← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 141

Sashe 120

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwansa kawai ya lumshe, a hankali ya ce" Sai kin cika sharudan da nace maki, ko nan zaki zo inda nake ki saka hijab, ko falon kasa ne, ki ringa saka katon hijab da nikaf, idan kika RINGA sakawa zan duba kin ji?"

Nur ta yi dan tsai kafin ta ce" Zan dai ringa saka madaidaicin hijab din in sha Allah, Ama nikaf din ne nake ganin in na saka ta yaya zan yi saurayi to????, dan Allah ka duba yayana, bari in je kar Anna ta yi wankin nan"

Da sauri ta juya ta fice tana ja masa kofar

Kofar ya bi da kallo, .......kafin ya sake yin irin kwoncin da yayi dazu yana kai hannayensa wajen gashinsa ya ringa cakudawa a hankali yana sauke ajiyar zuciya......

Innalilahi, to wai meye haka? Zai iya rantsewa a tsarin barin da mace ke iya BIRGE shi ma babu irin halittar nan, shi yana son mace mai tsoron waje, mai kiyaye harshe, mai rufe jiki ruf, wace bata fada da kowa, kuma mai jin magana......, to ama me yasa yake jin dadin fira da ita fiye da komai? Me yasa ta saka shi cin abinci kuma ya ci kawai dan kar ta fita tana kuka da wani tunani a ranta a kansa marar dadi? Me yasa ne yake jira ta fada ya bata amsar da zata gansar da ita?......ya Allah..........me yasa kalonta kawai ke saka ya ji murmushi na son kubuce masa? Me yasa du abinda zata yi yake jin kai tsaye shi ya shafa? Me yasa yake jin dole ne ya kare mutuncinta kai tsaye kamar nasa mutuncin??????

A nutse ta je dakin Inna, a hankali ta shiga , ganin Inna na barci kuma Anna bata nan sai ta fito a hankali ta nemi bin elevator

Sai dai tana kama hanya ta tuna maganar hijab, hakan ya sa ta juyo ta nufi dakin Farhana, ta bude ta shige hankali kwonce ta je ta ja hijab din da Farhana ke kai tana barci ta saka sannan ta juyo tana fadin" Dila gyara kafarki Indo kin wani baje "

A'isha kam kafar ta gyara saboda karatu take yi, kuma bata so ta hana ta, litafi ta samu na Hausa a wayar Farhana, gaba daya ta saka hankalinta wajen karatu shauki na dibanta..........

Tana rike da basket din ta samu kanta da ganin ya bude , wato ta bayyana a kasa

Wani murmushi ta saki ta sake kallon wajen da ta dana, wato du idan Farhana ta dana sai ta rike me ta dana,

A nutse ta fito da basket din, ta fara tafiya dan nufar kicin hankalinta ya sauka a kan tarin mutanen dake falo, WA'INDA ke magana kamar tattaunawa ce mai matukar mahimmanci suke yi, kamar tattaunawa ce mai girma suke yi, kamar ma Anna ke magana, sai dai fitowarta ya sa ta yi dif

Kasa kasa Mama ta ce" Ya Allah, Anna dama yarona ita yake so ake wahalar da mu?"

Da sauri Anna ta Dube ta hadi da girgiza kai, AUNTYN yara kuwa tunda ta ga Nur ta saki murmushi hadi da nufowa da basket din, hankali kwonce kusan Anna ta ajiye kasa kasa ta ce" Anna, ya ci , ga kwanonin bari in kai kicin......"

Sai kuma ta dubi tarin dandazon mutanen nan wallahi du ita suke kallo, banda abanta da auntynsu

Tsarguwa ta yi, kafin ta iya bude baki a jimulce ta yi musu gaisuwar baki daya, sai kuma ta mike a hankali ta zagaya inda abanta yake ta shagwabe fuska ta ce" Abana dama ka zo shi ne ko ka nemo Ni?, , abana da baka nan Auntynmu sau biyu tana kai min duka, kuma ta yi tafiyarta asibiti ta bar Ni dan kawai na cewa yayan FARHANA a fido min mamana, Abana ya dace a fido min Mamana saboda a bayyane yake idan muka koma gidan Auntynmu na iya dukana safe, rana da dare, Ni kuma ba son dukan nake yi ba Abana ka ji?"

Murmushi yake yi, a tausashe ya ce" na ji autana, tashi mana ki je abinda zaki yi kin ji????"

Kai ta gyada ta ɗan kalli auntynsu da ta zarro ido da mamakin sangarta irin ta NUR, a hankali ta ce" AUNTYNmu ina kwana"

Sai kuma ta mike tana turo baki irin ita an yi mata ba dai-dai din nan ba, ta zagaya ta dauki basket din tana kara cika da mamakin kallon nan kafin ta wuce ciki

Tana tafiya Anna kasa kasa ta ce" Dan Allah ku fahimce Ni, kar ku yi haka, yarinyar nan ina so kwarai yaron nan ya nuna mata soyayya kuma ta amsa da bakinta, sam bana so a yi mata fin karfi, bale ace za'a daura mata aure a yanzu yanzu, haba dan Allah sai kace ba budurwa ba?........dan Allah ku bar maganar nan "

A tausashe Malan ya ce" Annar yara, ya ci abincin kuwa?"

Anna ta sada kai, ta kasa amsa wa

Mama ta yi murmushi ta ce" Ya ci Malan "

Malan ya yi murmushi yana duban Aban yara da uncle a tausashe ya ce" ina ga, amsar da ake so gatanan, kuma zan so a yi masa uzuri a bashi dama a bashi ita....."

