← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 141

Sashe 128

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakatawa yayi ya bi bangarenta da kallo......., tana ciki da kannenta kamar yadda JAUHARA ta fada masa a dazu da zai taho wajen Anna bayan ta gaishe shi murya na mata rawa ta fada masa, yayi mata murmushi kawai bai ce mata komai ba domin da ta shi ta bi, da ta sirranta rikicin ta da shi, babu ma wanda zai ji, shi yasa sam baya nunawa kannenta komai, harta namijin baya ganin bacin rai a fuskarsa bale yan matan da yake daukansu tamkar yadda yake daukan FARHANA.

Juyawa yayi ya fice ya ja musu kofar ya saka imprunt dinsa sannan ya nufi wajen motar da Abdul Fatah ya sanar masa yana jiransa a ciki

Abdul Fatah din kadai ya samu a motar, ya bude ya shiga gefen sa yana duba baya ya ce" Ina sauran suke?"

Abdul Fatah ya yi murmushi ya ce" Ai sun yi tafiyarsu, Sulaimane yace shi fa ba zai yiwu ace ka masa rakiya ba mijin yarinyar nan ne kai fa......, shima MUTALAB yace da zai yiwu a raba tafiyarsa da ta manya, shine Abdul bassit yace mu je in kai su, shi ya raka ka, Ni kuma na kiya nace su je, ma je Ni da kai......, ga katin restaurant din da ya bada odern abinci naka, su na san sun je sun amshi nasu tuni"

Murmushi kawai yayi ya jingunu da kujerar , Abdul Fatah ya tashi motar a hankali ya shiga tuki cikin nutsuwa ya dauki hanyar restaurant din , domin sai sun amsa zasu wuce

A hanyar su, a tausashe yake kara ba IMAD hakuri kan halin da ya shiga a kwana biyun nan, domin kuwa ya fi kowa sanin waye amininsa, ya san cewa sosai yake cikin halin tashin hankalin zuciya.............., har suka iso get din gidan sa suka samu Abdul bassit da Aliyu a filin gidan sunna fira................Kisan mummuke page 80

Motarsu na tsayawa Aliyu ya karasa ya bude masa gefen da yake

A nutse ya fito yana mika masa hannu suka sake gaisawa, Aliyun na murmushi hadi da yi masa sannu da zuwa

Abdul bassit ya karaso yana dubansa daga sama har kasa kafin ya dubi Abdul Fatah dake rike da ledojin nan ya mika hannu ya ce" Bani in kama maka, mu je"

Dubansa IMAD yayi, kafin ya yi murmushi ya ce" Ku je ina?"

Abdul bassit ya Dube shi ya ce" Ciki mana, ko ba zamu raka ka ba?"

Murmushi Imad yayi, wato Abdul bassit gidan neman fitina....., to ai basa wannan al'adar a tsakaninsu, Ama dan neman su yi yake cewa zai raka shi

Bai hana shi ba har sai da suka zo daf da shiga falon ya mika masa ledojin yana murmushi ya ce" na zata zaka hana Ni shiga ai"

Murmushi IMAD yayi yana dubansa, kafin ya dubi Abdul Fatah, kuma ya dubi Aliyu dake bayansu

A nutse ya furta" Thank you broths........fr everything"

Da daidaya suke mika masa hannu suna gaisawa kafin Abdul bassit ya ce" Hpy mrg lf broth.....Please forgt evrythng that disturbs yr heart and be happy........injoy it....."

A tausashe ya ce" I wld lve to build a healthy life with her........ because I really love her..... I hpe she wl 2"

Abdul Fatah ya dan daki gefen hannunsa ya furta" in sha Allah zata fi kowa farin ciki da haka.....nd na san tana son ka ........., ka je.......kar ta yi ta jira"

Murmushi ya yi yana tsaye suka shige motocinsu suka tafi, ya rage Aliyu dake jiran fitowar wace aka bari ta zauna mata

juyawa ya yi ya nufi ciki a nutse

Matar dake zaune datijuwa ce, ita ta amsa salamarsa Sannan ta mike tana gaishe shi hadi da yi masa Salama ta fice

Kayan ya ajiye a falon, sannan ya je ya rufe baban kofar falon ya juyo a nutse yana bin ko'ina da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya ya nufi dakin da ya tabbatar a ciki take saboda karatun dake tashi a ciki

A nutse ya tura ya shiga saboda kofar ba a rufe take Bama

Fitila a kunne, hakan ya sa dakin barcin wadatuwa da haske ta ko'ina

A saman gadon ya hangota dukunkune cikin abin rufa, haka kuma ta kanta ya gane hatta hijabin da aka zunzumbula musu bata cire ba, kuma irin kwoncin da ta yi ya tabbatar masa bata yi barci ba , domin ya sha shiga dakin Inna ai ya sameta tana barcin, ya san yaya take kwonciyarta, wannan kwonciya ta nutsuwa ba ita bace......

