← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 268

Sashe 191

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abinda tace yasa faiz Jin sanyi cikin ranshi inda shi Kuma Ahmed ya kalleta with a smile Amma Sam baiyi tunanin she's talking to Amira ba, ita Kam Amira sauran kadsn data saki fitsari a jiki, her body was trembling, she was shaking, bintu Kuma wani irin kallo takewa Amira tana tunanin irin guts dinta, she can't believe amria zata iya zuwa inda take kaman she's not the cause of her problem, wato she's a good pretender kaman yanda tazo wajen wedding dinsu tayi pretending to be happy for her har da unique gift package dinta, now Kuma she's here again with her innocent boyfriend, she feels in ba hauka ba ya zaayi tazo, kou kilan she feels Bata sani ba like Bata sani lokacin bikin ba, or is it that faiz Bai fada Mata she knows ba, kou Kuma yafada Mata but still she decided to show her Babu abinda zata iyayi, wato it's all rainin hankali, budurwar mijinka tazo ganinka a hospital dukda she's the cause of your pain, budurwar ma ba Normal budurwa ba, budurwar da mijinka yafi so fiye da kowa da komai, budurwar da kaga yayi so many rubutun da Bai taba furta maka irin kalaman da yake Mata ba, budurwar da a naka tunanin suna Harkan Zina da mijinta, just imagine your self a position din bintu, what will you do, Will you just be the innocent girl or act wild and crazy, as for me Ina Iya yin the unthinkable, sakina have to look at bintu data zubawa Amira Ido, Amira Kam kasa daga Kai tayi, hajiya kadijatu Kam tasan da akwai matsala as taga har da Amira cikin Bakin da suka Shigo, she just wondered if faiz Bai San zata zo ba don in har ya sani ya Kuma Bari tazo at this moment yayi rashin hankali, ahmed durkusawa yayi har kasa ya gaidasu sabida yaga hajiyar su faiz da abokiyar Zamanta, amsawa sukayi with a smile ya Kara da cewa "Ya Mai jiki.. "ya fada Yana durkushe cikin respect, Bai daga Kai ba Balle yaga yanda bintu ta kumbura Tana girgiza kafa ahankali tana kadai Kai too, hajiya kadijatu dake neman yanda zatayi da bazaa samu matsala ba tace "Alhamdullilah da sauki..." Ta amsa Mashi Tana Kallon "Lallai ma..." Bintu ta sake fadi kaman zata fashe, hajiya Fatima dake zaune kusa daita kallonta tayi tace "What's wrong kike ta lallai ma like wata insane person..." Hajiya ta fada, hajiya kadijatu kallon bintu tayi Amma kou kadan bintu Bata kalleta ba balle taga yanda take kifta Mata Ido "Ai mummy ikon Allah na gani...wani irin rainin hankali na gani...can you believe this..." Bintu dake Magana kaman wata sabuwar Shiga mahaukaciya ta fada jikinta na rawa, Amira da jikinta ke rawa kasa tsayuwa tayi, Bata San lokacin data zauna kusa da inda faiz ke zaune ba, she was trembling and faiz ya gani Amma Bai ce komai ba, he wants this to end, his number one fear is Ahmed but he have to let it go, he wants this secret thing to be over so he is patiently waiting to here her say it, she will help him, at least let him face this fear and get it over with, Ahmed daya samu waje ya zauna kallon bintu da babu inda take kallo sai Amira, kallon Amira yayi yaga kanta kasa and she's trembling, now he knows bintu was talking to her, "Amma wallahi wasu Basu da kunya...wasu sunyi asara... imagine yanda wasu matan sukayi asara..." Bata Karasa ba hajiya kadijatu tayi gyaran murya, kou kallon inda take bintu batayi ba, kawai she's feeling kaman ta tashi da gudu ta chakumi Amira taci ubanta, she's so boiling inside, sakina da hajiya Fatima sai kuma ahmed da Basu San abinda ke faruwa ba sai kallon bintu suke yanda ta kurawa Amira Ido Tana magana ya nuna she's talking to no one but her, hajiya kadijatu na ganin she's not looking at her kawai sai ta Mike daga inda take zaune ta je kusa da Bintu ta zauna a dayan side dinta ta Dan Dora hannu Kan shoulder dinta sannan ta kwantar da murya zata Fara magana kawai sai faiz yace "Let her say it... allow her vomit what is eating her up..."Bai karasa ba hajiya tace "Kana hauka...dallah rufemin Baki ban son wawanci, .." hajiya ta hantareshi, Amira da duk taga tashin hankali duniya daga idanuwanta da har sun sauya launi tayi ta kalleshi Tana tunanin she fell into his trap, wato yaudaranta yaui Bata sani ba, she thought he was saying the truth sanda yace he will talk to her, she was so stupid to believe him, she should have known better, inda tasan hakan zai faru da ta Bari ahmed yaji fushi daita instead of ta zo na aci Mata mutunci, ayi Mata abinda zai sa sauran kimanta ya zube a idon ahmed, right now ba ta kowa take ba sai ahmed, he knows she's a mother out of wedlock yanzun Kuma yasan da akwai Dan Abu a tsakanin ta da fajz da akwai matsala, it's the biggest Shane she can ever go through, sai kasance ya dinga tunanin a jikinta yake it's like she didn't appreciate his efforts to make her a better person, hajiya