← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 268

Sashe 92

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yana Gama wannan maganar faiz ya lumshe idanuwa gami da sakin ajiyan zuciya ya bude Idanuwanshi ya kalleshi before yace
"Well you're somehow right....Amma not all girls are taken...dole da akwai wayanda suke Basu da lovers ai..." Fajz ya fada mashi
"Maybe Yan yara kou Amma in har zaa samu yarinya big babe Kuma Bata da kowa then kawai tayi nauyin jini ne so it's better your don't ruined someone's relationship for your own happiness...." Ahmed ya fada mashi hankali kwance sending him message cikin dabara yayinda shi Kuma faiz thinks he is really right, there's no reason to ruin others relationship because of your happiness,
"Well Allah yasa mu dace...it is well..." Faiz ya fada Yana relaxing.saids Ahmed yaci ya koshi yaga kayan dake gefe daya Nan ya tambayeshi na waye,he told him it's for his lefe Kuma ya fada mashi he wants to buy more from his girlfriend
"Ashe babe dinka big business lady ce...I saw many items on her phone.. Kuma at a very affordable price... yanzun zai sayi wasu Kaya daga wajenta..."faiz ya fada mashi
"Oh... gaskiya mun gode...kawai na manta in fada maka when ever you need anything in har kayan sawa ne muna dashi..."
"Gaskiya kayanku nada kyau...nama fada Mata she can introduce her business to Yan company din tunda suna da Mata da iyaye Mata,..."
"Gaskiya hakan yayi sosai.."Ahmed ya amsa mashi,  bathroom faiz ta Shiga yayi alwallah shima Ahmed ya shjga yayi alwallah suka fita tare inda suka tarda Amira zaune looking so Lost, now Ahmed knows she's not over her pain har yanzun and har ga Allah hakan na ci mashi tuwo a kwarya, yasan it's not easy Amma she should try to let it go, abincin daya kawo Mata Yana inda ya barshi, kou tabawa Amira batayi ba, faiz na fita baj kou kalli inda take zaune ba yayi Saurin ficewa yayinda shi Kuma Ahmed ya jinjina abincin yaji Yana Nan inda ya kawoshi, kallonta kawai yayi without saying anything because he is running late already, kafin ta fita har faiz yayi mashi mugun njsa, kaman he is flying yanda yake tafiya, Ahmed was so surprised to see him so far away from him, tare sukayi sallah a masjid din company sanna Ahmed ya wuce shi Kuma faiz ya koma office dinshi, yau Amira na fitowa daga sallah shi Kuma Yana shigowa, Saida ya Bata dama ta wuce shi ma ya wuce, one thing is he is trying very hard to block any sort of thought da zai Shiga zuciyar shi, he is not thinking about anything,it's the kind of moment you block any thoughts that doesn't suit you, Kiran Amira yayi ta landline dinsu ta fada Mata taje wajen accountant ta amso mashi wasu file containing all the details from last year zuwa yanzun, Hakaa Nan he wants to get himself busy, doing something, he feel he should call bintu suyi Hira Amma sai yaga it's not going to help at all and he needs to be ok, he needs something to do, for the first time he feels Zama Haka nan  not doing anything is not so good at all, Amira na zuwa wajen accountant ta fada mashi sakon CEO,he was so surprised by this,how will someone just wake up ya Fara neman file din last year all of a sudden without notification,
"Ki fada mashi zan tabbatar everything is ready by tomorrow sai in kawo Mashi...Amma yanzun hadasu yanzun is going to be difficult..."ya fadawa Amira, Amira that is Also looking for something to take her heart off her pain komawa tayi ciki  kaman ta kirashi kawai sai tayi kawai ta wuce ta fada mashi, office dinshi ta bude ya daga Idanuwa ya kalleta for only a second ya saukesu
"What..." Ya fada atakaice,
"Yace a bashi zuwa gobe...it will be ready..." Bata karasa ba yace
"Ki koma kice he is insane...ya zaayi in tambayeshi Abu yanzun yacemin sai gobe...ki fada mashi I need them now...now or never... period..." Ya fada Mata atakaice face dinshi kaman Bai taba Dariya ba, juyawa tayi ya daga Idanuwa ya bita da kallo tare da tabe Baki Yana sauke kanshi, Amira dake cewa
"Now you're the boss.." ta fita cikin ranta Tana tunanin Daman mutunci da kirki doesn't suit him like zagi da mugunta, fita tayi ta koma ta fada wa accountant he needs the files now, tsayawa tayi bawan Allah Nan ya Gama hada files gabaki daya ya tattara Mata, kou daukan su Bata utayi as Yana dauke da duk wata income din company in written dukda da akwai wasu bayanai Kan computer that can be easily transfer to him he prefers the papers kawai don he is indirectly going Insane, Amira Bata iya daukansu duka, she knows he can ask the messenger to do this but he prefers to send her, first set of the files ta kawo Mashi ta dire a gaban shi with wasu dust a jikin file din,da sauri ya Mike Yana cewa
"Amma Kun Raina min hankali...wato in bance ayi Abu ba bazaki San ya kamata ba?...why will you bring dirty files into my office..."ya fada face Dinshi kaman Bai taba dariya ba Amira tsaye tayi tana kallon ikon Allah,
"Abeg take this out.. dust them and bring them back..." Ya fada Mata tare da Galla Mata harara Yana sake kumburewa, wannan mutumin Yana da different colors, wato he can be nice and still be a pain in the ass, Babu masu ta kwashe su ta fita dasu, .
"gosh..she won't even argue...." Yafada Yana shafa goshinshi looking so angry, nikam I can't even say or see why the sudden anger, shi kanshi he is angry for no good reason, Amira dai fitA tayi tare dayin abinda ta sakata ta maida mashi,
"Su kenan?..."ya tambayeta Yana kallon files Din dake ajiye a gabanshi,.
"No.." Amira ta fada Tana juyawa, inda yasan abinda take ciki da he will understand nothing hurts her or get her angry right. She's at the peak of anger and nothing or any behavior zai sa ranta ya baci Kuma abinda Bai sani ba is she prefers him hurt, she's always ready for the worst from him don she knows Bai da mutunci and bataga abinda zaiyi Mata da zai Bata Mata Rai ba, ficewa tayi ta dauko sauran Saida tayi dusting dinsu sosai, she loves doing this because it takes her heart a way from pain for just fee minutes before it goes back to it's normal State, shigowa tayi ta ajiyesu faiz Kam kou kallon inda take baiyi ba,  tana ajiyewa ta juya zata fita yace
"Come back here..." Ya fada Mata atakaice, juyowa tayi ta dawo gareshi
"Ki rabasu Kashi biyu...kiyi accounting dinsu... I will do the rest...after all ke kikayi suggesting mu dinga accounting..." Ya fada Mata kou taba files din baiyi ba,
"Ok..." Ta fada Tana dawowa ta ta raba twelve huge files din gida biyu ta dauki six ta bar mashi sauran,
" I will need them by Monday...so you have form today Thursday zuwa Sunday night..." Yafada Mata.
"Ok..." Ta amsa mashi tana ficewa.
Tana komawa office dinta ta Fara aikin as it's as if he knows she needs something like this.
Chapter 92 · 0% Book details