← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 141

Sashe 64

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rai bace mama ta juyo ta nuno A'isha da yatsa ta ce" A'isha Ni zaki kawowa maganar banza a nan?, idan ba shi ya haife ki ba wa zai haife ki? A'isha idan kika kuma min wannan maganar Allah ya tsine maki..............."

"Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une!" Aban yara ya fada da karfin da ya sa du suka kale shi a tsorace

Malan na Magarya ya girgiza kai ya dubi maman yara sama da kasa , kafin ya dubi Aban yara a raunane ya ce" Da wahala idan ita ta haife ta, ka tashi mu je asibitin dabe din!"

Ido mama ta fitar, ta dubi Aban yara ta dubi Malan na Magarya

Auntyn yara da ta kamo A'isha ta janyota jikinta sosai tana dubanta ta ce" A'isha, ki yi shiru kin ji?, kar ki kuma yin magana kin san idan ran mamanki ya bace komai faɗa take yi, kar ki kuma yin magana kar ta maki bakin da zamu shiga uku kin ji? Ki yi shiru hakanan "

A'isha ta zuba wa auntynsu ido , a hankali ta kai dubanta kan su mamansu da suke shan wani gumurzun domin Malan yace a yau yau zasu je asibitin sai an ciro musu litafin shekarar haihuwar A'isha an fito da komai sun gani......, idan ya so ma ya yarda in maman ce ta haife ta Dan shi yanzun kam baima yarda ba, domin shi ya san mama ba mahaukaciya bace, kawai mutun ce mai son kanta da shegen fadan tsiya......ama ba maganar hauka, a rayuwa kuwa in ba hauka mace ke yi ba , shi bai ga ta inda zata tsinewa d'an cikinta ba

Maman kuwa a tsakuyarsu take rantsuwa take da abinda zai kashe ta yarinya Tata ce ita da Malan, du ta fita a hayacinta, Yaya sulaimana kuwa a tsaye kawai yake ya harde hannayensa ya dubi wannan, ya dubi wancen bai ce da kowa komai ba.

A hankali ta ce" Aunty, da gaske ba mama ce ta haife ni ba, aunty da gaske ba ita ce ta haife ni ba......., ni na san cewa ba ita ce ta haife ni ba.........., aunty mene abu daya da zan jinginu wanda zai sa in ce ita ce ta haife ne?, Ni gaba daya ban ga ko daya ba......., kin ga fa aunty Ni ban san dumin uwa ba, ban san wani dadinta ba......., aunty wai menene abu daya da zan rike ya tabbatar min ita ce mahaifiyata?, to ba gwara ta tsine min din Bama? Ta yiwu ma Umar wani tsinanen......."

"Idan baki kama min bakinki ba, zan wanka maki mari!"

Aunty ta fada da karfi kuma a mugun daure

A dole A'isha ta shige jikinta ta yi shiru, aunty tana kallon su Malan suka wuce su da SULaimana

A tsorace maman yara ta ɗora hannayanta saman kanta ta shiga ihu tana fadin" Malan, kar ka bari a wulakantani Malan, kar ka bi wannan munafukin abokin naka Malan, idan ka yarda ka bi shi kuka fita wallahi Malan sai na kashe kowa a gidan nan , Malan in ka bi shi asibitin nan sai na kashe kowa a gidan nan Malan!"

A tsorace aunty ta jimke hannayen yan matanta tana kallon Mama wace ta nufi wajen madafa ta warto wuka sharbebiya wace suke anfani da ita dan saran ice

A mugun tsorace du suka zarro ido......,

Aunty ta fara jan yara da nufin guduwa daki sai suka ga gadan gadan Mama ta biyo bayansu...........Kisan mummuke 38

Tabbas sun mugun Tsorata, sai dai cikin ikon Allah suka ga an dafe ta an murde an amshe wukar sannan ya ja ta kiiiiiiii soron kofa ya sakata a dakinsu ya rufe, domin ya sani a dakin nan ko almakashi babu bale wani abin.

Ihu take tana tsine masa albarka, ya rufe da kyau sannan ya dawo cikin gidan ya ja kujerar tayani tsegumi ya zauna ba tare da ya ce da su aunty komai ba ya sada kansa

Aunty na rungume da yaran nan sunna jiyo ihun maman yara har ya lafa ta ringa gunjin kuka ama ba wanda ya je inda take.........., haka kuma Sulaimana ya kasa ya tsare, shi kunyar mamansa ma ta ishe shi, ya gaza kwakwaran motsi, haka kuma tausayin yarinyar nan ya ishi zuciyarsa uwa uba kuma fitinar da ake ciki a gidan nasu tana mugun raunata masa zuciya

Tun suna tunanin zuwan su Malan, har karfe daya yayi, dare ya tsala sosai, du sunna filin gidan nan idannuwansu a soye, ba Malan ba alamunsa, haka kuma ba wanda ya kwanta a cikin su, mama da kanta bata iya rufe baki ba kamar haushin kare sai ta ɗan lafa da kukan sai ta fashe da wani har aka fara kiran sallar farko

Auntyn yara ta daga rinanun idannuwanta ta sauke a kan Sulaimana, a mugun raunane ta ce" Sule, ina su Malan ne? Kar dai aje wani abin ya faru da su???"

