa......., sam A'ishan bata iya koda minti goma a dakin nata zata sadade ta gudu, ko ka ji ta kwashi zage zage tana fadin dan ubanta gaba gaba ana iya hada baki da ita a wulakantata.............
Ita kadai ta san irin cutarwar da maman yara ta dauki lokaci tana yi mata ta hanyar Nur wanda idan baki yace zai fada zuciya ba lalle ne ta iya dauka ba.....

Ta tabbata sai dai ta iya taro wani abin a lamarin nur, ama da wahala ta iya taro komai da komai......

A hankali ta ce " Dan Allah ku yi hakuri, ban san me yake damun yaran nan ba, maimakun su zo su zauna a fuskanci wannan baiwar Allahn, sun tafi sun bamu waje....., zan yi magana da su in sha Allah zasu nutsu......"

Anna ta yi murmushi , ta kai dubanta kan IMAD dake kallon Mama a tsanake wace tunda A'isha ta mike ta yi elevator da su Nur ta sada kanta kasa gumi take ta ko'ina ama bata daga kan nata ba, bata ce komai ba........

Mikewa ya yi ya nufi hanyar kicin ya shige ya dafe abin kicin ya sada kansa hadi da lumshe idannuwansa
..................................

Sanin cewar ba abinda ke iya kai shi kicin ya sa Anna duban Mama dake zaune , irin zaman da ta yi ita da kanta yana cikin zuciyarta, domin tunda ta mayar da kanta ta sada bata daga ba, ita addu'ar da take ta yi a cikin zuciyarta shine Allah ubangiji ya sa sanadiyar samun lafiyarta Kenan......., dan haka ta mike a tausashe ta ce da auntyn yara" Auntyn yara, Bara in kawo maki wani abin kafin yaran su sauko ina zuwa"

Aunty ta yi murmushi bata iya cewa komai ba, saboda tunanin dake kanta ya fi karfin magana a yanzu, hankalinta du a kan wannan baiwar Allan, bata san ta yadda zata iya taimaka mata ba, hakan ya sa kawai take ta sake sake..........

A hankali ta ɗora hannunta saman kafadarsa daga baya a tausashe ta ce" Andadi, na zata yau ranar farin ciki ce mai girma a wajen ka, saboda muna zaune har gida alkhairin sanin inda yarinyar maman ka ya same mu har cikin gida, an ganka cikin koshin lafiya, ciki ahali masu son ta, da mahaifi mai son ta, na zata a yanzu kam cikin farin ciki kake sosai......me yake faruwa ne wai hankalinka du a tashe"

Idannuwansa dake rintse ya bude ya juyo yana duban Anna

A hankali ya dan dantse hakoransa ya sake budewa yana duban Anna a tausashe ya ce" Anna......, aka ganta a yaya? An ganta ama sam ba yadda na so ganinta ba, kina gani ba ta sanin su waye iyayenta take ba, ba ta zuwa inda mama take ba, ta fi son matar nan fiye da mama , .......hum koda yake ya dace hakan kar ya bani mamaki saboda wace take kawa a wajen ta Yar uwarta ai bata da hankali.....Anna Fisabililahi ki rasa wa zaki yi haihuwa da ita a duniya dai yarinyar nan? Ki duba ki ga irin abinda take yi a cikin mutane , ki kalli irin yadda suke hayaniya.......da Farhana ko? FARHANA ko? Ya Allah......"

Anna na dubansa da yanayin abin tausayi ta ce" Aya, Andadi ba zaka gane wace Nur ba sai ka zauna da ita, ba fa mahaukaciya bace, da hankalinta, yarinyar nan ta shiga hannun wace ke son tozarta mahaifiyarta ne ya sa ka ga du wasu abubuwanta sai a hankali, ama ka ga yarinyar nan ko? Tana da hankalinta ga ilimi ga shiga zuciya, Ni wallahi jinta nake yi har cikin raina dan Allah kar ka ji haushinta, bata iya Tsorata bane, du a firgice take, ka auna fa ka gani irin yadda mamanka ke riritaka a wayi gari a kamata da ire Iren laifukan nan, kuma ma a riinga kokarin nuna maka zama da ta yi da kai ba dan Allah bane, yaya zaka ji?????"

Yana duban fuskar Anna, a tausashe ya ce" Zan ji babu dadi, Ama zan fi shiga halin nutsuwa dan in fahimci abinda yake faruwa da Ni, idan na san ainahin abinda yake faruwa da Ni zan fi samun solution din da ta dace da Ni.......ba wai in riinga neman zubar da kayan jikina ba.....Anna da na rike maki ita dan ki biyo bayana in raka ku dakin ki ko kwa samu natsuwa ke da mama me yasa baki bi Ni ba?"

Anna ta ce" Na mike dan in bi ka, sai da na mike dan in bi ka, a lokacin ne kuma muka sake zaunar da yayansu saboda mu rarashe shi shima ga kuma A'isha da ta ki yarda ta dubi Malan har baban nata ransa ya ɓaci sannan ta je inda Malan yake....., Son du abubuwan ne a hargitse yau, shi yasa ka ga haka......."

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce" To dai yarinyar taki mai hankali, kawai dan ta ganta a corridor ta ji tsoron da ya sa ta..........ta................ta.............."

Sai kawai ya kasa karasawa bayan abinda ya fi ci masa tuwo a kwarya kenan, gaba daya sai ya sada dubansa yana dan murza hannun Anna wace ke jiran jin ta yi me?????????????????, sai alamun hadiyar yawun wahala da yake yi wanda ya tabbatar mata da wahala ya karasa maganar tasa

A hankali ta budi baki ta ce" Ta yi me Andadi????"

Idannuwansa ya dago ya zuba a fuskar Anna

A hankali ya budi baki zai yi magana Muryar auntyn yara da karfi tana fadin" Subahanalah, dan Allah ku taimake Ni, ba kowa ne? Anna ? ANNA ????"

Da sauri ya yi waje, haka ma Anna da sauri ta bi bayansa har kamar zata kifa

Sunna fitowa suka ga Aunty sai girgiza mama take yi, Ama maman a shinfide a kasa plat kamar wace ta rasu

Da gudu ya karaso yana dauke hijabin Mama da ya rufe mata fuska ruf ya kalli fuskar,

Da sauri ya kai kunnensa wajen kirjinta ya saurara kirjinsa na bugawa, ya kama tsintsiyar hannunta ya rike, ya kuma taba gefen wuyanta

Da sauri ya dago yana duban Anna ya ce" Suma ta yi, Anna ku kamota mu kai ta asibiti kar kwakwaluwarta ta kara tabuwa, shok ne, "

Da sauri ya mike ya nufi waje ya bude kofar .....

Yana budewa Aliyu ya karaso da sauri ya duka. Yannayinsa du ya kara daurewa saboda halin daurewar da uban gidansa ke ciki ......, Da sauri ya ce"

43

Da sauri ya furta" Ka matso mota"

Daga haka ya juya ya samu su Anna sun kama mama ita da auntyn yara sun nufo wajen da ita

Haka suka hadu suka dunguma asibiti harda su Malan baki daya du hankalinsu a tashe

A lokacin da suka je aka karbe ta aka yi ciki da ita, nan da nan likita daya ta shiga bata kulawa sai nurse biyu dake tare da ita, domin ita ce da aiki a ranar a matsayin likitar mata kuma Babar likita ce kwarariya........

Sun jima sosai kafin su fito ta nufi office din ta bayan ta nemi ganin shakikanta , hakan ya sa Malan da IMAD shiga wajenta
Chapter 72 · 0% Book details