← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 225 OF 268

Sashe 225

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saida koina ya nutsu uncle abdulrahaman yace
"Yanzun meye abunyi...wane shawara kuke ganin ya dace...don tunda an San he is responsible Bai kamata ace ya barta haka Nan ba...kowa yasan cewa babu Wanda zai bar danshi yace zai aureta.... duk inda zata ma zagi zata jawa family dinmu...Amma yanzun na Bari kowa ya Fadi abinda ke ranshi.. " ya fada Yana kallon kowa da kowa har da alhaji Muhammad da tunda yazo Nan Babu abinda yake cewa sai kallon su kawai yake
"Ai kawai a hadasu...babu wani two ways about it.. " wanda ya fara magana Bai karasa ba alhaji Muhammad yace
"Baa hadamin ya da wannan shaidanin..." Ya fada breaking his silence,
"Why?..."alhaji abdulrahaman ya tambayeshi
"Because I said so...Baku ganin yaron Nan Baiyi min hallaci kou kadan ba... it's better yata ta zauna a gidana har tsawon rayuwarta da ta hada zuria da maciyin Amana irinshi...yaron da nayi nurturing baiji kunyata ba...baiji tsoron Allah ba...yayiwa yata Haka...." Alhaji Muhammad Bai Karasa ba wani yace
"The mistake is from both of them...ba Habib kadai yayi laifi ba...ita Amira data boye abinda yayi Mata taki Fadi fa?... both of them have to be punished...ba Habib kadai zaa hukunta ba..." Still wanda ya fara Magana Bai karasa ba alhaji Muhammad ya sake cewa
'"ban damu da duk irin hukuncin da zakuyi mata ba...kawai dai banso hada zuria da Habib..."
"We understand your pain.. " wani ta Fara fada Bai Karasa ba alhaji yace
"Non of you will ever understand my pain.. " ya fada cikin muryar dake Nuna he is in so much pain and agony
"Babu Wanda zai Gane halin da nake fiki ace yadon da na Raina ya rasa wacce zai lalata sai yata.." ya fada Yana dafe goshinshi Yana tsayar da maganar Da ya farayi as kuka na neman kufce mashi
"We understand...yaran zamani sai hakuri...kana naka suna nasu...all of us sun San kayi kokari da Habib, ai ni na raini Yar uwarshi Amma we all know you gave Habib what is I didn't give saudatu,..kayi hakuri..."
"Nayi hakuri....in banyi hakuri ba ya zanyi?...will that change anything?.." alhaji ya fada Yana murza idanuwa, ganin alhaji Muhammad is in a very bad mood yasa alhaji abdulrahaman yace
"Yanzun dai kowa ya tafi... Muhammadu kaje ka huce... zamuyi magana Nan da sati guda..."
"Aa...I don't need Time to heal...bana bukatar time to heal...kawai bana son jin maganar hada Amira da Habib...abinda ya faru is destined to be..."
"We know..." Alhaji abdulrahaman ya fadawa alhaji Muhammad cikin rarrashi, don yanda yake magana kasan dannewa kawai yake Bai kuka but he is broken to the core, it's like it happened today and not More than 4 years ago, inda wani Chan yayi zaifi mashi sauki sosai Amma kasan cewa Wanda is ciyar ka shayar ka tufatar sannan ka bawa muhallin da all the necessities of life yaci amanarka da zafi
"Yanzun dai zamu samu haduwa next week sai a San abunyi..." Alhaji abdulrahaman ya fada, Nan sai aka rufe taron da adua.
Amira Tana zuwa gidan ta fadawa mum dinta abinda ya faru da Kuma abinda taji uncle abdulrahaman ya Fadi, Idanuwa lumshe hajiya tace
"Hakan is the only way ai....in bashi ba ina Zaki samu mijin aure...kawai hakuri zakiyi..." Bata karasa ba Amira ta zube kasa tare da rike mum dinta Tana cewa
"Dan Allah mummy Kar ki ce Haka...Kar ki yarda a hadani dashi... ranar dayazo ya fadamin Yana da matar da zai aura a Lagos...nasan yayi aurenshi... wallahi I will rather die than to be married to him..." Amira ta fada cikin matsanacin kuka
"Hmmm kimayi adua ya yarda ya aureki...ai yanzun you're not like every lady out there...he is the father and the person beyond all this mess...so Baki da zabi...da ya wuce kije ki aureshi... you have no choice my dear..." Hajiya ta fada Mata atakaice tana goge face dinta.