Murmushi yayi, ya karasa bakin bed din a nutse ya zauna yana kai hannunsa wajen goshinta ya taba dan ya ji zafin jikin

Idannuwanta ta bude ta sauke a kan fuskarsa

A hankali ta kura masa ido kirjinta na bugawa

Kalamansa ne suka shiga dawowa kunnayenta hadi da sauka a cikin zuciyarta
Matse mata Wajen da yayi a dazu da kurewa lebenta ido ne ya fado mata cikin ranta

Da sauri ta zarro ido hadi ta jimke bakinta tamkar yanzu ne ya so nufar lebenta da manufar da ita ta fasarawa kanta

Kunya, mamakinsa suka sa ta risinar da dubanta a kansa kafin ta ja numfashi a ranta tana ayyana ' Ka min shigar sauri, ka min shigar karan tsaye, ka fado rayuwata bayan tsarina ba zan zauna da mai aure ba? ..........Ni zaka Duba, ka gigita ka fada min kalmar da ta fitar da Ni a hayacina Sannan ka je ka kwaci aurena?'

"HALLAH......, taso in ji jikin ki"
Ya furta a tausashe sosai yana sake kusanta fuskarsa da tata

Baya ta ɗan ja kadan hadi ta neman boye fuska

Kallon yannayinta yake yi kafin ya sauke ajiyar zuciya hadi da yin murmushi ya ce" To taso ki ci abinci"

Kai ta girgiza cen ciki ta ce" Na ci fa"

Da ba dan daf da ita yake bama, da ba lalle in zai ji abinda ta fada ba

Hannayensa ya saka ya yaye rufar Tata, hakan ya sa ta mike zaune da sauri tana dubansa hadi da fadin" Yaya, ka bani abin rufar sanyi nake ji"

Hannunsa ya sa ya riko nata yana dubanta a tausashe ya ce" Jikin ne? In kai ki asibiti ne?"

Nur ta girgiza kai a hankali tana duban hannunta cikin nasa kamar yau ya fara riko hannun nata cen kasa ta ce" Aa da sauki, sanyi dai nake ji"

Acn dake kunne ya duba, sai kuma yayi murmushi

A tausashe ya ce" A haka zaki iya yin barci ne? Ki cire hijabin nan sai ki kwonta"

Nur ta girgiza kai da sauri tana dan kankame jikinta

Gane abinda take nufi ya saka shi sakin hannunta hadi da mikewa a nutse ya fice daga dakin

Ajiyar zuciya ta sauke ta sauko a hankali ta ɗan leka

Hango shi ta yi ya nufi wani dakin, hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya ta koma saman gadon tana jin yadda hijabin ya takura mata

Ta dan jima a zaune, tana dari dari

Gannin shiru bai dawo ba sai ta cire hijabin tana sauke ajiyar zuciya da tunanin kawai ba zai dawo din bane , hakan ya sa ta saki jikin ta, bata jin yinwa , sai dan ciwon kai kadan, da kuma bakunta....., ama ta kasa cire doguwar rigar dake jikin ta, ta kwanta da ita tana ta addu'a hadi da sake duban dakin da tsoron girmansa.....sai dai a yau ta gwammace ta zauna a haka da ta je inda yake, haka kawai take jin tsoronsa a rants, gani take yi kamar kamar kamar.....yana iya neman ganin abinda babu wanda ke gani a duniya sai ita........cabdijan😓😌

Tun tana kallon hijab din da tunanin da ta ji motsinsa zata janyo, har ta daina dubawa......... harma jikinta ya fara abin saki da neman barci

Ya jima da fita, sai da ya kilace abincin nan , ya cenza sutura sannan ya zauna yana tunanin yadda zai bi ya shawo kanta ta saba da shi.......kafin ya mike ya sake kashe komai ya kuma nufar dakin ta a hankali ya shiga hadi da rufewa ya sake kashe fitilar dakin nata kafin ya nufi bed din.............

A nutse ya haye gadon, ..........a hankali ya saka hannunsa ya janyota jikinsa, wanda hakan ya sa ta bude idannuwanta a tsorace ta ce" Innalilahi, waye"

Murmushi yayi, a hankali ya ce" Waye zai zo nan banda ni ?"

Jikinta rawa ya kwasa, hakan ya sa a hankali ya sake rungumeta a jikinsa kasa kasa ya ce" Nur, ki nutsu, babu abinda zan yi miki a yau, ki saki jikinki mu yi barci ......., ai kin san in kwonta a inda kike halal ne tunda Ni mijinki ne ko?"

NUR dake dauke numfashi kamar ta yi tsere a hankali ta ce" Ama, Ni ai ban saba haka ba, ban saba kwonciya da , da, da namiji a waje daya ba, kuma kai da yayanmu ne ko? Ka taimaka ka sauka, ko Ni in sauke bargo ka ji yayanmu?"

A hankali ya girgiza kai, ya mayar da kanta da ta dago kirjinsa kasa kasa ya ce" idan ba dakinki na bari ba....babu abinda zai raba shinfidata da ke yayarmu......., kin san muryarki na sakawa in ji kamar in maki komai din ma......., ki kwonta mu yi barci....idan kuma firar kike so mu yi, Ni na fi son haka din ma"

Idannuwanta ta zarro, sai kuma ta yi mukuuusssssss cike da tsoron wannan yannayi da kuma tsoron abinda zai kuma fada idan tace ta masa gardama ko abinda zai kuma yi.............., sai dai rashin sabo da kwonciya irin wannan a jikin namiji ya sa ta ringa mutsu mutsu, shi kuwa yana jinta, du inda ta juya sai ta ji shi a jikinta, har barci barawo ya sure ta bayan ta sha fama da kyar

A hankali ya ja baya saboda irin yadda har jikinsa ke rawa rawa
Chapter 128 · 0% Book details