Sashe 140
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nutse suka so isawa, sai Muryar maman su Fa'iza, da Fa'iza , harma da ta Anas suka katse musu hanzari, wanda a dole suka dakata da kula suka shiga gaisar da maman su Anas din, har ma da shi din dan kuwa ko ba komai ai yaya yake a wajen Fa'iza kawarsu
Nur ta yi murmushi a lokacin da maman su Anas ke kara gaisheta tana faman fadin " Hajiya sannu da gajiya, Allah ya raba lafiya, ai mun jima a nan din tunda akace mu zo mu jirayeki.........., gamu mun dake zuwa, Allah ya baku hakuri ya huci zuciyarki, a kuma ba ogan hakuri dan Allah a sanar masa idan har zai samu ko wane ne aikin a bashi dan Allah, wallahi komai ya tsaya mana, yaron nan bai iya adano ba, sam bai san zafin hakan ba, ya shiga halin kaka naka yi ba komai a hannu, har gidan da aka bashi ya so sakawa a kasuwa, shine nace mu dawo din dai ko Allah zai sa a dace....dan Allah a yi hakuri da dukan abinda ya faru, a yafe mana"
NUR a tausashe ta ce" Mama ki manta da komai, haka Allah ya hukunta, mu karasa ciki kar mu tsaya a nan saboda waje ne, mu je , in sha Allah zai ganshi yau, kuma komai zai wuce..."
Gaba suka fara yiwuwa, ya zamo su kuma a bayansu suna biye da su, sai dai tunda suka shigo get din suka hango shi tsaye a gefen bangaren Anna, idannuwansa a kan su, da duban da ya saka su kallon junna, kasa kasa Farhana ta ce" me yake faruwa? Kamar ransa a bace?"
Nur ta ɗan dakata saboda murdawa da cikinta yayi, sai kuma ta ɗan daga kafar ta sake bin bayansu a hankali, hadi da dan waigawa ta sake duban get din, tana ganin cewar get din ba rufafen nan bane, kwarai ana iya ganin na waje domin idan dare yayi ne ake janyo kantamemen mai rufewa ruf, warhaka kuwa an bar iya karafunan nan ne,
A hankali ta ce" Ran ya'yan FARHANA a bace yake, kuma ba komai bane hango mu da yayi da ANAS ne, A'isha anya ba bangarena zamu nufa ba kuwa, yana da karfin gani Masha Allah, na tabbata ya gane su waye a bayan mu, ba zan so ya yi fada a gabansu ba, ba zan so in kara cakula abin ba, bayan taimako ne zamu yi, daga wannan ba wani abu da ace yayan FARHANA zai yarda"
A'isha ma sai ta ji kamar hankalinta zai tashi, a tausashe ta ce" Idan muka yi bangaren ki, bin mu zasu yi, mu je kawai, tawakaltu Allalah"
Ci gaba suka yi da nufarsa, har sai da suka zo daf da inda zasu hau su same shi sai ya juya ya nufi cikin falon Anna
Kasa hakura ta yi, ta hayewa da sauri ta bi bayansa tana fadin" Ya'yan FARHANA, ya'yan FARHANA...
Andadi"
Suna shiga falon na Anna ya juyo yana duban ta ransa bace ya ce" Ki yi shiru da kiran sunana, nace ki kyale Ni!"
Sai kuma ya juya da nufin zagayeta ya fita
"ANDADI, zo nan, taho nan!" Anna ta fada bayan ta mike tsaye, saboda du sunna falon harda Jauhara da ake shirye shiryen bikinta da MAZNA da Mama
A dole ya dakata ya juyo kirjinsa na wani irin tafasa
A rikice Nur ta karasa ta ce" Anna, wai su Anas ne suka zo da mahaifiyarsa suna son bashi hakuri dan ya koma bakin aikinsa, shi ne nace mu je yana ciki, daga wannan babu abinda ya haɗa Ni da Anas, shine na ga ransa kamar a bace, Yayanmu babu abinda ya haɗa Ni da shi, kawai rakiya na masa wajenka dan ya baka hakuri ya koma bakin aikinsa, dan Allah ka yi hakuri"
Da karfi ya ce " Nace ya bata min rai ne?, ko nace na Kore shi ne?, karya yake yi da gangan zai sake biyo ki gidan nan, so yake yi lalle yayi maki aiki, bayan ba ta yadda za'a yi in bari ya rabi inda kike, Nur a kan me zai tsaya yayi maki magana, bai san inda zai sameni bane? Ko dan kawai ki daga min hankali zaki tsaya kina magana da shi?"
Wani irin takaici ya turnuke Nur, tana dubansa da mamakinsa ta ja numfashi saboda ciwon da take fama da shi tunda ta shiga wata na bakwai ne ya murda mata, wato nakudar tsaye, hakan ya sa ta rintse idannuwa hadi da sakin hawayenta suka zuba masu tafe da takaicin lamarinsa da tunanin kenan bai yarda Bama da ita ta budi baki tana shashekar kuka bayan Mama ta kamo hannayen ta tana dubansa ta ce" Kenan zargina ma kake yi?"
MAZNA dake dukansu a hankali ta ce" Kar ki yi tunanin yana zargin ki Nur, ko daya, baya zargin ki, yana kishin ki ne, wanda sonki ya janyo haka, kuma har abada ba zai taba yarda ya ga ko menene ya haɗa ki da ANAS ba, ki yi hakuri......"
