← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 141

Sashe 25

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Tallah, mun kasa rabe ka siyar mana

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

*14*

IMTEE ta turo baki ta ce" Ke Dilla wuce mu tafiyarmu, to mu kuwa me muka masa??"

A'isha ta sauke ajiyar zuciya ta koma bayan Imtee, suka nufo gidan suna dari dari, Ama kan IMTEE tsaye ta nemi raba gefen yaya Sulaimana ta shige

Ita dai bata san lokacin da ya riko hannunta ba, sai baya da ta ji ya dawo da ita ya riko kumatunta ya aniya gaura mata yan tagwaye masu zafin gaske

Ihu ta shiga zabgawa da dira, A'isha kuwa ta saki jakar da gudu ta yi cikin gidan itama tana ihun

Mahaifinsu dake ciki ne ya taho da saurin gaske ya karbe IMTEE a hannun sulaimana ya zuba masa ido, irin yadda idannuwansa suka yi ja alamun dama ransa a daf da ɓaci yake kuma aka kara masa wani bacin ran ta hanyar yin maganar wa'inda suka zo neman a basu damar dansu ya nemi auren IMTEEn

Hannu ya nuna masa , har zai yi magana ya ajiye ya nufi ciki, saboda maman yara da ya hango zani a hannu zata fito

"Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, ya jirkice min fuskarta, sulaimana idan ka yiwa yarinyar nan rauni ko uban ka ba zai rabani da kai ba, sai na kai karar ka kotu, idan ka yarda ka yi mata wani abin da zai fito da muninta sulaimana ka kade, ......" Sai kuwa ta rushe da kuka tana riko Imtee dake kukan itama

Rai bace ta dubi aunty dake tsaye ta ce" Ke kam Allah wadai da kamarinki, makiyiyar y'arta ta cikinta, shin ke ba zaki so ta yi aure Bama ko? Ba zaki so Imtee ta samu darajar aure a kanta ba ko? Ke burinki to ta yi karuwanci ko me????"

" Ki sassauta kalaman ki maman yara, sun yi tsauri ko a kunnan yayanki" Aban yara ya fada yana kokarin katse fushin maman yara

Maman yara bayan ta tura Imtee dakinta da karfi ta juyo tana duban baban yara ta ce" Ai zuwa yanzu ko me zaka ce ya daina bani mamaki, saboda na gama yarda cewar kai fa an gama shanye ka, Malam kai fa honko ne kawai sai yadda ta yi da kai, to meye ba'a kada an baka ka sha ba, an matsa kuma ka anfana, to ka ga ai dole ka ringa jin maganar kowa wai a kan tata, Ama in ba wannan ba Malam har Ni matarka zata ƙaryata? Daga sake dauko maka maganar manemin auren yarinya na fada maka yau ma sun leko Shikenan sai tace ita kam tana ina wai suke zuwa? Ni makaryaciya ko? Nace Ni makaryaciya ko?, to malam ka ci gaba da rintse ido tana korar maka maneman auren y'ar ba tare da ka gane komai ba sai an wayi gari wata rana wanda zai ce yana son Imtee an gagara samu!"

"Kin ga maman su, ki fa iya bakinki wallahi, kin ga bana so in nuna maki cewar sai kin jira, Ama kina so ki sa yaro ya wayar maki da kai cewar sai kin jira, aikin banza to ai ko bar aunty da rashin kuzari da tsoro uwa farar kura da rufe asirin munafurcin ku, Ama aunty ai ba zata yi karya ba gaskiya, ita ai bata iya wannan ba, to ke in ba jaraba ba wai ita HALLAH din y'ar waye? Yau Ni na ga BALAKI ganin idona, to wallahi ki kiyayeni, kar ki sa in saka maki hannu!" Sulaimana ya karashe yana zaro ido da dan marowa kamar zai shako maman yara

Da gudu ta yi ciki tana ihu, Malam kuwa ya tare shi hadi da zuba masa ido, a tausashe ya ce" Kana ji? Ka wuce kawai, ka je kanti ka jira ni, Allah ya shirye ka"

Sulaimana ya gyada kai yana ta gaba yana baya, da hannu ya yiwa auntyn yara alamu ya ce" Je ciki ki buya ki sha kukan ki, tunda ke shi kawai kika iya, Ni nan zan ci kaniyyyyyy"

"Sulaimana idan ban wanka maka mari ba ka ce ba Ni bane!" Mahaifinsa ya fada da karfin da ya sa yayi gaba yana fadin" A huce haka, eh, a huce Malam Ahmadu!"

