← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 141

Sashe 91

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali A'isha ta furta" Kowani bawa nada tasa salon kadarar......., ki daina kuka FARHANA, Allah zai wanke ki a lokacin da kowa bai tsamani ba, ina da yakinin Inna sai ta nuna maki so saboda Allah zai nuna mata abinda take zargi a kanki ba haka bane......., ama ki daina fadin magana a kanta irin haka, ki daina fadin maganganu na raini a kan Inna, ko ba komai Inna tana da shekaru, koda baki hada komai da ita ba tarbiyar da kika samu zata sa ki girmamata , ......, ba ruwanki da tsakaninta da Anna, dole Anna zata yi hakuri da ita saboda uwa ce ita a wajen ta......, kin ga abinda Anna ta ce zaki ba mahimmanci, wato ki nemo shi ki sanar masa!"

HALLAH dake dubanta a tausashe ta ce" Shin kin san inda ake iya samunsa?, misali kin ce ai kuna yawo tare, na tabbata du inda ya saba zuwa ya kai ki ko dan ya gabatar da ke??"

FARHANA ta gyada kai ta ce" ai ba inda ban sani ba inda yake zama, wajen abokansa ne, ke hatta gidansu na sani, kawai ban taba shiga bane a mota nake zama ya shiga ya fito "

FARHANA ta ce" To zuwa zamu yi mu same shi, kila ko bashi da lafiya ne ko wani abin, idan ya so sai mu sanar masa maganar an ce ya fito da magabatansa, ba shiKenan ba?"

Da sauri FARHANA ta dube ta ta ce" Mu je ina? Cabdijan ta ina zamu ji mu je din? Ki rufa min asiri yaya na gari? Hum!"

A'isha ta yi shiru saboda itama dama abinda ta yi tunani kenan, dan a gaskiya Farhana na cikin tsaka mai wuya

Nur ta ce" Ai ba dole sai ya sani ba, gobe in sha Allah zan cewa Anna mu je wankin kan nan, idan muka fita zai kai mu sai in sa ya kai mu inda zamu je "

FARHANA ta girgiza kai da sauri ta ce" A'a, ba abinda zaki fadawa Anas ya yarda yayi haka, idan ma yayi sai ya sanarwa yaya, bayan wannan du inda motar gidan nan ta je ana iya sani, du Yama yakan sanar da inda muka je a wajen manyansa..........a'a ba zia yiwu ba"

Nur ta mike tana tabe baki ta ce" ku tashi kar Anna ta biyo bayan mu, kuma zai yiwu ..........ku mu tafi"

Daga haka ta bude dakin ta yi gaba

Mikewar suka yi, A'isha ta jira FARHANA ta dauko mata abinda zata saka ta shige bayi dan ta cenza, ita ma sai ta shiga cenzawar.......

A kasa kuwa, du yadda IMAD yayi tunanin Anna zata yi maganar bata yi ba, hakan ya tabbatar masa dan Inna na nan ne, sai kawai yayi shiru yana jiran sallah domin idan lokacin sallah yayi in aka hauda Inna , ko ta kiya ta hayewarta da kanta sai da Yama lis take saukowa ko kuma sai ma washe gari wani lokacin....., sai kawai ya tsaya ya biye mata irin yadda ta dage cewar lalle lalle sai sun yi Shari'a da iyayen su Nur an amshe mata yaran gaba daya take so, kuma mama kuwa dama ba zata taba bari ta fito daga gidan kaso ba,

Shi kuwa kawai mamakinta yake yi irin yadda ta ki yarda ta gane komai, Anna kam murmushi take yi tana kallon su, bata shiga maganar ba, haka kuma bata yi masa maganar da yake jira ba

Budewar elevator da fitowarta ya tsayar da maganar da ya fara lokaci daya yana zuba mata ido hadi da duban Inna a ransa ya ayyana ' Madallah, yanzu zan ga maganar lulubi da kika yabi wannan abar da shi!'

A nutse ta karaso tana murmushi ta dauki ruwan dake ajiye ta je ta zauna kusa da Inna ta bude tana sha a lokacin da Inna ta ce" Sanu yar nan kin sauko? Haba koda na ji, Ni na so in ce maki ki dinga dan saka marar nauyi, saboda kar kuraje su dame ki, Allah sarki wai a gidan naku basu takura maki ba kuwa? Basa dukan ki? Ya dace ki fada min du abinda ake maki marar dadin da zai sa in karbe ki a hannun su kin ji yar jikata?"

Ikon Allah kawai ya saka shi kai hannunsa kusan girarsa ya zuba mata ido ba tare da shi kansa ya gane abinda yayi kenan ba har sai da ta kalli Inna da mamaki ta ce" su wa Inna?"

Inna ta kara gyara gilashin ta ce" Su iyayen naku, ta yiwu ke ma sato ki suka yi"

Nur ta zarro ido, kafin ta yi dariya tana girgiza kai ta ce" Inna ai abanmu baya duka, mama ma bata duka, auntynmu ce ke yi itama idan aka yi rashin ji, kar ki ji haushin abanmu shi ma bai san A'isha daukota aka yi ba, kuma mama ma kar ki ji haushinta bata yi dan ta cutar da A'isha ba kin ji Inna?"