sai shafa shoulder din bintu take, Baki ta Kai wajen kunnenta tana cewa "'haba my daughter... you're a good... girl...kina da hakuri...Amma...Kar ki Bari bacin Rai yasa kiyi anyhow...pls... kiyi hakuri...I will handle them myself..." Hajiya ta fada Mata cikin whisper, bintu lumshe idanuwa tayi sai ga wani hawayen Bakin ciki, she feels hajiya never does anything don she have relied on her sosai Amma Babu abinda takeyi "Iyami...kina Jin abinda yake cewa ai...he said in fada..." Bintu dake hawaye ta fada cike da bakin ciki "Don't mind him..." Hajiya ta fada tana goge Mata hawaye, kowa na cikin dakin da tunanin da yake especially Ahmed daya zuba Idanuwa waiting to hear what all this is about, he can't just wait to see how this ends, Yana son yaga yanda komai zai kasance Kuma yaji abinda yake faruwa, Daman with behavior din da Amira ta dinga displaying dazun he knows something is wrong, he knows da akwai wani Abu don suna cikin Mota ta Zama very weak "Wati did the innocent boyfriend knows....yasan kina two timing dinshi?.." bintu ta fadawa Amira despite hajiya kadijatu tana kokarin hanata magana, cikin fushi hajiya kadijatu ta Mike Tana cewa "Tunda ban Isa dake ba good...bari in barki kiyi duk yanda kikeso..." Ta fada cikin anger tana daukan hand bag dinta, she wanted leaving Amma sai taga amatsayinta na babba Bai kamata ta bar Yara suna cikin wannan halin ba hakan yasa ta kalli Amira da har ta Fara hawaye Jin last statement din bintu Wanda already tasan it's over between her and Ahmed don tasan he heard what she said, daga Idanuwa tayi suka hada Ido da ahmed da ke kallonta heart dinshi na beating faster than ever, at Least knows faiz Yana son Amira and he had make sure he knows she belongs to him Amma for bintu to say she's cheating on him yasa duk hankalin shi ya tashi, ya mugun Shiga damuwa don wani irin zufa ne ya keto mashi "Tashi ki fita..." Hajiya ta fadawa Amira, "Ai nasan Zaki gudu...kinji na fata fada maki gaskiya...wato you're dating two friends...kina iskanci da Daya...did you intend to marry the other one?..." Bintu ta fada idanuwanta duk waje, she's not obeying hajiya kadijatu because she feels she's over faiz, tana Tunanin it's the right time tayi wulakanci da ranta ke so don ba lallai ta sake samunsu waje guda Haka ba, kou a Haka she feels happy, ahmed was just looking at Amira data Fara kuka, shi faiz sadda Kai kasa yayi Jin wannan kalaman iskanci, he didn't say anything because he wants ahmed to think of the worst so that ya bar mashi Amira kawai, yanda yayi shuru with his head down sai ki ranste da gaske bintu take irin kawai ta tona mashi asiri din Nan, Amira kallon ahmed tayi tace "Dan Allah... it's not...like that.. " "Dalla malama rufe mana Baki...shame on you...ba sai kin boye relationship din ba... because ni na hakura dashi...ni da budurcina nayi aure...ke Kuma da kuke watsuwarku har Malaysia sai aje ayi aure a cigaba daga inda aka tsaya..."bintu ta sake watsa mashi another hot words, ahmed Kam kasa Zama yayi, he was dying inside that he decided to leave, he have heard enough, , Amira kallon Hajiya kadijatu tayi tana cewa "Wayyo...na shjga uku..." Ta fada cikin kuka Sosai "Wai meke faruwa Haka ne...duk Kun barmu cikin duhu..." Hajiya Fatima that wants to dig into the issue ta fadawa Bintu "Mummy... wnanan banzan secretary din...suna watsuwarsu da faiz...mummy har kasar waje sukaje su biyu...itace sanadiyar rasa cikina..." Bintu ta fada Tana fashewa da sabon kuka, "Inna lillahi waina ilaihi rajiun..." Both sakina da hajiya Fatima suka fada inda ahmed ya Mike lokaci guda kaman walkiya ya bar dakin, Saidai sukaji anyi banging kofar da karfi, sai da ya fita faiz ya saki Ajiyan zuciya ya daga Kai with a smile Kan face dinshi, all this doesn't hurt him one bit, tace suna iskanci ai ba kansu farau ba, "Tir..." Sakina ta fada, "Hope you're happy... hankalin ki ya kwanta kou... nagode da Kika nunamin ban Isa dake ba... nagode Sosai Fatima..." Inji hajiya kadijatu, . "Ai wannan ba abun boya bane...in ba rashin kunya ba ya zaayi kana budurwar mijin mace Kuma kazo ganinta a hospital.. it's a total disrespect..." Inji hajiya Fatima that is siding bintu "Big disrespect.. "sakina tayi adding, hannun Amira hajiya ta rike tana Mika daita, Amira feels in Bata ce komai ba an gama daita, cikin kuka tace "You have ruined my relationship...but remember I didn't ruin yours...shi..." Ta fada Tana nuna faiz dake kallon yanda take kuka tacigaba da cewa "Shi yayi ruining... relationship dinku....banyi wani lalata da mijinki ba...Babu abinda ya Shiga tsakanina da mijinki....in har nayi lalata dashi Allah ya tozarta ni duniya da lafiya..." Ta fada yayinda kuka yaci karfin ta, Baki bihtu ta dinga tabewa alaman she doesn't care, "Shi yace Yana Sona...Kuma I didn't know...mu biyu kadai
Chapter 191 · 0% Book details