Shi da kansa saboda gadin gidan nan ya sa bai fita ba, Ama tuni zuciyarsa take raya masa ba lafiya ba

A tausashe ya ce" aunty, jira nake hasken rana ya fito sai ki fito ku yi jirana a kanti in nemo su, Ni ma na fara damuwa"

Aunty ta gyada kai, jikinta ba karfi sosai ta dubi yan matan ta, a tausashe ta ce" ku tashi ku yi wanka ki yi bruch sai mu yi sallah mu jira zuwan su Malan, ku daina kukan nan ku yi ta addu'a kun ji?"

Kai kawai suke gyadawa, wankan ma dan dai jikinsu ya saki ne ta ce su yi saboda kamar an likira musu duka haka suke tafiya a hankali

NUR ce ta janyo musu ruwa ta tara musu , ta mikawa A'isha sannan ta ja ta bar kofar bayin ta koma ta tsaya har ta yi ta gama sannan itama ta ja ta shige bayan ta cika mata buta

Da ta fito ma sai ta cikawa auntynsu ta mika mata sannan ta daura alwallar itama ta shige dakin su

Auntynsu da ta karaso kusan sulaimana ta ce" Ya dace ka bude ta ta yi sallah sule, lokacin sallah ya shigo, kai ma ka tashi ka yi alwallar"

Sai yanzu ya hada ido da auntynsu, wato ido cikin ido

A tausashe sosai ya ce" Zan yi, jira nake yi ku gama ku shiga daki sai in yi alwallar in yi sallar a nan, Ama ki yi hakuri, ba zan iya fito da ita yanzu ba, saboda idan har ta yi gigin taba daya a cikin ku, tabbas zan dau doka a hanuna.....zata yi ramuwa ne!"

Aunty ta zuba masa ido, magana ce yayi sak ba wani abin daba dabar nan, haka kuma maganar a ba wani alamun fita a hayaci, iya gaskiyarsa ya fito mata ya sanar mata......, sai kawai ta ji kamar ta maimaita masa tambayar shin yana son A'isha yace ko me? Sai kuma ta ji ta kasa, yaya za'a yi ta masa tambayar nan? Bayan amsar na fitar da ita a hayacinta?, haka kawai ta fadi a nan yaran cen su yi yaya????, sai kawai ta wuce bayin itama dan lokaci sai shigewa yake yi

A daki kuwa A'isha doguwar riga ta zurma Sannan ta haye tabamar da suke Sallah a kai ta kabbarta sallah

NUR kuwa rigarta da ta wuce gwuiwa ce kawai ta iya sakawa saboda wace ta kwana da ita a jikinta ta sa du ta kara rikicewa domin ta kamata, sai ta saka pant Sannan ta dauki katon hijab din auntynsu ta saka wanda yake baba ne sosai Ama kuma irin masu dan tona asirin abinda ke kasa ne, ta dai kabbarta Tata sallar ita ma

Bayan sun gama sallar hasken rana ya fara fitowa Sule ya dage labulen dakin ya duka ya ce" Barka da safiya Auntynmu"

Su duka ido suka zuba masa da mamakinsa....., sai kuma auntyn ta amsa tana harde kafafuwanta a hankali

A tausashe ya dubi NUR ya ce" HALLAH, amshi ki samo muku ko koko ne kafin in dawo, na sake rufe dakin cen kar wanda ya je koda kusa da shi ne dan ALLAH kun ji????"

Nur ta dube shi duban tsanaki, haka kawai ta ce" Kana nufin kar in je in bude maman da ka rufe tun JIYA? Ba'a juyo motsinta fa yanzu, idan fa wani abin ya same ta?"

Hum.....
, kawai ya furta Ya ajiye mata kudin ya wuce a ransa yana Ayyana' Yar kaniya wannan ai ba sai ina shaye shaye ba zata sa in yi zage zage, wai mama, banza ai du ita ta janyo mana masifar matar nan har nake son y'arta, Ni kam ai gwara a yi a gano ba ubana yayi cikin yarinyar nan ba ko an bani ita mu yi nesa da garin nan, in muka je cen wani wajen zan bata kula , zata dawo hayacinta, ama in tana ganin wannan fitinaniyar yar ta abanmu ko? Ta yiwu ma ta zigata ta ce ta yi me da Ni in ci mata uwa a garin nan!'

Manyan duwatsu ya jera a kofar dakin ya sake dane kofar kafin ya fice ya fantsama asibitin dabe, dan nan ne kawai zai fara zuwa saboda neman su Aban domin nan suka nufa ai......

A cikin gida kuwa auntyn yara na shafa kan A'isha dake saman cinyarta, Ama ba mai alamun zai nemi koda ruwa ya sha Bama a cikin su bale har su nemi abinci......, Nur kuwa tana jingine da jikin garu tana ta jan carbi , kirjinta ya mata nauyi sosai, hankalinta du a tashe, abu daya take son yi, shi ne kuka, Ama kuma ta kasa yi dan ta san idan ta sako su a gaba da kuka zata kara dagawa A'isha da auntynsu hankali ne kawai...., domin su duka sun ga kokarin A'isha kwarai da gaske, ba zata so ta hargitsata ba.
Chapter 64 · 0% Book details