Inna ta Dube ta, kafin ta kalli IMAD da ya mike yana duban Anna a tausashe ya furta" zan dawo, zan duba jikin MAZNA ne"

Daga haka ya nufi waje abinsa, har yan matan suka sauko sauran suka hade suka shige kicin aka bar Anna da Inna har sai da lokacin Sallah ya gabato suka shige sama tare, Anna da niyar tana gama sallah zata sauko ta yi magana da shi...............Kisan mummuke Page 55, and 56

Yan matan a kicin suke sunna aiki, sai dai du karfin aikin FARHANA ce , domin su abinda suka iya bai kai girman wanda ta iya ba, uwa uba aiki da kayan gaz du sai suka tsaya suna koya sannan sunna yin du abinda tace a yi cikin tarin tambayoyin da suke yi mata wanda ya dauke hankalinta daga yanayin rashin kwarin jiki da fargaban da take ciki

Anna da ta sauko ta shige kicin din da murmushi ta shiga duba abinda suke girkawa harda jus din da suka hada suka saka a frij, nan ta umarci mai yin sallah da ya je yayi ya dawo, wanda yake halin fashin sallah kuwa ya zauna ya kula da girkin

Su duka tafiya suka yi, hakan ya sa Anna tsayawa tana kulawa da girkin hadi da gyara fruits din Inna, domin su ta fi sha fiye da komai, bata cika fada abincin da ake yi ba, wannan ya sa bata haduwa da yawan ciwace ciwace...............

Saukowa suka yi yanzun su duka da hijaban Farhana saboda sallar da suka yi basu cire ba, sai dai sunna fitowa suka samu Murtalab da IMAD zaune sunna fira wace alamu suka nuna mai mahimmanci ce

Gaishe sun da FARHANA ta yi kusan tare suka yi da A'isha, a dole itama HALLAH ta yi sannan ya zamo ita ce karshe wajen nufa kicin din bayan ta bi wata kyakkyawar butar shayin dake tafasa saman wani kyakkyawan murhun garwashi dan Karami mai kyan gani a ido yana saman wani faranti na karfe wanda ke tare toka da yan kananun garwashin dake fadowa sama

Fira suke yi, firar ma mai mahimmanci domin Mutalab din ke fada masa zai so ya mayar da kaso mai tsoka na harkar reshen nemansa a nan, sannan yana so ya yi gini , domin shi fa Nijar ta masa, yana kyautata zaton zai dawo nan da zama gaba daya ne....., hakan ya sa IMAD fuskantarsa da kula ya ce masa ya dace yayi hakuri kadan ya kara tabatarwa zuciyarsa abinda yake so kenan, ba dan kowa kuma yake so ba sai dan kansa, saboda lamarin rayuwa kar halin rayuwa ya cenza masa abinda yake so din...

Ya koro da bayanin ne suka fito, a hankali ya ja bakinsa ya yi shiru yana dauke dubansa daga kan FARHANA da ta fara gaisar da su, sai dai sunna nufar kicin din ya sauke dubansa a kanta a lokacin da ta zamo ta karshe wajen shiga kicin din har shirunsa ya matukar bayana a wajen, har ma Murtalab ya zuba masa ido da tarin mamaki da kuma yarda da bayanin da Aliyu ya masa

A hankali ya dawo da dubansa ya sauke kan Murtalab, wanda yayi kamar ba shi yake kallo ba

A hankali ya jimke hannunsa kasa kasa sosai ya ce" Ina ga banda lafiya"

Mutalab ya zuba masa ido, a tausashe ya furta " Me yake damun ka? Subahanalah"

IMAD yayi shiru na dan lokaci, kafin a tausashe ya ce" Zan je in ga likita, kwanakin nan ina fama da bugawar zuciya, may be jinina ke son hawa......."

Mutalab ya zarro ido yana kare masa kallo, da girmamawa ya ce" Subahanalah, eh gwara mu je, ka tashi mu je yanzu, sannu Yaya"

IMAD ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Zan je, fira zamu yi da Anna idan muka gama zan je......." Ya karashe yana tunanin bari su gama firar ya tisa keyar MAZNA su je su ga likitan tare, saboda shi bai wani yarda ba cewar wai ta warke duda ya same ta da yan uwanta sunna ta fira da dariya yanzu ma, Ama kawai zuciyarsa bata bashi cewar MAZNA tana lafiya ba

Da kula ya sake duban Mutalab ya ce" kar ka yiwa abih firar nan ta waya, kuma kar ka yi masa ita yanzu, ka ga magana ce mai girman gaske kuma mai mahimmanci, ka bari zuciyarka ta kara aminta da haka, sai ka je ka same shi, abinda ya yanke kuma shi za'a yi ok???"

Mutalab ya dan turo baki irin na shagwababen kanin nan ya ce" Kai da na zo dan ka kama min?"

IMAD ya girgiza kai ya ce" Akoy abinda zan kama maka ido rufe, ana akoy wanda dole zan sa mu bi a hankali......"

Mutalab ya sauke ajiyar zuciya sannan ya mike yana fadin" Bari in je in shirya zan raka ka ganin likitan nan....."
Chapter 91 · 0% Book details