← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 268

Sashe 52

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amira da gudu ta shjga bangaren mamanta ta taddata zaune da nazifa sai asiya a dakin, cikin serious excitement ta Shiga dakin tana Cewa
"Mummy Kinga abinda Yaya Ahmed ya kawo min..." Tafada Tana kallon face din mamanta to know if she's welcome or not, hajiya Bata amshi ledar ba Balle taga abinda ke ciki sai tace
"Ya kyauta Allah ya biyashi..." Ta fada atakaice not looking at her at all, nazifa da asiya saj wani irin kallo suke Mata kaman ba yar gidan ba, Yar gidan ma yayar su, ahankali Amira tace
"Mummy...har da form din makaranta ya Saya mashi..." Ta fada ahankali don tasan the main source of her happiness not the cloth but the love he is showing to Nasir
"Tou Allah ya biya shi..." Hajiya ta sake fada Mata ahankali, Amira miss this, she misses staying in the bedroom da mom dinta gisting she remembers sanda in suna labari su nazifa da asiya sauka shigo sai mamansu tace
"Baku ganin magana muke zaku zo ku Yi min zaune?.." take fada Masu anytime she is discussing something important da Amira, tasan wannan na daga cikin reason daya sa Suka tsaneta sosai, ganin mum din ta Bata Kara cewa komai ba Kuma Bata kalli inda take ba Yasa ta juya ahankali da ledar hannunta, she's ok with this, ai before Bata samun hakan so it's ok
"Ai Baki fada Mata kina da waya ba...kinsan mummy har waya gareta ..katuwa Mai chatting..."inji nazifa,wani irin kallo hajiya ta Watsa Mata yasa tayi Saurin yin shuru Bata karasa Maganar ta ba, Amira Kam Bata tsaya ba ta fita zuwa dakinta, to her surprised tana shiga sai taga Babu Ahmed, tasan ba fita yayi ba don ba dadewa tayi a dakin mum dinta ba, ruwa taji cikin bathroom sai ta zaro idanuwa sosai tare da ajiye kayan hannunta, her bathroom is one of the most secretive place da bazata so kowa ya Shiga ba but sai ga whole Ahmed a bathroom dinta, hannuwa ta Fara yarfawa cikin fargaba da Kuma kunya sosai dukda ba Wai ya fito ta ganshi ba, kawai she knows he is going to see her old underwears and ba karamin Abun kunya bane a gareta,
"Wayyo Allah...why do you have to enter my toilet..."fa fada kasan makoshinta with the assurance cewa he will surely see them, they're almost everywhere a bathroom din so tasan Vai taba yuwa ace Bai gansu ba, she wish zata iya suma Kafin ta fito, gashi bata da inda Zata iya boyewa ya fita ya tafi kafin ta dawo dakin Amma ba karamin kunya zata ji ba, Zama tayi bakin gadonta kanta kasa bayab kaman minti goma sai aka bude kofsr bathroom din, kanta kasa Bata kou iya daga Kai ta kalleshi at all, kallonta yayi wondering kou yanzun ma another old rag ne a jikinta.
"Yaya...mummy tace...allah ya biya ka..."ta fada mashi kanta kasa,
"Oh.. it's nothing..." Ya fada with a smile,
"Am sorry na Shiga bathroom dinki...I have to pee ne..."ya fada Yana kallon yanda ta sadda Kai kasa tana Wasa da yatsun hannunta,
"Ba komai yaya..."
"Yanzun Zan tafi...kinsan try and fill that form gobe Zan zo in amsa Kuma Ana bukatar passport dinshi biyu da Kuma birth certificate dinshi...da akwai?" Ya tambayeta
"Aa...duk Babu..."ta fada kanta kasa
"Ok...Zan fadawa ismail ya taimaka ya kaishi a Yi mashi passport ssi Kuma birth certificate din Zan yiwa sister murja magana kilan zsra iya samo Mana..." Ya fada Yana tsaye gaban mirro ya bawa mirror din baya
"Ok Yaya... thanks..." Tafada mashi, Bai kara cewa komai ba ya fita, yau Kam Bata rakashi ba kaman yanda ta Saba, before she will follow him har kusa da falo sannan ta koma ciki, yau Kam tana zaune kanta kasa with a very huge shame one, she knows abun kunya ne namiji ya gan pants dinka balle Kuma ya gansu old, old din ma na beyond words, Yana ficewa ta Dora hannu bisa Kai Tana Mikewa don ganin condition din pants dinta, har ta nufi kofar bathroom din sai Kuma ta tuna Yana iya dawowa sai tayi Saurin zuwa ta kulle kofar dakinta sannan ta dawo ga bathroom din ta bude, Nan taga all pant da bra dinta kasa, Babu kou daya inda take shanyasu, ba ganinsu kadai yayi ba he made sure she knows he sees them, ya nuna Mata he sees everything
"Wayyo Yaya..."ta fada cikin matsanacin tausayin kanta, kawai sai tafara Kuka sabida yanda takeji cikin ranta. Ya zatayi ta sake Kallon shi kafin ta mutu ta bar duniyar nan, wannan abun kunyar yayi Mata yawa, tana zaune tana kuka sai ga message ya shigo wayarta da sauri ta dauka thinking it's Costumer Amma tana dauka sai taga it's Ahmed
"What the size of your pant and bra..." Ta turo Mata, da sauri ta ajiye wayar tana cewa
"Wayyo kaicona... kaicona...Amira kinji kunya...kinji kunya...kin Gama tozarta...Wanda kikewa kallon Wanda Bai da single matsayi to get close to you gashi ya Zama Wanda zai Saya Maki pant and bra..." Ta fada Tana kuka sosai, kou kadan Bata da niyyar replying dinshi sai gashi ya sake turo Mata
"Wallahi kou ki fadamin kou Kuma a bar maganar aikin...Kinga na rantse ban kaffara.." ya sake turo Mata
"What did you want from me..."ta fada Tana kuka,
"Nidai ban iya turawa..." Ta fada Tana ajiye wayar ta, Bai Kara turo Mata Komai ba sai bayab sallah ishai ya kirata, kin dagawa tayi don tasan it's about the inners, he gave her good 5 miscalls Bata dauka ba, Dole ya shirya ya Kama hanyar gjdansu, Daman it's just 30 minutes drive zuwa gidan, Bai Shiga ciki ba iyakan shi falo ya gaida mum dinta sannan ya kalli nazifa ta fada Mata taje ta Kira mashi Amira, Yana kaiwa Nan ya koma cikin Mota, kou da nazifa ta fadawa Amira sai da taji gabsnta ya mugun faduwa,
"Na dai Lura so kake ka tozarta ni..."ta fada tana Mikewa, hijab ta dauka ta saka ta fita don Daman Nasir ta Riga yayi bacci, she's so happy data taka compound dinsu yau but the situation at hand won't let her show how happy she is, she's so ashame of herself, Ahmed na ganinta ta fito ya fito daga cikin Mota ya tsaya a jikin Mota face din shi daure kaman Bai taba Dariya ba,
"Ke Baki gan message Dina ba ?.." Ya fada sounding very Angry at her
"Na gani..." ta fada kanta kasa wondering yanda he can change into many colors, he just talked to her like he is her father
"Kin gani shine Kika sa na fiti bayan a very hectic day?..kou ban Isa in tambayeki Abu bane... kou kunyata kikeji.." ya tambayeta sounding very Angry
"Aa..." Ta amsa mashi
"Then now tell me..."
"Zan rubuta maka.. " tafada cikin kunya
"It's kind of late for that...tunda har Kika Sa na zo Nan da kaina sai kin fadamin...or ki Shiga Mota muje mu sayosu..."ya fada Mata, da sauri tace
"Aa Yaya pls...am sorry...kayi hakuri...wallahi Zan rubuta maka ta text message..." Kai kawai ta dinga girgiza Mata alaman Sam Bai yarda da hakan ba, dole sai da ta fada mashi sannan yasa ta rubuta mashi date of birth din Nasir da sauransu before ya tafi, she just wondered wane iri ne wannan bawan Allah.

