← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 234 OF 268

Sashe 234

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan sati guda akayi meeting inda alhaji  ya fadawa family he won't let Habib ya auri because of some reason, he showed them abinda ke wayar Habib da maigadi ya kawo Mashi, a ranar Habib ya bar wayar shi a dakin maigadi shi Kuma ya bawa alhaji, he didn't hide anything, he showed them komai da komai inda kowa sai fadin Allah ya shiryeshi kawai yake, Babu Wanda ya yarda ya sake Shigowa inda suke don da ganj yanda Habib ya San mace su da suke manya Basu sani ba, duk sunce zasu zame hannunsu daga lamuranshi sai alhaji abdulrahaman yace Kar ayi hakan zai Zama Kaman don Dan uwansu ya rasu ne, ya fada masu hannunka Bai rubewa ka yanka ka yarda, Dole in danka yayi laifi nor matter how heavy zaka dinga kokarin maidashi Kan hanyar daidai bazaka barshi ya Ida watsewa ba,
"Nidai he is not welcome anywhere near my home..." Alhaji Muhammad ya fada masu
"Hakuri zakayi...he is our son... your son...yaron Nan Yana bukatar mu like never before ..we have to stand and make him do the right thing... alhakinshi Yana kanmu..."alhaji abdulrahaman ya fada mashi, Nan dai aka yanke shawarar a kirashi ayi magana dashi,.
Wacegari yazo family house, Yana ganin wayarshi a hannun alhaji abdulrahaman hankalin shi ya mugun tashi, wayanda suka zo wurin na zaune suna kallonshi, kanshi kasa, cikin Daya daga cikin pictures din alhaji ya Shiga ya nunawa Habib yace
"Wacece wannan?..." Ya tambayeshi, Habib kasa karya yayi yace.
"Matata...ce..." Ya fada saying it finally
"Oh...matarka?...Ashe kana da aure...wato kai ba Dan iska bane har karya ka iya...duk mugun Hali Kai kadai ka Tara cikin kanka kou..."  Daya daga cikin su ya fada.
"Ba karya nake ba...aure mukayi daita.. " ya fada masu, duk kallon juna Suka dingayi,
"In kuka duba...cikin pictures din...da akwai na auren mu..."
"Wa zai iya Kallon through abubuwan dake Kan wayarka...wato Kai Haka Allah ya yika...of all this family members babu Wanda ya San kayi aure.... what type of a child are you...." Inji Daya daga cikin uncles dinshi,
"In ba don late mahaifin ka ba da wallahi duk mun fita harkanka....tunda baka dauke mu a bakin komai ba.. "
"Am sorry...ku yafemin..." Yabfada kanshi kasa.
"Baka San in mutum ya rasu ya bar da na gari a baya zai dinga mashi adua ba...Kuma Aduar da na gari Yana isa ga iyayen shi...why ake son mutum ya bar baya...saboda ya samu masu Yi mashi adua...Kai yanzun a irin wnanan rayuwar da ka zabawar kanka kana ganin iyayen ka will benefit from you in anyway?...ku biyu kadai suka Haifa why Kai da Yar uwarka bazaku Zama hanyar samun Lada ga iyayen ku..." Alhaji abdulrahaman ya fada calmly, Habib feels this, it really gets to him
"Ya kamat ace duk abinda zakayi sai ka tuna da wayanda sukayi sanadiyar zuwanka duniya are no more and kaima wata Rana tafiya zakayi...ya kamata ace kana rayuwa Mai tsafta ba kazamar rayuwa ba... yanzun if we Abardon you zai Zama  Kaman don bamu muka haifeka ba... zamu baka last chance... last chance to he a better person...to change...ba Wai zamu saka maka Ido ba..Amma kasani Allah is all watching and he is watching you...kou me kayi zaka tardashi chan...in sharri in khairi...so the choice is all yours..." Alhaji abdulrahaman ya fada sounding so calm, Kan Habib kasa for the first time he is shedding tears out of pain,
"Yaya...ka mance zancen matar da yake Dashi...banji kace komai ba..." Inji wani daga cikinsu
"Yes I forget...now tell me...ya maganar matarka...zaka kawota Nan...kou Kuma Yaya..." Alhaji Bai karasa ba Habib yace
"Ban Zama daita..." Ya fada Kai tsaye, hannu alhaji ya daga mashi yace
"Babu Wanda yace ka rabu da Matar ka...yanda Ka Riga ka Saba da mace ai bazai yuwu ka zauna babu mace ba...don Haka ..." Alhaji Bai karasa ba Habib yace
"Aa...nidai ban Kara auren....ban komawa Lagos....am so sorry it was all a mistake..." Ya fada calmly
"If you say so...Amma ka tabbatar da mun kara ganinka da wata...kou a cikin family kou a wani waje you're disowned ...ka yarda?..." Alhaji abdulrahaman ya Tambayi habib, abinda Basu sani ba is Habib have seen it all, yaga mace gaba da baya kou kadan Bai shaawar mace balle ace wannan matar tashj da Bata da gurin Daya wuce ta ganshi jone daitaz duk jarabanshi tafishi sosai.
"Eh...na yarda..." Ya fada ahankali praying zaayi mashi maganar Amira Amma nothing,
"Good...then kana iya Zama Nan gidan cikin Yan uwanka...Amma ja sani babanka Muhammad Bai yarda kaje koina kusa da gidanshi ba so be warned. " Alhaji abdulrahaman ya fada mashi, sadda Kai kasa Habib yayi Yana jin wani irin Abu cikin ranshi, it's like having it all and at the Same time loosing it all. He didn't intend calling his wife ya fda Mata komai, all he did was go to the bank and withdraw all his money, wajen Ahmed yaje, at first Ahmed Bai saurareshi ba Amma after long time of pleading ya yarda ya saka mashi kudin a nashi account din, he wants to see his son Amma he won't dare talk about it.

Saida bintu ta saki hawayen farin ciki da aka kawo Mata jewelry da faiz ya Saya Mata, she was so over joyed, she couldn't hide it dukda she's in pain, yanda faiz keyi Mata yanzun ya bambata da before, he is totally taken care of her, ya maidata tamkar kwai, the amazing thing is normal time da yake dawowa daga office lokacin yake dawowa, Bai sauya time kou stay out late ba, he comes home early, takes very good care of her, gives her more than she deserves, duk kishin dake damunta faiz ya dauke Mata damuwa.
Chapter 234 · 0% Book details