Sashe 85
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Su kuwa dama murmushi Anas ya sakar mata ya tsaya ta shige ya rufe kafin ya shige gaba ya tayar
A lokacin da suka juyar da motar su, sai ya samu kansa da dan bin bayan motar kafin ya maido dubansa kan malamin da suke magana a tausashe ya ce" Malan, a kula da dukan abinda na ce, in sha Allah zan shigo gobe ma"
Daga haka suka yi Salama ya dage madubin motar a hankali ya sake lumshe idannuwansa yana riko hannun Anna ya jimke a hannun nasa har sai da ta dube shi kafin ta maida hankali kan tukin Aliyu, domin idan ta shiga daya cikin motocin da Aliyu ke jan ogansa tamkar ba tafiya suke yi ba, Ama nan da nan sai a iso waje,
Hakan ce ta faru, domin nan da nan sun iso, sai dai da yake shi ma Anas gudu ya yi da su ,tuni ya iso da yan matan Anna, har masu aiki sun yi ciki da kayan, ya zamo Su ne basu shige ba, haka ma Anas yana tare da su
Isowar motar su ta sa FARHANA karasawa ta bude bangaren da yake, tana budewa sanyi da kanshi na buso mata tana murmushi ta ce" sannun ku da karasowa, Anna yaya kan?"
Anna ta ce" Da sauki, baku shige ciki ba??"
FARHANA ta ce" Eh zamu shiga yanzu , ke muke jira"
Anna ta gyada kai, kafin ta dubi IMAD ta ce" Idan ka huta, ka zo ina son yin wata magana da kai mai mahimmanci"
Idannuwansa dake kan Anna ya sake budewa a lokacin da ya fito da ita kamar wace ke cikin babbar jinya ya sake nufa falo da ita a tausashe ya ce" Yanzu ma mu yi maganar, ban gaji ba Anna"
Anna ta matsar da labule idannuwanta suka sauka a kan Inna dake zaune, hakan ya sa ta hadiye abinda ta so fada ta saki fuskar ta sosai tana duban Inna dake gyara gilashin fuskarta tana sake duban IMAD dake talabe da Anna ta ce" Subahanalahi, innalilahi, me yake damunta? Na shiga uku me ya same ta? "
Anna ta janye hannunta hadi da raba rikewar da Imad ya mata ta karasa inda Inna take tana sake sakin fuskarta da kyau ta ce" Ba komai fa Inna, kaina ke ciwo shi ne yake riko Ni kamar wace bata da lafiya"
Inna ta mika hannu tana riko ta , ta ɗan janyota da dan karfin da ya rage mata tana fadin" ya wahaku ya gafuru ya salamu, zo in gani Allah ka rufa min asiri kar ka amsar min ita kafin Ni, in Kika mutu kika bar Ni ai matar yaron nan da kanwarsa da kuma mamansa shake Ni zasu yi su kashe Ni su kirbe banza dan a yadda nake ganin abubuwa da wahala su bari ya bine Ni, zo in maki kamu, sanu kin ji? Ko mu je asibiti ne?"
Farhana ta tabe baki, a tsaye suke su uku , su biyun kowane na son ganin matar nan da kyau, Farhana kuwa abinda ya dame ta ya fi karfin tunanin son ganin gigitar kakarta, gaba daya hankalinta a tashe yake, ji take yi dama bata je dakin Anna jiya ba, gaba daya ita ke cikin damuwa ba kowa ba
Anna kuwa dukawa ta yi gaban Inna ta yi mata addu'a sosai sannan tace ta zauna a gefenta dan ta kula da jikin nata......, hakan kuwa aka yi domin ko hayewa kasa yi ta yi saboda ba zata take umarnin Inna ba
A tausashe ta ce" Inna tafe muke da yarinyar fa ta wajen maman Andadi da kuma yar uwarta "
Inna ta tabe baki ta ce" Kai Ni me ya haɗa Ni da yarinyar da aka zo gidan nan jiya ba'a neme Ni ba na ganta? Barni da kayan haushi ba abinda ya haɗa Ni da ita!"
Anna ta dubi Imad da ya zagaya ya zauna yana duban farantin da mai aiki da ta ajiye dauke da kayan tarba ya dauki ruwa ya bude yana kafawa a bakinsa saboda yadda yake jin wata ƙishirwa na neman damun rayuwarsa......ta ce" Ku karaso ku gaishe da kakarku mana, ku taho, Nur taho maza"
Nur dake baya baya a dole ta taho din , kuma tana fara zuwa sai ta duka kasa sosai ta lalubo hannun Inna a tausashe ta ce" ina kwana kaka, ya gajiya? "
Inna ta gyara gilashinta da kyau ta zubawa fuskar ido , a hankali ta kalli dan bakinta kafin ta kalli Anna ta ce" ikon Allah, jikina du yayi sanyi, ki ga y'a kamar yar tsana kukub da ita Masha Allah wannan ai ba zaka iya fushi da ita ba abu a mulmule, gaskiya basu yi mata rikon bakin ciki ba ji dan bakin sai kyali yake, kuma tace da Ni kaka ikon Allah ashe bayan IMAD zan samu mai ce min Kaka? Taho jikata matso in ga kumatunki?"
