Sashe 28
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Auntyn yara ta mike ta fito daga dakin ta tana dage labule ta ce" Bari ku ga mu hasa gawayi mu yi dafa duka sai a ci gaba daya harda maman naku idan ta shigo ko? Ku mayar da kayan miyarta akoy saura a nan kar mu lalata mata nata kun ji yan albarka na?"
IMTEE ce ta mike ta mayar da kayan , sannan suka dawo suka hadu da AUNTYN yara
Cikin ikon Allah da hikima ta ringa saka su aiyukan , ya zamo hatta zuba kayan miyar a cikin tukunya su suka yi, har ya zamo suna gardamar Ni zan duba yanzu, a'a Ni zan duba.....
AUNTY amarya na zaune tana murmushi zuciyarta na wankewa daga dacin da ta shaka yau har ya zamo sun gama
A tausashe ta ce" Idan an gama abinci yaya ake yi?"
A'isha ta ce" zubawa ake yi a ci a koshi aunty"
AUNTY ta yi murmushi ta ce" Kafin nan me ake yi?"
A hankali IMTEE ta dubi aunty, a hankali sosai ta ce" Za'a zubawa mutanen gidan kafin a zuba a ci ko aunty?"
AUNTYN yara ta hana hawaye fitowa daga cikin idannuwanta a hankali ta ce" Eh , za'a zunawa jama'ar gida, za'a daidaita yadda zai ishi kowa, a tatare komai a kilace, an fi so idan ana aiki ana wanke abinda aka bata, ya fi tsafta, sannan ana daidaita bakin murhu, ba'a cika son tara kazanta ba, idan kuwa ka fi so sai ka ci zaka wanke kwanonin ma ba laifi bane, abinda yake laifi kuma kazanta shi ne ka tara kwanonin nan kace sai gobe, idan ba rashin lafiya ba ko wani abu mai mahimmanci ya shigo maka ba wani alfanu da tara dati kudaje na bi, wari na buga ciki ace sai gobe ko sai an tara na kwana biyu ko sama da haka kafin a wanke.....kun fahimta???"
Kai suka gyada, IMTEE na tunanin wata magana da suka yi da mama wani lokaci da ta gama girki , girkin harda koko, ya zamo guda sai bin kwanoni suke yi, ta so wankewa sai maman tace da ita kawai ta kikifar da su ta je ta huta wannan ai alamun an ci an koshin kenan a gidan su, idan ba wannan ai ba'a wani ci ba Kenan.........., mama kenan.
Abincin nan suka ci, auntyn yara ta rasa ina zata tsoma zuciyarta dan dadi, suna daf da shinfida tabarma saboda tace su zo su yi firar dare maman yara ta shigo
Lamarin maman yara da ba gajiyawa da fitina sai ya zamo tana tardo wannan abin da bacin rai ta kama dukkan A'isha cikin bacin rai ta ce" Ke da baki da zuciya baki san zafina ba shine har kika shiga harkar wace ta tsane Ni? To bari ki ji, a kan shiga lamarin Rahama sai in tsine maki albarka dan Ni na haife ki ba uban wani ba, wuce min daki marar mutunci kawai........"
Wannan lamari ya Tsorata A'isha, IMTEE, da auntyn yara, ya zamo kowane a darare ya iya rabar wajen kwonciya saboda an gama daga musu hankali...., ita IMTEE kam da sando ta sadada ta je dakin, AUNTYN yara na saurare dan ta yiwa kanta alkawarin idan ta koro IMTEE tabbas zata kama abinta ne ta kwontar a gefen ta, ama sai ta ji shiru, hakan ya sa ta rabu a shinfidarta cike da tunanin shirun Malan da Sulaimana yayi yawa , dan har zuwa lokacin basu shigo ba.
(YAR UWA , MUNA TAFE DA TSARIN DA ZAI IYA SAKAWA KI SAMU NUTSUWA TA HANYAR SAMUN ABIN KASHEWA DA GARANTEE, A GABAN MU AN YI DA YAWA SUN FADI WARWASSSSSS, AMA BANDA META FORCE.... KWARAI MAGANA CE TA GASKIYA WACE IDAN KIKA SHIGO ZAKI TARAR DA ALKHAIRI, KE DAI KI YIWA HAJJA TAMU MAGANA, KIN SHIGA HANU MAI KYAU DAN YIWA DUKUYARKI JAGORA MAI KYAU, TARE DA HAJJA A TAFIYAR META FORCE.....FARIN CIKI DAWAMAME)
Sulaimana da abokinsa Ashiru
A shagon gidan su Ashiru ya wuni, domin tunda ya fita bai wani nufi kantin babansu ba, gaba daya irin yadda zuciyarsa ke kuna sai ya wuce shagon abokinsa ya kwonta ya ringa barci, har sai da magariba ta gabato ya farka cikin magagin barci da sakewar abinda ya hadiya ya mike da sauri yana duba wajen window ya ga duhu duhu, hakan ya tabbatar masa wuni ya yi cir cikin halin da yake ciki, ba sallah ba salati......
Shigowar Ashiru da hasken waya yana haske shi dauuuuuu ne ya sa ya zuba masa ido kamar yadda shima ya zuba masa
Ashiru ya bude baki ya ce" Ka farka Kenan?"
Sulaimana ya dan sosa keya murya cen ciki ya ce" Ashe nan na zo? Ka yi hakuri zan kuma jaza maka fada a wajen mahaifinka, nima ban san na nufo nan ba...."