Aunty a hankali ta silale ta sada kai hawaye wani na korar wani

Malam kuwa ya shige dakin mama ya yi kiran maman da su Imtee gaba dayan su

Fitowa suka yi su duka suka zauna a inda ya nuna musu, inda Aunty ke zaune kanta a kasa

Malan ya ringa bin su da kallo harda mama wace du take darare, kana kallon ta zaka gane a tsorace take dan sai kofa take kallo

A tausashe Malam ya furta" innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Allah ya kyauta ......, yanzu wace riba aka ci da aka wulakantar da juna har haka? Fisabililahi wace riba aka ci da aka zo wannan matakin?, yanzu maman yara ranki ba zai bace ba ki yi abinda ake kira da kawar da kai da kame baki har sai kin ji ranki ya huce sannan ki yi magana a kan abu? Shin da suka zo din ba sai ki ce da su ga abinda nace ba? Su basu san inda zasu same ni bane? Idan da gaske suke ai su same ni, ni sai in ji abinda ke tafe da su ba,? Ama da yake ba a bakin komai maganata take ba sai kika karbe su har kike kara fada min abinda ke tafe da su???????"

Maman yara ta cire kai tana girgiza,

Baban yara ya girgiza kai ya ce" menene amfanin hakan? Ribar me aka ci da aka yi haka? Ki duba ki ga irin yadda Sulaimana ransa ya ɓaci har yake neman zagin ki...."

"Malan, yanzu dai idan zaka gama ci min mutunci da wulakanci a kan IMTEE, dan kawai na dauka cewar da gaske kai kake Ni mamanta ne na kawo maka maganar mai neman aurenta ka ci ka gama, Ama Malan ka daina sako maganar yaron cen dan kai da kanka ka san dan shaye shaye ne, ya sha abinda ya fi karfinsa ne ya nemi taba lafiya ta, malan ba zan ce maka komai ba Ama ina mai tabbatar maka idan ya taba min lafiyar jiki sai na rufe shi domin ba wani uzuri da zan masa tunda ya san me yake yi, ai bai rarumi uwarsa ba sai Ni da aka raina....., IMTEE kuwa gatanan, yadda kuka yanke kai ubanta da kuma ita uwarta nawa ido ne, Ama daga yanzu ta tataro kayanta ta koma dakin Rahama, idan tana so yau ta kwadata ta cinye dan kiyaya, zan yi ta mata addu'ar hutu a kabari, dan kuwa a duniyar na yi iya yina abin ya ci tura!"

Tana gama fada ta mike tana fashewa da kuka hadi da nufar dakinta ta saki labulaye ta ringa bodar kuka har ta gaji dan kanta ta yi shiru, du suna kallon kofar Tata, ba damar su tashi domin da suka gwada tashin ya hana su

A hankali sosai Aban yara ya ce" KHAIRY, samari kika fara kulawa a waje bani da labari????"

A hankali AUNTYN yara ta dago kanta tana sauke idannuwanta a kan IMTEE, wace ta sake sada kai jikinta na sake daukan rawa

A tausashe Aban yara ya ce" Wanene shi? Menene karfin alkarku da har ya nace sai ya zo? Ke kike turo min shi ne?"

Da sauri A'isha ta ce" A'a baba, ba ita bace, wallahi baba bata san da ya zo Bama, ya'yan kawarmu ne, a kofar makaranta ne ya hadu da ita, shine fa , shine yace yana son ta wai, daga nan ita bata turo shi gidan nan ba"

Baban yara ya zubawa A'isha ido na dan lokaci kafin ya gyada kai a tausashe ya ce" Allah ya kyauta, Ni ba zan hana ku aure ba idan shi kuke so, sai dai ba zan lamunci a yi ta min kai kawo da zance na bata lokaci da bata tarbiyya ba, idan har da gaske ne Ni zan neme shi da kaina saboda ba zan yarda ya ringa zuwar min gida yana karawa ba, ya daina tare ki a hanyar makaranta ya kuma daina min sintiri a kofar gida, yayi hakuri in yi bincike sai in bashi damar tsayawa, idan ya so sai a yi ko? IMTEE kin yarda da haka???"

Wani tsoro ya kama IMTEE, ta rasa me zata ce, kanta na kasa zuciyarta na bugawa

A tausashe Aban yara ya ce" Ni da nake cewa in sake dage dantse in yi ta zuba asusu saboda an ce islamiyar ku za'a kara ta boko a ciki, sannan karatun zai zama mai girman gaske? Ashe ke aure zaki nema da wuri haka? To Allah ya dafa mana, ya bani abinda zan kula da ku........., Allah ya shirya min ku ya tsare min mutuncin ku"
Chapter 25 · 0% Book details