IMAD ya dubi kaka da mamaki , ikon Allah, meye haka kuma?????
Anna kuwa dariya ta yi tana janyo A'isha ma ta ce" ai kam, wannan din ita ce yarinyar da nake firarta cewar na yi y'a din nan? Wato Nur, A'ishan kuwa gatanan Inna, yan uwa ne tare suka tashi ...."
Inna ta dubi inda A'isha ke duke itama ta mika mata hannu tana sake washe baki ta ce" a raina na ji zan so ya'yan nan, a cen cikin raina na ji tabbas ya'yan nan zan so su, ina fatan ka maka iyayen kotu dan a bamu su ko? Dan yaran nan ba inda zasu je, ita din ma ba bata zan ba gaskiya saboda a nan sai an fi kulawa da su, Allah sarki ka ga yan mata yan ya'ya Masha Allah ga hankali ga nutsuwa ga musulunci ziryan a tare da su, ikon Allah ka ga lulubi....."
A zuciyarsa kwarai ya yi tunanin Ayana amon da ya fito fili a lokacin da ya sake duban yarinyar nan mai son yawo ba sutura ya ga ta wani sune kai tana murmushi ya fitar da amon "HUM" , wanda hakan ya sa FARHANA dubansa tana gyada kai a ranta ta ayyana ' ai kadan ka gani in dai matar nan ce, yanzu dai gwara a yi a yita ta kare, dan ni na fi shiga wani hali, gwara mamanka ta fadi abinda ta yanke min na tashin hankali, kai kuma kace a'a ba zaka yiwa kakarka rashin biyayya ba, daga nan a bani lafiya har in samu hanyar nemo wannan dan daban.....mtsssss ko ina ya je????"
Anna ta dubi FARHANA a tausashe ta ce" Farhana, ki tashi ku je su cenza tufafin nan ku sauko ku shiga kicin tare, ku mana girki sannan ku hada da jus kala biyu, ku yi harda bangaren Mama dan ba zata shiga kicin yau ba na fada mata............"
FARHANA ta mike kai a kas ta ce" To Anna, ku taso mu je"
Mikewa suka yi, sumui sumui Farhana ta yi gaba suka bi bayanta wajen elevator, Inna na kallon su ta ce" Ki dai ja wa y'arki kune kar ta saki ta koya musu halayanta na rashin girmama baba da rashin kunya "
Anna ta yi murmushi, IMAD kuwa ya sake duban ta ba tare da ya ce komai ba, sai ma waya da ya shiga amsawa wace ta sa du suka yi shiru har ya gama kafin su yi maganar.
FARHANA bata bude baki ba sai da suka shige dakin ta ta dafe kirji zuciyarta na bugawa ta duka a nan tana fadin" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, na shiga ukuna na lalace, yau kam na san na shiga uku a gidan nan, Anna ta yi fushin da har zata yi masa maganar nan, shi kuwa na san ba wani saurarata zai yi ba, idan ransa ya bace kuwa baya ce min komai kyale Ni yake yi ko gaisuwata baya amsawa....ina zan saka raina?"
Daga A'isha har Nur sai suka zuba mata ido da mamakin yannayinta
Nur ta ce" Farhana me yake faruwa da zafi haka? Waye zai maki fushin? Me aka yi?"
Farhana ta riko hannunta ta ce" Nur, Anna tace in fadawa saurayina yau yau ya zo su gana da yaya, bayan ina rabona da mu yi magana da shi ta fatar baki tunda na sanar masa yayana yana kasar nan, gaba daya bana gane kansa, bayan da baya nan kulun muna tare, yanzu Fisabililahi kai tsayen nan yaya za'a yi ya wani zo?"
A'isha da mamaki ta ce" To me zai hana ya zo din tunda dai yana son ki?, kuma yaya ai tamkar uba yake a wajenki idan aka ce masa yaya na neman sa zai ki zuwa ne?"
FARHANA ta Dubeta ta ce" Kwarai ina da tabbacin yana so na, ama sakamakon tsoron da yake yiwa yaya tunda yace masa ya rike ƙafarsa yayi hakuri ya sa bai kara neman ya ga cewar muna tare ba!"
Nur ta yi mata duban mamaki ta ce" Ban gane ba, ya hana ki ganinsa ama kike ganinsa? To wannan din wani irin zubar wa da manyan ki kima kike son yi a gabansa?"
A'isha ta karɓe da fadin" FARHANA ya hana ki soyayya da shi kike yi????"