Ashiru ya zauna yana dubansa, jiki a sanyaye ya ce"💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
_PAID BOOK_
*BY*
_SAJIDA NIJAR_
*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618
*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*
*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*
*16*
Ashiru ya zauna yana dubansa jiki a sanyaye ya ce" Kai abinda ya fi damunka kenan ko?, Sule yaushe zaka gane cewar wannan hanyar ba mai bule maka bace?, wai me kake so da rayuwarka ne? Me kake so ka mayar da rayuwarka?, ka wuni a yashe, ba ci, ba sha, ba tsafta, ba ibada, kai da ka san ma'ikan mutuwa na zuwa a duk lokacin da aka bashi umarnin daukan ranka, ba zai kara koda second daya ba zai cika umarnin mahaliccin sa, ama kake shagala irin wannan, da abin da zai nisanta ka da mahaliccin ka, da iyayenka, da jama'ar kirki, ya kusanta ka da mutanen banza......., abinda ke iya kaika ga halaka, sule Allah ya kiyaye idan ka mutu a halin maye a halin maye za'a tashe ka, domin fadar Allah ce, a duk abinda ka mutu za'a tashe ka a abin, walau alkhairi ko shari..... , shin kai wani irin mutun ne da bai san ciwon kansa ba? Me kake so ne a duniya????"
Ashiru ya sassauta ganin sulaimana ya zauna yana ta wani irin huci
A sanyaye ya ce" Kai ne baba a gidan ku, kai ne namiji, kana ganin fafutukar da mahaifinka ke yi dan ganin gidansa an fi karfin komai, kana ganin kokarin da yake yi a rayuwa dan ganin an samu ci gaba a gidan sa....., kai kai ne hannunsa na dama, kai ne abinda zai iya duba ya ji sanyi da tunanin koda mai faruwa ta faru da shi ya barwa iyalinsa bango majingina.....,maimakun ka dage, ya zamo ka amsa sunnan bangon da ake kiranka da shi, sai kake dagewa dan ganin lalle lalle ka tonawa kanka asiri ka haukata kanka da kwayoyin dake kashe duk wata garkuwa ta jikin dan adam.....????"
"Ba zaka gane ba!" sulaimana ya fada murya cen kurya
Ashiru ya Dube shi ya ce" Ka ganar da ni, so nake in gane, kai abokanan banzan ne ba zaka fasa bi ba , ko kawai kai ba zaka tausayawa iyayen naka da kai kanka bane....?"
"Sun maida min uwata tamkar wace bata da komai a kirjinta sai jan nama....., a bayyane nake gane matarsa munafuka ce, ama dan ya fi son ta da uwata yake muzguna mata......, an fada masa idan ya sake ta ba zan iya rike abina bane??????"
Sulaiman ya fada da dakewa kafin ya daki kirjinsa ya ce" Namiji ne Ni, ko da dako zan iya ciyar da uwata , karyar wahala ta kashe Ni a hanyar rike mahaifiyata, Ama itama da ka ganta sonshi take yi a haka, du inda na bilo mata sai ta ga sabo ma nake yi, idan ta sakani a gaba tana min wa'azi a kan wancen salamamiyar sakaryar da aka hada kai da ita ake cutar mamanta da kuma shi baban namu sai in ji kamar in yi ta rusa kuma......sai kuma....... Sai kuma........sai kumaaaaaaaaaaaaa"
Ya yi shiru yana dafe gaban goshinsa kansa na sarawa saboda tarin abinda ya rike masa kirji yake gigita shi...........
A irin lokacin kuwa mahaifin Ashiru da shi Sulaimanan sun jima tsaye sunna sauraron su, tunda Ashiru ya saci jiki ya bace musu a lokacin da Aban yara ya zo tambayar ko sun ga sulaimana, mahaifin ashirun yace lalle lalle su bi Ashiru dan kuwa yannayinsa ya nuna wanda bashi da gaskiya tiryan..........
"Kuma me?" Ashiru ya fada yana dubansa......
Da jin haushi mahaifin Ashiru ya so kwashe labulen dake kofar shagon, sai baban yara ya rike da sauri yana ɗan daga masa hannu alamun ya dan dakata........
Sulaimana ya ja numfashi ya ce" Ni ban san cewa Allah ya juya min baya ba sai da idan na kalli A'isha nake jin bugawar zuciya irin wace kanwarka tace tana ji idan ta ganni wai soyayya ce ba......, Ashiru na gama shiga uku Ni kam ai na gama lalacewa........., magana nake maka a kan A'isha ta............."
"shiKenan ya isa haka kuma kai dan ubanka tashi ka bi ubanka!" Mahaifin Ashiru ya fado ransa bace ya jimko hannun sulaimana ya fito da shi
Tsuru tsuru suka yi, su kalli iyayensu su kalli juna, Ama suka kasa tambayar abinda ya tsaye musu a wuya dan tsoro..........
Aban yara ya nunawa Sulaimana hanya ba tare da yace da shi komai ba
Hanyar suka ɗauka suka nufi gida, a wajen baban masallacin isalamiyar su IMTEE suka daura alwallah suka shige masallaci, bayan sun bi sallah ne mahaifinsa ya masa umarnin ya nutsu ya gabatar da salolin dake kansa sannan ya fita waje dan ya jira shi.