← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 141

Sashe 20

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe sosai ya ce" Waye yace maki mutanen nan yan yankan kai ne?, kin kuwa san su wanene su?, Shikenan ba za'a iya tara dukiya ba sai an yi mata fasara? Allah ne fa, yana iya malakawa bawa abinda ya fi wannan, ai an yi a zamanin su karuna ko?, haba NUR yannayinki kin yi kama da mai hankali, bai dace jita jita ta ringa shiga kwakwalwar ki ba, Fisabililahi a firar da kike nufin kin yi da Anna a shekarun da na dauka ina aiki gidan su ban taba yin doguwar fira irin haka fa ita ba....., tabbas irin yadda kika kama zuciyata farat daya dama na san ke din nan y'ar baiwa ce........., Ama in tambayeki a kaf firar da kika yi da ita har kuka gama kin ga alamun cutarwa a tare da ita? Kin ji a jikinki zata iya cutar da ke?"

Imtee ta sada kanta, wani gefe na zuciyarta na ce mata yaya za'a yi ya kasa kare iyayen gidansa to? Wani sashi na zuciyarta kuwa na tuno mata irin nutsuwar da ta shiga na dan lokacin da ta yi fira da matar nan, a lokacin da ta fara koya mata karatu kuwa sai ta ji kamar da yaran Hausa kadai take yi mata bayani irin yadda ta bata lokaci, ta bi ta a hankali, ta yi mata koyarwa mafi sauƙin da kanta zai iya dauka......., a gaskiya idan tace ta ji kanta a hatsari a katon gardin din nan daga ita sai matar nan ta yi karya, dan haka a sanyaye ta girgiza kanta

Murmushi ya yi ya ce" To kin ga, sauka zaki yi ki koma ki amso littatafan sannan ki bata hakuri, matar nan idan har ta yarda da mutum in sha Allah ba zata cutar da shi ba, a lokacin da na je gidan su neman aiki zuwana ya fi a irga, ban taba samun dama ba sai ranar da Allah ya sa ta dawo daga anguwa , ita ta sa aka saurareni , tana jin bukatana ta tambayeni karatun da na yi, Ni na sanar mata bakina secondry, aiki nake nema da zan taimaki iyayena, shine tace na iya mota? Na nuna ban taba jan mota ba, nan ta ce in hada takarduna in kai baban makarantar koyar da mota idan na je in ce SIR IMAD ya ce in zo, tun daga lokacin sai da aka koya min tukin mota karama da baba, Bus da ta kwasar kasa......, ya zamo babu motar da ba zan iya ja ba, ina fitowa suka dauke Ni aiki da albashin da na zarce manyan ma'aikata............"

Imtee kallon sa take yi kawai, sosai ya dage yana sanar mata alkhairan ahalin da ta girma da tsoron su da jin akasin abinda yake fada a bakin yan anguwa.....
To ko gidajen da suke siyewa cewa aka yi fa zuwarwa mutane suke da bindiga su baka zabi ranka ko gidan ka, a dole ka siyar musu gidan ka tafi ka bar musu filin....... Su ne kaɗai suka gagare su, ehe!

Ajiyar zuciya kawai ta sauke a lokacin da ya gama ya sake fuskantar ta a tausashe ya ce" Ba zata cutar da ke ba, taimaka maki zata yi, ba zan so su dakatar da ke daga zuwa makarantar nan ba, ki tausayawa iyayenki irin kudin da suke zuba Miki, ki yi kokari ki jajirce ki zamo cikin zakarun da gobe zaki samu damar tafiya musabaka har Saudiya, ke ba zaki fi kowa jin dadin ace kin tafi da mamanki da babanki Saudiya ba? Baki da burin kai su dakin Allah ne????"

Da sauri ta zuba masa ido, a tausashe ta ce" Zan iya kai baban mu dakin Allah da maman yara????, Ni????"

Kai ya gyada mata cike da gamsarwa ya ce" Kwarai kuwa, idan kika dage da karatun nan har kika samu kika zama zakwakiya a cikin sauran, tabbas za'a ba iyayenki kujerar maka , wace zasu maki rakiya har su yi ibada kafin ku dawo cikin aminci a karkashin kulawar makarantar nan....."

A saman lebenta ta furta" Ya Allah ....., yaya ka ga maman yara a Saudiya, ace Ni ce na kai ta.....???"

Sam bai iya jin me tace ba, sai sake cewa ya yi" Kin yarda zaki koma????"

A hankali ta gyada kanta, sannan kasa kasa ta ce" Ama ba yau ba, sai gobe idan na dawo in sha Allah "

Kai ya gyada yana murmushi ya ce" Madallah, ya batun soyayyar mu????"