Ta kai dubanta kan Anna dake yiwa IMAD fadan a kan me zai rinka yin haka, idan ya bari suka zo ya sauraresu ya ce ya yafe ya koma bakin aikinsa ba shikenan ba, ai ba ita ta janyo shi su yi magana ba, ba kuma wata maganar zasu yi marar kyau ba ko???"
Nur ta sauke ajiyar zuciya, sosai bayanta ya rike da mararta, haka kuma irin juyin da aka mata kwanaki ne ake yi mata a yanzu, wanda ya sa kanta ke kasa, ta rike hijabin Mama da karfi , idannuwanta rintse jikinta na daukan rawa hadi da gumi....wanda ya sa Mama dubanta da sauri ta ce" Nur, menene? Lafiya? Nur"
Numfashinta ke fita da sauri sauri, sai ta dafa Mama ta mike a hankali ta ce" Zan je bangarena Mama, ba komai......"
A hankali ta juya da nufin tafiya sai kawai facal ruwa ya bale mata wanda ke nunin da fashewar fawa
Hijabin nata ta daga tana duban ruwan, wanda ya sa Mama mikewa da karfi tana fadin" Innalilahi, mu gani? Ina yake maki ciwo? Me kike ji?.......da yau ta kai wata takwas da sati uku ko???????, Anna "
Ai Anna sai ta nemi rikicewar itama, uwa uba IMAD da ya nufo Nur din yana dubanta hadi da kama hannayanta ya ce" Bab, look at me, kar ki daga hankalinki ki haihu lokaci bai yi ba, ki yi hakuri da ihun da na maki, kawai dan bana son komai ya haɗa ki da ANAS ne, im sorry love, kar ki haihu lokaci bai yi ba, kar ki haihu ranki a bace"
Nur dake sake rintse ido, a hankali ta ce" Plz ka daina fushi da Ni , ka daina tunanin zan iya duban wani a duniya bayanka..........., ka daina irin wannan plz "
"Kai, ku wuce mu je asibiti, yarinyar nan ciwo take ji" Anna ta katse su, tana riko Nur, hadi da mikawa MAZNA wayarta da take miko hannu dan ta kama mata ta ce" MAZNA, ku je bangarenta ku hado kayanta da aka hada a dakin baby ku tardo mu, haihuwa ce fa"
Ai kam su Farhana dake boye a kofar shigowa sai suka shiga ihun haihuwa kuma?????
Aliyu da ya dawo daga aika ya ga su Anas tuni ya ja su gefe suka zanta, ya nunawa Anas cewar ai ba wanda ya kore shi, oga ma yace a barshi ya huta idan ya ji hankalinsa ya dawo ya je ya kama aiki ba wata damuwa kawai suna iya tafiya, gobe ma ya koma bakin aikinsa, ama idan yana son ganin OGA ya tambaye shi inda yake zasu hadu ya daina zuwa nan, domin idan har a da oga bai ji haushinsa ba, a yanzu zai ji in har ya matsawa gidan nan da zuwa, bayan ya salame su ne ya zo dan ya yiwa su FARHANA masifar a kan me zasu sanyo Anas, kawai suka kama ihun haihuwa kuma????, a lokaci kankani wajen ya rikice saboda fitowa da Anna ta yi da mama talabe da Nur, shi kuwa ya dauko slifas dinta suka sauko suka shiga motar Aliyu , su kuwa suka nufi bangaren ta da gudu dan su hado kayan da Anna tace , wato MAZNA da ta fi kowa zumudi sai su Farhana da tsoro ya kama su, suka shiga haɗawa dan su bi su a baya .....
Suna zuwa likitoci suka amsheta suka shige da ita, ya zamo Anna da Mama suka bi bayanta saboda ana bari a je a ringa yiwa mai haihuwa addu'a da bata kalamai, wanda shirun NUR yake basu mamaki saboda ba baka sai ido, sai dai ta rike hannun wanda ta samu ta sada kai kikikikinit kafin ta dago tana sauke ajiyar zuciya ...............
A hankali IMAD yace" Aliyu, na bata mata rai, har zata haihu dan bacin rai, idan wani abu ya sameta mutuwa zan yi Aliyu, wallahi ina son ta, ina jin haushin ganinta da Anas a duniya"
Cike da tausayi Aliyu ya ce" In sha Allah ba zata mutu ba sir, kar ka daga hankalinka, haka haihuwa take, bacin rai baya sakawa a haihu, lokacin haihuwar ne yayi,, itama ta san ba zaka bata mata rai ba dan baka sonta sir"
A hankali ya ce" Ka tabbata Aliyu?"
Aliyu kam ya kara yin ala wadai da soyayya, tsakani da Allah ubangidansa ne fa yake wannan kalaman kamar wanda zai bar duniya saboda mace...., kai so, so? Hum
A tausashe ya ci gaba da kwontar masa da hankali, sai dai ƙasa fita yayi daga motar har su MAZNA suka karaso suka shige wajen zama da kayan haihuwar, kafin ta fito ta zagaya barin da Aliyu yake, hakan ya sa ya fita, ta shiga motar a hankali ta kama hannunsa tana dan murzawa ta ce" in sha Allah zata haihu lafiya, kar ka daga hankalinka Akul"
Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya ce" har yanzu périod din naki bai zo ba ko?"
Mazna ta gyada kai tana duban cikinta hadi da sauke ajiyar zuciya....
Bata taba zarce lokacin périod din ta ba, wannan karron Gayanan har kusan sati Uku bai zo ba, Ama tana jira dai ga gani