Aban yara ya sake jinjina kai cike da mamakin wannan lamari, a tausashe ya ce" Bani da haufi a kan lamarin nan, kamar yadda na fada maku babansu na hanya, saboda da na yi kiransa da safe na sanar masa maganar dan nasa yace Gayanan tafe da Yama zasu taho, Ama bari in yi kira yanzu ma in kuma sanar masa da wannan, Ni dama ai ban ga wani amfanin zaunawa da yarinya ba, auren fari ne, muna da damar yi mata miji, kuma ina kyautata zaton auta zata yi biyayya ko auntynsu?"

AUNTYN yara yanzu kam sai ta dubi Malan da mamaki a hankali ta ce" Haba Malan dan Allah a daina saka Ni....." Sai kuma ta sune kai cike da jin kunya

Anna ta ce" A'a a saka ki wallahi, kuma kin ce baki yarda ba, Aban yara bata yarda ba sai idan Nur tace tana so, dan haka a kirawota a tambayeta idan tace bata so Bama sai an yi maganar ba"

Aban yara da ya turawa baba na Magarya kira , ya zamo wayarsa sai an saka amsa kuwa , wayar kuma ta fara ringin, ya dubi uncle da ya dubi Abdul bassit ya ce" Abdallah, tashi ka kirawo min IMAD, lalle lalle ya sauko yanzu, domin ba zan daura masa aure baya nan ba, idan kuwa ya ki saukowa kace masa nace ina gayatarsa daurin auren yarinyar nan"

Ya karashe yana murmushi hadi da duba wayarsa da sir ya maido sakon abinda ya tura masa, wato magana a kan IMAD ɗin ne

Abdul bassit ya mike yana murmushi ya nufi elevator

Dagawar baba na Magarya ke da wuya ya ce" Man AHMADU Ni ko kai ma Amaryar zaka yi ne?"

Aban yayi dan murmushi yana duban wayar, domin sam bata da sirri, kuma a ransa yake jin idan ya tashi ya fita kamar mutanen ba zasu ji dadi ba

Dan haka a tausashe ya ce" Malan, dama wata maganar ce ta taso, shi ne nace bari in sanar maka kafin ka zo din, abinda ka ce"

Malan ya ce" wata maganar? Kar dai kace min bayan na yi ta lalabaka kan maganar ginin nan so kake ka kiya ne Ni?"

Da sauri Aban yara ya ce" A'a ba wannan maganar bace, maganar auta ce "

Malan ya ce" To to to, auta tawa, auta jaja manya, me yake faruwa da autar ne?, man AHMADU kar ka yarda kace min marar mutuncin yaron nan ya rarasheka ka hakura zaka bashi auren auta, dan kuwa na rantse maka sai dai in alwali zaka CENZA mata ka wulakantani, wannan kenan, domin ba abinda zai sa Ni din nan in bashi y'ata, daga shi har uwarsa kuma ina nan tafe sai na kai musu ziyara na fada musu ai Allah ke azurtawa, kuma sun yi tsugul su hada min ya'ya kishi, son abin duniyar namu bai kai cen ba, tunda duniya ta gama yin lalacewar da ake yiwa kowa kudin goro ace son abin duniya na damun kowa, su din ma tunaninsu kenan tunda har suka iya zuwa da wannan magana"

A tausashe Aban yara dubi AUNTYN yara da ta kame baki kai a kasa ya ce" ka yi shiru mana in fada maka , ka ga autar ce ta yi miji kuma ake son daurawa a kusa kusa, wato so ake yi a daura shi a yau idan har hakan ta samu, shi ne nace bari in kira"

Malan ya ja salati yana sanar da Ubangiji ya ce" Miji kuma ? Kai tsayen nan? Me ta tsare maka da kake son rabuwa da ita ta karfi haka?, a'a a'a, haka kawai sai ta yi miji kai tsaye ka mika ta? Waye? Ka san shi ne? Ka san usulinsa ne? Gani nan tafe kar a min wannan danyen aikin ba zai yiwu ba ka ji na fada maka idan gani kake yi zaka kawar da y'ar uwarta ita ta zame maka kaya a gabanka sai in hado abina mu taho nan, dama Ni rigimar auta ado ce a idannuwana Gaskiya!"

Malan baba na murmushi ya mikawa Aban yara wayar a tausashe ya ce" Malan Bismillah dan bani wayar"

Mika masa yayi kafin ya ringa girgiza kai,
Wato mutumen nan ba dai rigima ba

A tausashe Malan baba ya ce" ASALAMU alaikum Malan, Ni ne Malan na baban masallaci "

Tausasa murya Malan yayi, saboda ya gane wane yake nufi , haka kuma a zuciyarsa ya shiga tunanin kar dai shi ne ke son NUR din?

A tausashe Malan ya ce" Ka yi hakuri Malan, mun dame ka da kira, kiran ne ya zama wajibi a yi maka shi, mijin da ya fitowa HALLAH Elhaji IMAD ne, yanzu haka muna nan tare baki daya da duk wani mai fada a ji a lamarin rayuwarsa......, muna Bara a bamu, idan har hakan ba damuwa, muna so a bamu , kuma bama so a ja saboda wasu dalilai masu karfi............."

Mikewa Malan yayi tsaye yana rike wayar da hannayensa bibiyu

Kasa kasa ya ce"Allahu Akbar, wai Mai gida ake nufi?"
Chapter 120 · 0% Book details