Alhamdullilah
3/17/21, 8:35 AM - Ummi Tandama: 95💜🧡💚💙�
Dawn of a new beginning
❤💜💚🧡🤎�

9️⃣5️⃣

Amira ta Shiga bakin ciki sosai saboda maganar mum dinta, wato she have no choice than to marry habib, hakan is something that will happen over her dead body, she can never marry him. Fita tayi daga dakin mum dinta ta koma nata tana kuka, she have no body to tell sai Ahmed, hakan yasa ta dauki wayarta amid tears ta Kira Ahmed Yana picking ta fada mashi abinda ake fada, Ahmed wasn't too shock don yasan in har family Dinsu ne abinda zaayi kenan,
"Baby... hakuri zakiyi...Amma kinsan wannan family din kou akuya kayiwa ciki sai ka aureta...kin manta da labarin Khalid da akayi forcing ya auri Mai aikin gidansu kawai because he was teasing her Alot..." Ahmed Bai Karasa ba Amira dake kuka sosai tace
"Yaya... wallahi saidai in mutu....I will never marry him... wallahi it's better kawai in mutu..." Ta fada cikin matsanacin kuka
"Pls mutuwa is not an option...kindai San kou wani yazo yace zai aureki yanzun bazaa Bari ba...tunda har Habib is responsible for everything... it's part of the reason da yasa nace Kar ki Bari kowa ya sani a lokacin...I know something like this will come up..." Ya fada Mata cikin matsanacin damuwa
"Yaya tell me what to do...pls tell me.. " ta fada cikin matsanacin kuka
"Pls ki bar kuka...kin Dade kina kuka... stop crying Haka Nan...did you know if we care about our problems alot sai Allah ya barmu muji da damuwar mu?...Amma in har muka bar mashi komai zai zaba Mana abinda yafi alkhairi....in aurenki da Habib alkhairi ne..." Ahmed dake magna cikin zafin Rai da Bakin ciki Bai karasa ba Amira tace
"Pls Yaya Kar ka Ida abinda zaka ce....Habib can never be alkhairi to me.... remember what you told me about him... remember you told me he is a Casanova...Yaya zaka so ace na auri irin Habib?...Kar ka manta ka fada me he doesn't deserve me...Dan Allah Kar ka sauya Baki pls ...ka fada masu Habib na Neman Mata..." Ta fada Tana kuka kaman ranta xai fita, idanuwa Ahmed ya lumshe Yana Mai jin wani irin Bakin ciki, family Dinsu Yara Basu interfering a magnar manya, he doesn't have anything to say,
"People Change..."
"No pls...ka bar cewa hakan...nidai Yaya if you care about me...ka taimaka min... ka fada masu who Habib is...pls kayi min Rai..." Ta fada cikin kuka Sosai,
"Kar ki damu... zanyi komai yanzun don taimaka maki....zanyiwa daddy magana ..he pay listening ears...Zan fada mashi irin lifestyle din Habib..." Ya fada Mata cikin sanyimurya
"Ok tou...pls help me..." Ta fada relaxing a bit,
"Amma kinsan in har  aka yarda da maganata Ana iya cewa in har Baki auri Habib ba ki auri wani...tou ya kenan..." Ya fada Mata with another intention
"Yaya...kasan ban da wani..." Bai Bari ta karasa ba yace.
"You have Mana...kina da faiz...he loves you... maybe fiye da yanda na soki..." Amira data lumshe idanuwa tana hawaye cewa tayi
"Yaya...kasan I can't and you know why...kasan..."
"Baby he knows...yasna you have a son...." Ya fada Amma cikin ranshi, he wants to tell her he knows Amma zaiyi Shuru tukun
"Kasan bazai taba auren Mai yaro ba..."Amira ta karasa maganar ta
"Why not ki fada mashi why kike kinshi... maybe he will understand...kinsan mamanshi Yoruba ce...suna bawa mutane dama ba kaman mu da iyayenmu Basu ganin abinda ya faru da wacce zai iya faruwa da tasu ba...pls Talk to him..." Ya fada Mata Cikin sanyimurya praying she will just say ok, it's very difficult for him saying it Amma it's good to keep selfishness aside and do the right thing, Amira Bata San yanda zata fada mashi abinda ke zuciyar ta ba, she knows it's not going to work kou da kuwa kowa nashi sun yards ya aureta,
"Yaya...I can't....bazan iya ba... you're my only hope and you're gone..." Ta fada tana shesheska,
"Pls ki bar cewa...hope belongs to Allah...shi ke badawa a lokacin da bamuyi tsammani ba...Allah kadai yasan Wanda yafi alkhairi..."ya fada Mata cikin sanyimurya Yana kwantar Mata da hankali
"Yaya kawai bazan iya aure ba... imagine ka auri mace da komai second...faiz Yana da beautiful wife...kou zaman kishi bazan iyayi daita ba... she's totally different from me....he married her brand new.." ta fada tana tunanin ya zaayi ta auri namiji ya gan nononta ya rutsuna, ya gan under dinta open, she will rather die than ta auri namiji a ganta a wulakance,
"It doesn't matter...it doesn't matter at all...love conquers all...in har mutum na sonki zai manta da duk Wannan ya so ki don Allah...I loved you and would have still marry you Amma destiny Bai Bari ba..."
"Nidai Yaya pls Talk to Daddy...ka taimaka min kaji..." Ta fada mashi don ya daina maganar da yake Mata don taga it's of no use to her.
"Ok zanyi mashi magana..."ya fada Mata. Sallah tayi ta sake Kiranshi Tana fada mashi Kar ya manta ta fadawa daddy.
Chapter 225 · 0% Book details