Sashe 125
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamansa dake kulkule a filin gida ce ta Dube shi da yanayin tashin hankali ta mike tana nufar sa ta ce" Anas? Lafiya? Subahanalah me yake faruwa?"
A gigice ya daga mata hannu, gaba daya ya mayar da girman da darajar bata gefe idannuwansa na fitar da hawaye ya fashe da kuka yana fadin" shiKenan, shiKenan kin raba Ni da ita, shiKenan ta min nisa, shiKenan ba zan taba samun ta ba, wayo Allahna shiKenan kin min sanadiyyar rasa ta, sai da na fada maki ina sonta ko yaya take, na sha fada maki mutun ce mai daraja, mama na sha fada maki ki bari in malaketa, ama kika dage , kike wulakantata da iyayenta, mama shiKenan kin raba Ni da ita!"
Mahaifiyarsa da gabanta ke ta faduwa tana dubansa ta ce" Na shiga uku, wace masifar ce wannan kuma? Maganar yarinyar nan ne kuma? Ni kam na hadu da jarabawa mai zafin gaske Ni da mai kayan miya da mamanta sai Allah ya isa........, wai ba nace zaka aureta ba Ama idan ka auri A'isha?"
Kukansa ya fitar da Fa'iza a tsorace ta nufo su tana tambayar lafiya
Mahaifiyarsu da ta fara share kwallah ce ta ce" Ina fa lafiya yaron nan da mayiya ya hadu, ya lashe masa kurwa, yarinyar nan ta gama da Yarona, to kuwa ina kan bakana du masifarta sai dai ta zo a ta biyu in A'isha ta yarda!"
Wani kukan ya fashe da shi yana dubanta ya ce" Mama kenan, ki kwontar da hankalinki, in dai NUR ce a yanzu ko mutuwa mijinta yayi da wahala ta aure ni, domin ta min nisan da ba zan kamota ba, Mama an daurawa Nur aure da ogana yanzu yanzu, Mama an daura auren Nur dina da sir IMAD yanzun nan.......sai ki yi hakuri da zaginta hakanan ta bar miki danki, sai dai ina mai tabbatar maki mutuwa zan yi, mama duniyar zan bar maki Ni ma, idan ya so shiKenan sai hankalinki ya kwonta........."
Ya karashe yana kwontawa a nan cikin kasa yana sake saka wani kukan
A gaskiya du gigicewa ta yi, domin sam bata gane Hausar sa ba, hakan ya sa da karfi ta duka tana girgiza shi ta ce"Kisan mummuke page 79
A rikice ta rike hannayensa ta ce" Kana cikin hayacinka kuwa? Kana jin abinda kake fada kuwa?, wani irin an daura auren sir IMAD da yarinyar nan yar gawurtacen talaka, marar ilimi? Ke Fa'iza , ba ke ce kika ce min yarinyar nan tana da matsalar ɗaukan karatu ba?, wace irin masifa ce wannan? Wai me kuka gani a tare da yarinyar nan?, na tabbata idan kai ka rikice saboda jikinta ne, shi fa? Ai kuwa tunanina ya tabbata, asiri suke yiwa ya'yan mutane, aure? Du yan matan garin nan ya rasa ta aura sai wannan? Baya cikin hayacinsa!"
Anas cikin kuka ya janye hannayensa ya mike da kyar ya nufi ciki
Da sauri ta bi bayansa rai bace ta ce" Wai me kake yi haka? Dakin ka zaka je ka kwonta dan an raba ka da alkakai?, to ai gwara haka ma, idan ya so lokacin da zai dawo hayacinsa ya daure iyayenta da ita baki daya, kai kuwa sai a aura maka aishanka dan na tabbata du Wanda ya samu A'isha shi ma karamin mai kudi sunansa!"
Girgiza kai kawai yayi, ya karasa wajen gadonsa ya zube
Bata hakura ba ta kara shiga tana fadin" Ka tashi ka je ka yi wanka ka koma bakin aikin ka, babu abinda zai faru sai alkhairi....., ka yi tafiyarka ka kwonta ka huta.....aikin banza ina nan da kai zaka dawo ne ka fada min cewar asiri ya tonu suna hannun hukuma, ai dama da wahala kai a cin maka saboda ban zauna ba, bana yarda, babu wani ƙaramin shegen da zai cin maka in dai ina raye!"
A gajiye ya dubeta ya ce" Mama, ki yi hakuri ki fita, saboda zuciyata na iya tsayawa da aiki a yanzu idan na ci gaba da jin kalaman zagin da kike yi mata, bayan ke uwata ce bani da wani abinda zan iya yi maki dan in rama ko in hana ki, ki je mama ki zageta son ranki, shi ne kawai abinda zaki iya yi a yanzu.....dan kuwa a fili hakan ba zai faru ba, sai dai ki boye ki yi........."
Ya rike kai yana tarin wahala ya ce" Ba zaki gane ba, ba zaki taba yarda cewar auren soyayya yayi ba sai da ya nuna min ƙarara cewar ya fi ni sonta ta hanyar kara nisanta ni da ita......