Wace gari ya kawo Mata 2 dozens na pant da bra sai Kuma perfumes kala uku da Kuma kayan gyaran gashi sai takalma don ya amshi size dinta,Nan ta fada Mata ta shiryar ranar Monday zatayi resuming office Kuma. Ranar Friday ya amso uniform din nasir Bai shiga ciki ba ya bada aka Kai Mata don ta lura kou kadan Bata son Yi mashi magana tun ranar da aka samu pant case din Nan, shi Kuma ya bar matsa Mata ya barta..

Fajz Kuma cikin halinshi babu Wanda ta fasa especially yanda yake treating bintu, har yau baiyi unblocking dinta ba, Kuma duk layin da zata Kira dashi in har ya daga yaji voice dinta zaiyi blocking layin, shidai Bai ce Kar ayi auren ba Amma Kuma he won't give her face da kou me zata gani game dashi tayi broadcasting, zai dinga ja Mata aji in a way that she will be afraid to do anyhow when she gets to his house..
Bintu ta shiga damuwa Amma duk yanda mum dinta zata tambayeta abinda ke damunta Bata taba fada Mata har mum dinta ta dinga tunanin kilan fargaban aure ne ke maidata Hakan say Kuma ta dinga tunanin ai she's too big ta dinga ramewa saboda zaayi Mata aure, Kuma she is so much inlove with faiz to be thinking otherwise. Har babanta hajiya tayiwa magan Kan ta tambayeta why she's loosing so much weight sai alhaji yace a kyaleta maganar auren ne.

Hajiya da alhaji haruna keep praying for faiz kan Allah ya kawo sauyi a rayuwar shi don sun hada Baki sun fita Harkan shi dukda alhaji yasan he comes to the office anytime he wish and leave and time he wants. Amma kou ya sakar mashi komai na office din yayi yanda ya gandama dashi in yayi Ida liquidating office din shikenan. Hajiya kadijatu Bata da abunyi sai adua especially da safe when zata tsaya a window dinta looking kou ta fita, kullum Kan idonta yake fita Kuma its way to late ace maaikaci Yana fita Amma Bata cewa komai iyaka tayi mashi adua, Bata Samun kwanciya hankali sai taga ya fita daga gidan, she knows alhaji means lot of goodness for him as his first son Amma he is loosing the love alhaji have for him and hakan Yana kona Mata Rai sosai.
Chapter 52 · 0% Book details