← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 141

Sashe 57

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani irin gaggawa Farhana ta karaso ta suri hannun IMTEE kasa kasa sosai cikin Yaren turanci ta ce da Murtalab " Please ka bashi hakuri, mun tafi, bamu san ku ne a nan din ba, da bamu zo Bama"

Sai kuma ta ɗan dubi ƴaƴanta a hankali ta ce" mun tafi mu yi wasan yaya, a huta lafiya"

Tana fadin haka IMAD ya dauke dubansa daga kansu ya juya da nufin tafiya ya ga tahowar aliyu da mugun sauri

Da ido kawai ya masa alamar ya koma, hakan ya sa ya ja ya tsaya ya shige gabansa kafin shima ya mara masa baya.........

Da karfi ta sake jimkar hannun Hallah dake son janye hannunta ta ja da karfi ta ce" Wuce mu je NUR !"

Bin bayan nata kawai ta yi takim takim ta yi mata ja irin na ko baka son tafiya za'a ja ka ne

Basu tsaya ko ina ba sai da suka isa daga baya kusa da office din Anna

Ta kwabe dan kwalin kanta da ta yafe kan nata da shi sosai ta yi baban mayafi da shi, ta nuno Nur da yatsa ta ce" Ke Ni zaki saka a uku? Ni zaki saka a halin ha'ula'in rayuwa?? Kwace mu daki juna, idan ban nuna maki yayarki nake ba ba zaki taba bani lafiya ba, Ni zaki amsawa mutumen dake iya cin ubana a gaban wanda ya ga dama ba tare da an bi min kaidi ba? Ni??"

Muryar dake tashi sama sama ta sa Anna yin shiru da mamaki kafin ta mike a hankali ta ɗan ja abin window din ta sauke dubanta a wajen da take jin hayaniyar

Tana fada tana cakumar Nur ne, wace itama ta kama hijabin ta sauke saboda ta cakumeta sosai

Ai kuwa Nur itama ta cakumeta tana fadin" Farhana idan ba lalasaki na yi ba ba zaki bani lafiya ba, bari ki gani!"

Ido Anna ta zarro tana hangen su kafin ta bude window din gaba daya tana duban su ta ce" Kai kai....me kuke yi a nan? Ikon Allah, FARHANA, HALLAH?"

Da sauri suka saki juna suka biyo sunna kallon window din kowace da alamun Tsorata da ganinsu da aka yi

Anna ta gyada kai tana jimke baki irin lalle ma din nan, kafin ta ce" Sai ku zagayo yanzu yanzu , ku zo!"

Tana gama fada ta zuge window din office din nata ta koma ta zauna saman kujerar ta ci gaba da cike bayanan da IMAD ya tambayeta wa'inda du take so a zuba mata a makarantar

Sumui sumui suka shigo, Farhana a gaba, Hallah na biye da ita a baya

Sunna shigowa Farhana ta karaso da dan sauri ta ce" Anna, kin san yarinyar nan rainin da ta min ya wuce misali kuwa?, kawai fa magana muke yi da ita ashe yaya na cikin Library din nan , kawai ya kama mu, Anna bai ce da mu komai ba, Allah ya sauko masa da zuciyar tausayi yace mu je mu yi wasan mu shine ita wannan jani jau din mai shegen son girman tsiya ta dubi idannuwan Yaya tace da shi wasa Kuma? Anna yaya ta cewa wasa kuma? Idonsa idonta ta tambaya Anna, shi da kanshi yau ya san ya hadu da wace aka cire tamanin a kaso darin hankalinta....., Ni zata janyowa abinda ya fi karfina ko? Gwara in san na mata dukan tsiya Ni karamin alhaki kafin ta tabo gwaskan!"

HALLAH dake cike da farin cikin ganin Anna, sai dai yadda Anna ta daure fuska ya sa take tsayen itama kanta a ƙasa cike da tsoron bacin ran Anna din, ama haka bai hana ta saukewa Farhana harara ba ta ce" Kike ya faman fadin yaya yaya yaya, waye shi? Ni ban san shi ba ai, kuma a kan me zai Dube mu yace mu je mu yi wasa???? Yara ne mu???"

Anna ta sake zubawa Hallah ido

Farhana ta ja salati ta sanar da Ubangiji kafin ta dubi Anna ta ce" kin gani ko? Yarinyar nan bata fa hankali fa, Allah bata da hankali, ki nemi iyayenta su zo su tafi da ita kawai...."

Anna ya mayar da dubanta kan takardar dake gabanta a hankali ta ce" Da kika ce masa wasa kuma? Ya kale ki?"

Farhana ta dubi Hallah, Hallah ma ta dubi Farhana........., da ido Farhana ta mata alamun sai ki bada amsa

HALLAH ta ɗan sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Ban sani ba nima Anna"

Farhana ta sauke nata harara ta ce" ya kale ta wallahi!"

Anna ta sake dago idannuwanta ta sauke a fuskar HALLAH, duba na dan lokaci kafin ta dubi farhana ta ce" A lokacin ina gadanga yake?"

Farhana ta dafe kirji ta ce" Ai Ni wanda ya fi sakawa na kamota muka fito kenan, dan kuwa yana iya ƙaryata, Anna kina tune lokacin da muka je haji gaba ɗayan mu? Ranar da wani Balarabe ya bige hannun Yaya? Marin da gadanga ya masa har yanzu na daya daga cikin abinda ke Tsoratani cikin dare ......, y'ar nan gwara dai a mikata hannun iyayenta tun kafin ta janyo maki matsala Anna !"