Sai da ta zarro ido tana dubansa kafin ta dauke kanta ...., dan ita abin har kunya yake bata, wai ashe zata girma itama ta fara soyayya? Cabdijan

Juyawa yayi baya ya dauko ledar da ya zo mata da ita ya bude ya ciro waya kirar Samsung ya miko mata yana fadin" Wai Fa'iza ke batun baki da waya, shine na je na siyo maki ita yau harda layi da komai na saka maki, duba ki gani????"

Da dan tsoro take duban wayar, a hankali ta miko masa ta ce" Yaya zan yi da waya Ni? Ta yaya zan iya rike waya a gidan mu? A'a ai da ba'a bamu ba har yanzu babanmu ne yace sai mun girma"

Murmushi yayi yana kallon kwayar idannuwanta ya ce" Girma? Bayan wannan? Ai kin gama girma baby, kuma wayar nan da kika gani kina iya amfani da ita har ta tsufa in sake maki sabuwa ba tare da an sani ba a gidan ku, duba fa ki gani irin yadda yan mata ke fantsamawa da waya, kin ga fa sai da na lodo maki film ne, wakokin soyayya ne da sauransu, dubi ki gani....."

Ya kuwa ringa nuno mata abubuwan da sai dai su dauki rediyon maman yara su buya su saurara, Bama kamar yan wakokin nan na soyayya ....gasu ƙarara a gabanta tana kallo

A tausashe ya ce" Ki yi hakuri ki amsa, zan so in riinga kiran ki da dare muna firar soyayya kin ji? Please dear......."

Kasa cewa komai ta yi sai sada dubanta, dan kuwa zuciyarta ta kasu kashi kashi da tunani daban daban......., kamar ta amsa kamar idan ta yi haka ta ci amanar mahaifinta ne?????????, to Ama ai mamanta ta sanar mata ba wani laifi a haka ko? Sai ma da ya ciro kudade ya saka a ledar ya hade ya daure mata ya ce" Wannan kuwa ki sha ice cream kafin ki bani dama na zo zance sai in zo maki da shi mai yawa.....shin kin taba shan ice cream kuwa???????"

Gaba daya zuciyar Imtee sai ta ringa kasuwa kashi kashi......, karshe ma sai ta kasa yankewa kanta hukuncin abinda ya dace sai shine ya yanke mata ta hanyar daukan hanyar gidansu da ita, ya sauke ta daf da gidan sannan ya mata Salama ta shige gidan da sakon ta jikin ta na rawa

Kicibus ta yi sakamakon ganin auntyn yara na shanya a filin gidan, kuma tsayuwar motar ta sa ta dan dakata dan tunanin waye zai zo nan a mota kuwa?, hakan ya sa ta dan zubawa kofar ido tana kallo, har Imtee ta shigo bata daina kallon kofar ba da jiran jin an shigo, sai da motar ta tashi ta yi gaba sannan ta dawo da dubanta kan imteen da tunanin ko kawai wani ne ya zo wucewa ya dan bi ta kusan gidan nasu, bata taɓa kawowa kanta cewar IMTEE zata iya shiga motar saurayi ba harma a kawota kofar gidan su ba, sai dai tsayawar da ta yi jikinta na nunin alamun rashin gaskiya, da abinda ke hannunta, da kuma gannin ita daya ce ya sa itama zuba mata ido tana son ganin shigowar A'isha, da kuma jin IMTEE ta mata Salama irin na yaya masu tarbiyya idan sun zo gidajen su, dan takan yi Salamar, tana yin Salama sosai, Ama yanzu sai bata yi ba......ko menene dalili........???????????????????

A tausashe ta budi baki ta ce..........💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Yawan tallah ya fi yawan roko sister, ki tsaya da kafafuwanki dan wuce gori...... Bismillah

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data
*11*

A tausashe ta budi baki ta ce" NUR, lafiya kuwa???"

IMTEE ta ɗan sauke numfashi, a hankali zata yi magana Maman yara ta fito daga bayi da buta da sauri ta suri hannun IMTEE ta ja ta suka yi dakinta da ita tana sakin tsaki kasa kasa ta ce" Ke kuwa meye zaki tsaya gaban yan saka ido kina wani abu kamar wace ke cikin wani hali? Lafiya? Me yake damun ki ne??"

Da sauri IMTEE ta yi kurya tana dafe kirjinta, a tsorace ta mikowa maman yara ledar nan jikinta na rawa ta ce" Anas ne ya kawo Ni a mota, kin ga abinda ya bani, shine da na shigo na hade da auntynmu, innalilahi idan ta ga ko menene kashe ni zata yi a gidan nan"

Maman yara na bude ledar itama jikinta ya dauki rawa......
Sai dai ita ba na tsoro bane, na tarin zalamar ganin kudi matattun marara
Chapter 20 · 0% Book details