Sashe 53
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A'isha ta yi murmushi ta mike ta ce" Nur kenan, Ni ai ban hargitse maki komai ba, abinda yake zahiri da baki cika son buda ido ki gani bane nake bude maki ido, domin zan so ki kara karantar matar da ta fi kowa iko da ke a duniya cewar ta fi kowa son ki da alkhairi , ki kuma sake koyon rayuwa, domin Ni nan da kika gani na jima da ɗaukan darusan auntynmu......, wannan susar kan da kike yi wallahi ki kunce kan nan a wanke mu je wajen kitso, na tabbata gashinki ya gama hadewa Nur........, kin ga tashi zubo kayan aunty mu gyara idan da masu dati mu wanke mata....... In yaso daga baya sai in taya ki kunce kan"
Nur ta juya ta nufi wajen da kayan auntynsu suke, sai ta ga kayan ninkaku daban, haka masu datin a cikin wani buhu haka a killace
Ta janyo buhun ne auntynsu ta shigo dakin
Dubansu ta yi ta ce" Me zaki yi da wannan, kayan datina da na mahaifinku ban riga na wanke bane, sai rigar Sulaiman biyu"
NUR ta ce" Wankewa ne zamu yi ai aunty"
A'isha ta dubi aunty ta ce" Auntynmu wai ina yayanmu ne? Ni wallahi sai yanzu nake gane na jima fa ban ganshi ba"
Dariya aunty ta yi, ta ce" Ya yi yar tafiya ne, kin ga ajiye wankin nan Anas ne fa fa abokinsa suka zo, suna wajen malan shi ne yace in maki magana ki gaisa su wuce"
Nur sai da ta zarro ido tana ajiye buhun ba tare da ta shirya fitar maganar ba ta ce" Yau ga jaraba, Anas kuma?"
Aunty ta zuba mata ido da kallon da ya sa ta mike ta karasa ta dauki hijab din auntyn a saman abin karfn gadonta ta zurma ta fice tana ji ina ma ta samu dama ta dudura masa ashar ko ta huce itama??????
Aunty ta dubi A'isha dake mata dariya a tausashe ta ce" A'isha, kin ga sai fa kun cenza min salon nan naku, yaya za'a yi ace wai ana magana da mutun ta fice a haka? Kin ga da gaske ta tafi, bata nemi turare ba bale kwali, kin ga, Ni tsohuwa bana rabo da kayan kwaliya, ledar cen cike take da kayan kwaliyana......gaskiya gabanan ko makaranta zaku je ba zan yarda ba sai an yi wankan kirki, an shafa mai da kwali da dan lips......, Ni har mamaki kuke bani , dai-dai shekarun nan naku ai sai yadda hali ya bada, kwaliya ce, tsafta ce, saka kaya ne....., hum tashi je ciro min kayanku mu wanke mu goge makarantar nan ta gobe in sha Allah sai kun min shiri mai kyau haba dan Allah "
Mikewa A'isha ta yi tana yar dariya ta nufi dakin mama dan ta dauko kayan, duda da ta shiga kame bakinta ta yi da sanda ta wuce ciki saboda mama ta ringesa ta kafa rediyo a kunnenta kamar rainon kurma tana jin labarun yama...............
Kayan nasu ta kwaso a hankali ta fice, dan hankalin mama ba a kan kofa ba ko kadan bata kula da an shigo an fita ɓa
NUR kuwa yau ma daga boye ta rage tsayinta ta gaishe da su, Anas kuwa sai murmushi yake dan wallahi ya zata ba zata fito ba saboda jiya ai kora shi ta yi........., shi kuwa ya fada mata yanzu ya fara zuwa in tana so ta yanka shi ta huta!
Kwarai ya so yi mata alkhairi yau ma, ama yana tsoro, haka suka wuce shi da abokinsa zuciyarsa na samun Salama , daga nan ma ya wuce ya ajiye abokin nasa sannan ya wuce gidan Anna, saboda har yanzu ogansa bai fara fita bane ya sa yake dan yawonsa, dan hutawa yake yi sosai ko shi da Anna da dare suke haduwa su yi fira ......Ama a yadda anna tace gobe zasu koma bakin aiki , shima goben zai fita in sha Allah, haka kuma a goben ne zai gane dalilin zuwan wannan bakon da iyalinsa, wato HAIDAR, domin har mamansa ya fadawa shi fa bai san me ake nufi ba, ita kuwa ta masa alkawarin in sha Allah babu wanda zai shiga gurbin sa a wajen ogansa ya ma kwontar da hankalinsa sosai da sosai in dai tana raye sai dai zumunci ya kara dankuwa shi da ogansa.................