Anna ta dauke idannuwanta ta sake duban HALLAH, yanzun ma duban har sai da HALLAH ta dago ta dan dubi Anna din, sai ta ga ta dauke dubanta ta yi dan murmushi ta ce " Me yasa kike susar kan nan?"

Nur ta dauke hannunta dake saman kanta tana dan yamutsa fuska saboda kaikayin da yake yi mata........

Farhana ta je saman kujera ta zauna tana sauke numfashi ta ce" Tun Dazu take susar nan, ta yiwu kwarkwata ce"

HALLAH ta Dube ta da wata hararar kasa kasa ta ce" Ba dai zaki daina kawo min raini ba ko? Zaki yi bayani!"

Kwarai Anna ta ji ta, hakan ya sa ta sake binta da kallo tun daga kasa har sama

A tausashe Anna ta ce" amshi byro din nan ki bata ta kunce maki kan"

HALLAH ta dubi Anna, byron da ta dauka ta miko mata ta bi da kallo...
A duniya abinda bata so abinda zai taba mata kanta ne, har fa kuka take idan zata yi tsifa ko in aka matsa mata sai ta yi kitso, shi yasa wani lokacin har wata biyu kanta ke yi da manyan kitso kwala kwala, wani lokacin kuma idan ta kunce shi ta kama dunkuma masa hula sai ya fi wata uku ba'a san me yake ciki Bama bale har a sa ta yi kitson, dan mama ba abinda ya shafeta da wannan, aunty ce idan Allah ya sa idannuwanta suka kai kai take matsa musu har sai sun je sun yi kitso.

Karasawa ta yi, ta ɗan rage tsayinta ta amsa da hannu biyu, sannan ta juya ta je inda Farhana ke zaune tana hararta itama, ta mika mata murya a raunane ainun ta ce" Dan Allah farhana ki min a hankali kin ji?"

Farhana ta dube ta da mamakib yannayinta kafin ta amshi byro din ta janyo hannunta ta girka ta a gabanta ta ce" Zauna min, inada aikin yi da yawa a gabana!"

Kai kawai Hallah ta soke saman cinyoyinta, FARHANA ta shiga neman bakin gashin wanda ke dunkule sosai cikin junna, da kyar ta samu ta warware su, kwaya shida ne kawai ta mikar da su tana kallo da mamaki ta sake duban kalar fatar Hallah, bata ce komai ba ta shiga tsefe mata saboda idannuwan Anna a kansu.......

Murmushi Anna ta yi sannan ta ci gaba da rubutun da take yi ba tare da ta kuma ce musu komai ba..........

Farhana kunce kan HALLAH tana mamakin tsayi da cikar gashinta.....har ga Allah bata taɓa sanin Hallah nada gashi irin wannan ba, sam bata taba tunanin haka ba.

Tana gama kunce mata shi ta shiga haɗe shi ɗan ta daure mata shi a tsakiya, domin ba abin cajewa a nan din, hakan ya sa Farhana ke jin zafi sosai, harma ta rintse ido da karfi tana jin zafin hakan

Wanda ke daure da bata gashin ta cire guda karami ne dama ta nemi hade gashin, sai dai ko dan yanzu ta kunce mata shi kuma alamu sun nuna irin yadda ya yi dati, sai abin daure gashin ya ki rubanyuwa......

Farhana ta dubi Anna zata yi magana aka dan buga office din

Anna ta kai dubanta da kula ta furta" Yes com.in"

Kasancewar ta ga wanda zai shigo din ta caméra sai kawai ta maida dubanta nan

Aliyu ne ya bude masa kofar , ya fara sanyo kansa....sai Mutalab dake bayansa

Da sauri Farhana ta mike ta kunce dan kwalin dake kanta ta yafa a saman kanta, sannan ta aniya dungurar kan Nur dan ta ganar da ita ta rufe gashin kanta

Nur ya dago fuska shabe shabe da hawaye ta dubi Farhana kanta tsaye da bayanta ta tura ta baya , sai da Farhana ta yi dabar a saman kujerar nan sannan ta dafa ta mike tana kallon Anna, wace ta zuba mata ido itama

A tausashe Anna ta ce" Kukan kunce kan ne kike yi Nur?"

Nur ta sada kanta tana shasheka, sam bata wani zabura dan daukan hijabinta dake kusa da Anna ba, hasalima sake sauke dubanta ta yi a kan Farhana ta sake fashewa Anna da kukan tabarar da bata san dalilin da ya sa kukan da iya Mama take yiwa a duniya ta samu kanta da yiwa Anna shi.......cike da sangarta ta ce" Anna......, kin ga ban san kin zo yau ba, dama kullum kullum kina raina, na rasa yaya zan yi in ganki, kullum cikin tunaninki nake , yau na yi niyyar zuwa gidan koda ba za'a barni in shiga ba dan kawai in gan ki....., shine yake ta cin zalina tun Dazu, Anna kalli yadda ta ja min kai kalli............."

Farhana ta langwabar da kai, saboda ƴaƴanta ya karasa saman kujera baba ya zauna yana dan sake sauke dubansa a kan HALLAH domin fashewa ta yi da kuka tsakaninta da Allah hakan ya sa ya dan sake zaro ido yana dubanta a lokacin da Anna ta ce" To kuma shi kenan sai kuka? Ba gani ba? Ko baki yi farin cikin ganina bane?"
Chapter 57 · 0% Book details