← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 268

Sashe 189

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

now yasan kusan lokaci guda Amira da Ahmed sai hajiyar su zasu hadu a nan, he is not going to say anything but he prays bintu react and say something, he prays ta fada Nan kawai ya huta, at least if ahmed yasan suna soyayya kilan zai hakura ya bar mashi ita, Dr ne ya Shigo Yana asking bintu some questions tana amsawa, Nan ya tsaya yayi Yan rubuce rubuce ya fita. Yanda faiz ya daure face alone kasan ba Mara lafiya ya zo gani ba, he frown his face kaman Bai taba Dariya ba, sannan kou da yazo baice ya jikin ba, he just sat there, bintu Dan Satan kallon shi tayi taga yanda ya hade Rai kou ita data Sha bakin ciki bai hade kaman nashi ba, ya kumbura kaman zai fashe, da cikin ya zube sai tayi nadama, she feels it's not the right approach to solve this problem, yanda fajz yahi magana jiya ya nuna Mata that at the long run ita zaa bawa rashib gaskiya, tasan magnar gaskiya she's the cause of the miscarriage don ita ta Fara dukan cikin a Kai kai, the baby is strong don kou mutum aka dinga duka Haka Nan sai ya mutu but it sticks around, sai gashi Wannan faduwar ta karshe ya kawo karshen cikin, it's all her fault, she's not regretting because she so much cares about faiz sai dai because she will be blamed by the whole family, Babu abinda zata Fadi da zai Kai nashi, he talks strong and louder than her, dakin Babu Mai cewa komai, all she knows is Ana sallamar ta gidansu zata wuce, kou sister sakina data dage da asking dinta if faiz is right bayab ta fada Mata karya yake tace daga Nan ta tafi gida har sai manya sunyi resolving issue din, she's so scared su zauna a gaban manya faiz na fadin ta kashe mashi Baby, tasan she will surely be dealt with, kadan taci ta Mika warmer din ga sister ta dake forcing dinta taci Naman "Na koshi..." Bintu ta fada ahankali "Wane irin kin koshi?...me kikaci da dazaki koshi...Baki ganin yanda Kika koma kaman wata matsiyaciya...duk kin lalace because of rashin kula...dallah eat..." Ta fada tana watsawa faiz harara before ta sake kallon bintu tace "Gashi kou lap guda Baki cinye ba...pls eat...ba matsiyata bane mu..." ta fada Tana fixge fixge "Sai ki Fadi kou su waye matsiyata..." Faiz ya fada Amma cikin ranshi Yana kallon yanda take magana he knows she's indirectly talking to him, "Na koshi..." bintu Ta sake fada mata, Nan sai ta amshi warmer din ta ajiye ta Hada Mata thick tea ta Bata, kadan kawai bintu Tasha, inda sakina data San halin da take ciki da Bata matsa Mata Kan cin abinci ba, she's in so much trouble, ga na haushin faiz, gana matsala da zai sakata if he tells their parents. Hajiya kadijatu da hajiya Fatima me Suka Fara zuwa, faiz ne ya tsaya daga waje suka Shigo tare, hajiya kadijatu knows bintu did it so tana zuwa ciki tace "Dafatan kina samun farin ciki yanzun.... are you ok?...now that you succeeded..." Ta fadawa Bintu "Iyami...bani bace..." "Will you keep quiet?..."faiz ya daka Mata tsawa cikin takaici that she's denying it, "Nayi magana da Dr...bana turo maki Dr ba?.. you practically made it clear that kina son cikin out of you..." Hajiya ta sake fada cikin takaici, kuka bintu ta farayi kanta kasa ta San ta Riga ta shigar da kanta, "Komai it base on destiny...Dan ba rayayye bane...so let's stop talking about it..."inji hajiya Fatima, sakina Kuma sai kallon su take deep down she's thinking maybe it's true but Bata ce komai ba "Stop crying my dear..." Inji Hajiya Fatima, harara fajz ya watsa Mata tare da hade Rai, now he knows she's trying to make what she did ok, Basu Dade da zuwa ba ahmed ya Kira faiz Kan suna Ina sun iso, Nan faiz ya mike ya fita, lokacin Amira da cikinta ke kadawa ta fito daga cikin Mota and so is ahmed, suna tsaye suna jiran faiz ya zo, Amira ji take kaman ta gudu, don she knows if tana position din bintu she won't take it likely, Amma in ta tuna cewa faiz yace zaiyi Mata magan sai ta samu sauki cikin ranta, faiz na fitowa ya hangeta da ahmed tsaye, she knows he is present so kasa daga Kai tayi, she can't just believed she hugged and kissed him, da ka ganta kagan mara gaskiya, ganinsu tare da ahmed ya mugun tsotsawa faiz Rai Amma what can he do or say, with a smile ya Karasa wajensu Yana mikawa Ahmed hannu, gaisawa sukayi inda ahmed ke cewa "Hard luck fa...Allah ya kawo rayayyu..." Ya fada, faiz that couldn't take his eyes of Amira cewa yayi "Amin...Haka Allah yaso..." Ya fada "Good evening sir..." Amira ta fada mashi, "Evening ma'am..." Shima ya amsa Mata, Dariya ahmed yayi Yana cewa "Sannu ku su sas and mas..." Ya fada, shige masu gaba faiz yayi suna Dan magana da ahmed but Yana kallon amira, ahmed ya iya sa Ido sosai don Haka he sees it all, Yana kallon yanda faiz ke kallon Amira but he knows she's not looking at him, kofar dakin faiz ya tsaya ya kalli Amira yace "Now here we are. ." Ya fada Yana bude kofar ahankali, Amira ji tayi kaman an bude chest dinta sabida tsoro, faiz ya Fara Shiga bintu da sauran mutanen wajen Suka kalli Mai shigowa, sai Ahmed na biye dashi, sai Amira dake tafiya kaman kwai ya fashe Mata a ciki, bintu na ganin ta Bata San sannan tace "Lallai ma...rainin wayau.. " ta fada tana kallon Amira in such a way that sai kace ba innocent face dinta ke irin wnanan kallon ba.
Chapter 189 · 0% Book details