Da NUR ta dawo, wannan wanki da auntynsu ta saka su yi ya mantar da su maganar kunce kai, sai kawai suka shiga aikinsu , bayan sun gama ma har dare ya shigo sallah kawai suka yi suka ci abinci suka kwonta,
MALAN kuwa dama a gidan ya idasa wuninsa, auntyn yara ya zamo ta leka shi ya dawo haka ta ringa yi, har sai da yace mata ta fa kwontar da hankalinta jikinsa da sauki sosai, shi kam anya ba kiran Malan zai yi ba? Wannan shiru ya yi masa yawa, har yanzu bai zo din ba, kuma bai yi kiransa da batun SULAIMANA ba, sai da auntyn yara ta yi dariya tace ita dai ba ruwanta , yanzu sai ya yi kiran Malan a kan maganar sulaimana?, ita kam ba da ita ba idan yi zai yi sai ta gudu dakinta su yi su gama.....,shima a dole ya bar maganar a ransa yana dariya, har ga Allah kullum sai ya duba hanya, Ama shiru kake ji, kar dai Malan ya kwace masa Sulaimana? Bai taba tunanin zai yi kewar sulaimana har haka ba sai yanzu da baya kusa.......rayuwa kenan ko yaya mutun yake yana da dadi sosai , da baya nan gwara yana kusa.
Washe gari da sasafe kuma auntyn ta farka ta haɗa gawayi a dutsin guga domin tana fadawa malan basu da gawayi shi ya je da kansa ya siyo musu, ta fara gugar kayan nasu , ko da suka farka sai suka shiga kama mata,
Da ta yi maganar makaranta ma sai A'isha tace yau malamin Kur'ani ne gare su da safe, shi kuwa yanzu baya yi da safen sai bayan an fito da su daga hutun breakfast yake shiga , dan haka bari kawai su gama sai su tafi....hakan ya sa suka ci gaba da aikin, mama kuwa dama da safe ta fita , su dai basu san ina ta je ba, Malan kuwa ta fada masa tana da fatihar daurin aure............
(Wannan kenan)
32
Gidan ANNA
A gidan su Anna, kwana hudu kenan da zuwan su IMAD, ama har yanzu bai nunawa MAZNA cewa ita mace ce, mai dauke da jiga jigan abubuwan da ta san cewa tabasss idan ta malake su ta gama samun mijinta a duniya, a kiyama kuwa da yardar Allah sai dai ta jagoranci matansa a aljanna....., sai dai wani ikon Allah tsoron da ya kamata da irin yadda take ta fama da saka audugar mata tana cirewa dan koda zai nemi wani abu ya musu katanga da shi, sai ta ga sam hankalinsa bai kai nan ba, wanda hakan kuma sai ya dawo yana neman daga mata hankali, saboda ita dai ta san waye mijinta a lamarin nan, gajiya, ko baki basa hana shi kebewa da ita....., tsoro da firgici suka shige zuciyarta da tunanin me yake faruwa ne? Shin wata yayi ko kuma ita din ce ta fita daga zuciyarsa........., cikin ikon Allah a daren yau ma da ya shigo daga wajen Anna bayan yayi wanka ya shige dakin sa na barci da ta zo inda yake ta shige jikinsa sai kawai ya dan shafa bayanta cikin rada ya furta " good nice bb........." Ya karashe da matsa bayanta wanda abin ke yi kamar ruwa ne aka zuba a balan balan
A hankali ta ɗan sake shigewa jikinsa murya cen ciki ta furta" me yake damun mijina ne?????,"
Shanyayun idannuwansa masu ɗauke da mugun bukata irin na kasantuwa da iyalansa ya bude ya sauke a kan fuskar ta...............
Sosai yake mamakin irin yadda du irin jimawar da suka yi da junna bata gane yarensa ba tare da ya fito ya fada ba yake........
Yaya za'a yi ya iya sakin jiki da ita bayan tunda ya dawo bai gane kalar fuskarta da gaskiyar dake fitowa daga bakinta ko karya ba???
Ko waya zata yi sai ta boye, da ta ganshi kuwa har dan zabura take ta ɗan ringa boye kanta wanda sam ba irin haka a tsakaninsa da ita a rayuwa.........
Rabonsa da ya ga ta je bangaren Anna kuwa tun ranar da aka yi abin nan, shi zata nunawa lokacin da take zuwa yana barci???????
Maganar Inna kuwa ta kara sakawa sai dai in bai samu damar yi mata kallon kwafffff ba....., kwarai yana so ya ga abinda take nufi da shi koda zai iya sakin karinsa............
Bai ce mata komai ba, sai sake duban kirjinta da yayi ....., a hankali makwaloton wuyansa yayi dan sama da kasa alamun hadiyar yawu da mugun bukatar saka koda kwara daya ne a bakinsa................
Idannuwansa suka sake mutuwa da abinda ke dauke da zuciyarsa .....a hankali ya ja bargo ya rufa mata cen kasa ya furta" Na gaji......., wunin ranar gobe kuwa Ni da kaina ban san adadin aikin dake gabana ba....lts sleep plz"
Daga haka ya juya yana kai hannunsa wajen hancinsa a hankali ya ringa dan murzawa dan hatta numfashinsa sai yake jin zai iya katsewa saboda halin da yake ciki, shi kuwa ya rantse ba zai biyewa gangar jiki ba har sai zuciyarsa ta samu nutsuwa da abin kafin hakan ya faru!
Washe gari da karfe tara na safe