, kin ga, ya aureta kuma ya saka katangar karfe tsakanina da gidan sa ma ba wai ita ba....., sannan A'ishan da kike magana ƴaƴanta ya aureta, Mama na yi biyu babu fa, na yi ba wan ba kanin duka saboda halayarki ta tsanar talaka da talauci........, ki yi hakuri ki tafi mama, aikin kuma daga yau na ajiye, zan zo in buga tebur a kofar gidan nan in kama sana'a.....ina mai tabbatar maki na kare aikin nan, sai ke ma ki fara yan sare saren kayan miya, ta yiwu na abinci ba zai gagaremu ba in muna siyar da kayan miyar!"
Daga haka ya ciciba ya mike ya nufi bayi , ya barta tsaye kamar wace ta suma hannayanta saman kai , baki bude
A rikice ta saka ihun tashin hankali hannayanta saman kai ta rike Fa'iza dake riketa tana fadin" Na shiga uku Fa'i, na shiga uku, abinda nake gudu ne zai same Ni? Ina gudun ya aureta ya zamo d'ana ya fi karfina, gashi yanzu uban gidansa ya aureta ta yadda ga d'an nawa ama komai zai fi karfina gaban nan? Fa'iza uban gidansa ta aura? Hakan na nufin Malan Ahmadu mai kayan miya ya zama sirikin wannan mutumen? Fa'iza kin kuwa san hakan na nufin gabanan sai dai su bamu ba dai mu basu ba? Fa'iza hakan na nufin ita ce uwar gidan d'ana? Lalle wasu sun nema sun samu Fa'iza, ni kuwa an cin min ina zaune , shikenan yan bakin ciki zasu min dariya Fa'iza, Shikenan shiga taro sai ya gagareni Fa'iza, shikenan karyata ta kare Fa'iza???"
Fa'iza dake share hawaye a raunane ta ce" Mama dan Allah mu je ki zauna, ki yi hakuri ki bar kukan nan, ki fuskanci yaya ki gane halin da yake ciki, ki ajiye maganar kudi da maganar NUR gefe ki fuskanci yaya, Mama da gaske yana cikin wani hali mai wuyar fasara, ki yarda ya so ta da gaske da zuciya daya, kuma ki gane dalilin abinda kika RINGA yi da kuma rabo ya sa bai sameta ba, Mama ki rarashe shi, saboda ina tsoron aje mu rasa shi, ban taba ganinsa yana kuka wiwi saboda komai ba, ki dube shi, kar ki rasa d'anki saboda wasu dalilain da basu da anfani dan Allah Mama "
Dif ta yi da kukan nata, tana kallon Fa'iza ta ce" In rasa shi? Saboda mace zai iya mutuwa?"
Fa'iza ta ce" Ba lalle sai mutuwa bane rasa shi, idan har yadda muke tunani ta kai a zuciyarsa ta wuce nan Mama kin san yana iya zama wani iri, yau ko fara'arsa ya rasa ai an shiga hakinsa ko? Dan Allah ki yi nadama, ki ajiye maganar ta zama matar mai gidan sa, ki yi mata murna da fatan alkhairi, ko Allah zai sanyaya masa shi ma, ko mu ma Allah zai sa mu dace, Ama idan kika ce zaki zauna a yanzu ma da Allah ya nuna maki shi ne ya isa ya maida mai kudi talaka, talaka kuma mai kuɗi kika ci gaba da wasu abubuwan zai sake nuna maki ba kudi bane jin dadin duniya, komai na iya faruwa, zai nuna maki ki ga walwalarmu kadai ya isa ya saka maki nutsuwa duniya da kiyama, dan Allah ki yi hakuri ki rarashe shi, kuma ki yi ta astagfari, Nur kam da iyayenta iyayen gidan mu ne, haka Allah ya hukunta"
Gaba daya sai ta rasa bakin magana, du irin yadda kirjinta ya cinkushe haka take kallon Fa'iza, har sai da kakarin amansa ya sa gabanta faduwa ta mike da gudu ta nufi dakin nasa ..........
A gidan su Anna, basu samu kansu ba sai da aka fito daga sallar isha'i.......,
A nan ne iyayen maza, da mata da ya'yan suka hadu a falon Anna bayan taron ya watse sai su ya su, ya zamo an hade, baki daya, Inna na zaune cikin fara'a mai girman gaske du ana sauraronta saboda bayanin da take yi mai mahimmanci ne sosai
Jawabi ta fara yi, kafin ta ɗora da nasiha, ta karashe da fada sosai irin na iyaye, tsofaffi, masu tsare gaskiya da fadinta a kowani yannayi, masu kokarin saka ya'ya a hanya a kowani lokaci
Da kula sosai ta ce" Zuwa yanzu kowane zai dauki matarsa ya tafi gidansa da ita, maganar kayan lefe babanku SAWIRIS yace a bari iyayenku su iso, suna tafe da duk shirgin da ya shafi lefen na amaren harda mazan........, Allah ya baku zaman lafiya, ya kade duk wata fitina ya hade kawunanku baki daya"
Anna dake kallon kasa tunda ta ji bayanan Inna na karshe ta dago tana kallon Innan har ta dasa Aya, kafin a hankali ta ce" Inna, tarewa kuma? A yau? , na zata sai ko nan da sati Daya haka mun gama shiryawa, mun gama shirya amaren, sannan an shirya musu gidajen nasu, an musu dinkunansu da komai sannan su tare?"