← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 244 OF 268

Sashe 244

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habib Kam Bayan ya samu ya isa office din ahmed Suka gaisa, Kallon how disturbed he is looking Ahmed yayi ya tambayeshi what's wrong, ajiyan zuciya habib ya saki before yace
"Pls taimaka min zakayi...Ina cikin damuwa sosai...nasan I am the bad egg of the family Amma pls kayimin Rai..."
"Wai me ya Fara..." Ahmed ya tambayeshi Yana kallon yanda yake magana kaman ba arrogant and Casanova Habib ba
"Well it's about Amira...I know Kuna da kusanci daita...sosai...pls...I want to see her...Ina son muyi magana daita...Amma the problem is daddy yace Kar in Kara zuwa gidan shi...pls zaka iya tsayamin ka kiramin ita kou ka rakani office dinta muyi magana.." irin kallon da Ahmed ke mashi ya nuna Sam it's not possible, Habib Bai Bari Ahmed yayi magana ba yace
"I beg you...ba wani Abu zai kaini wajenta ba...I want to ask her for forgiveness...she haven't told me she have forgiven me.... sannan Ina son in nemi second chance.. "da sauri Ahmed yace
"Lallai ma.... you're very funny...irin she's made for you alone din Nan...wato tunda Kai ka watsata Dole Kai zaka aureta...or in ba Kai ba nobody will come for her again. ." Ahmed ya fada cike da takaici,
"Aa...ba Haka bane....kawai I feel if she wants to be happy...we should be together... it's not all about abinda ya faru a tsakanin mu... it's about how I feel kanta... wallahi inason Amira.... she's my first love...rudan duniya ne yasa na kasa tantancewa sai yanzun..."Dariya ahmed Daya San halin Habib ya saki cike da haushi yace
"Su first love manya... wato she's your first love Amma ka dinga jumping from one woman to another...ka dinga shiga Nan Shiga chan...well let me break it down for you... you already loose her....Amira is getting married very soon...Kuma kasan wa zata aura?...he is the son of alhaji haruna labaran....am sure you know who am talking about..." Ahmed ya fada Mashi, Habib kallonshi yayi Yana tunanin it's not possible at all, yasn bazai taba yuwa ba with her former life she can't be with another that knows her secret sai kilan baa fda mashj ba, budan bakinshi saj cewa
"Hope you're joking...nasan Wasa kake min... you just want to pull my legs..." Ya fada cikin little damuwa
"Kasan bamu irin wannan Wasa da Kai ai...am serious..."Ahmed ya amsa mashi
"Mmmm Amma baa fada mashi gaskiya ba kou....baa fada mashj she have a son for me ba..."
"He knows...but he loves her...so kawai kaje ka zauna ka huta... just go and look for something to do and keep asking Allah for forgiveness...kilan ya baka wata Nan gaba..." Ya fadawa Habib Daya duk jikinshi yayi Sanyi, yasan kou da bakin cikin son da yakewa Amira aka barshi an Gama dashi, yasan it's a very huge punishment for him a barshi da kaunarta bayan wani ya aureta
"Inna lillahi waina ilaihi rajiun..." Ya furta under his breath
"Zancen asking for her forgiveness kawai kaje ni zanyi Mata magana....I know she won't want to see you..." Ahmed ya fada mashi
"No pls...kawai ka taimaka min...I want to see her...I want to talk to her...I need to speak to her...Dan Allah ka taimaka min nasan tana Ganin mutunci ka..." Habib ya fada kaman zaiyi kuka
"Kaida akace baa sonka a gidan ya zaayi ka ganta...Ina zaka ganta in ba gjdansu ba...I won't voilate rules din Daddy because of you...."
"Pls kou ba aa gida bane...I want to see her...pls ka rakani office dinta... I need to talk to her Dan Allah..."Habib ya fada Yana kokarin sauka daga Kan kujeran da yake zaune Yana cewa
"You're my only hope now... Kai kadai nake dashi a wannan family din...I beg you kayi min Rai..." Habib ya fada yana kneeling
"Pls ka tashi...ka tashi... yanzun dai da akwai abinda Zan iya promising dinka...I will talk to her first...don bazan kaika office dinta without telling her ba...ban son a sake samun matsala at all..." Ya fada mashi
"Ok...a hakan ma na gode...pls call her now..." Habib Daya koma ya zauna ya fada sounding so tensed, he feels in yayi magana daita zata iya yarda, he knows Amira ta damu dashi too that duk abinda yayi Mata she will surely come around if he keeps
Begging her she will listen to him, he feels babu Wanda Amira ta dace dashi sai shi Kanshi, he knows he will give her all the care he needs,
"Ka Bari tukun ai I promise I will talk to her..."..
"Pls I beg you talk to her now... Start now...pls.."ya fada sounding so anxious, babu musu ahmed ya fidda wayarshj ya Fara Kiran Amira but unfortunately Bata dauka ba because tana gidan gona, sau biyu ya Kira Bata daga ba,
" Ka dai ji Bata daga ba...so you will have to let me call her...nasan she will call me back in ta gan miscall Dina..." Ahmed ya fadawa Habib da duk ya damu, shi dai Habib ba Haka yaso ba, yaso ace ya sunyi Magana daita. Bai da choice ya Mike sukayi sallama ya fada mashi he will keep calling don yaji yanda sukayi daita,.

Faiz Kam bacci sukasha Bai Farka ba sai wajen karfe uku, da sauri ya Mike har towel dinshi na faduwa ya Shiga bathroom Bayan kaman minti goma ya fito da alwallah, har lokacin bintu na kwance, Kaya ya saka ya dauki wayar yaga kou Amira ta Kirashi sai yaga Babu miscall dinta kou Daya, hakan ya Dan motss mashi Rai
"Daman Baki damu ba..I know you're managing me..."ya fada Yana maida wayar ya ajiye, sai Kuma ya kasa da zai fita sai ta dauki wayarshi, still Yana zuwa falo sai yayi tunanin Bari ya jira yaga kou zata kirashi, haka yaje yayi sallah ya dawo ya sake duba wayar yaga Babu miscall dinta still dai na wasu workers dinshi, yanda ranta yake bace Haka nashi ke bace, he feels at least ta kirashi taji why Bai zo ba, daki ya shjga ya tsaya Yana kallon bintu dake kwance, she's sleeping so peacefully, ahankali ya taka zuwa wajen ta ya Dan tabata yace
"Tashi kije kiyi sallah.." ya fada atakaice Yana fita daga dakin, wayarshi ya dauka yayi dailing number ta, har ya Gama Ringing baa dauka ba kasancewan Bata je gidan gona da wuri ba Kuma it's very far,
"Oh she's not even picking...hmmm lallai ma.. "ya fada a zuciye Yana ajiye wayar, he feels so bad and he is not only mad at her har da bintu, sanda bintu tayi sallah ta fito gave dinshi Babu walwala at all, ya gumke like he use to do, daman dsurewa is among his hobby don Haka Bai jin euya ya sauya cikin Dan kankanin lokaci, bintu na Ganin yanda ya sauya ta Sha jinin Jikinta, tasan he is angry, tana Zama ya kalleta yacr
"Ya jikinki..." Ya tambayeta Kai tsaye
"Da... sauki "ta amsa mashi Kanta kasa, can I go out now?.." ya fada Mata Kai tsaye like he is asking for her permission Amma Sam ba Haka bane,
"Ok..." Ta amsa kasa kasa sannan tayi adding
"Ai I feel better..." Ta amsa mashi,
"Me zakici..." Ya tambayeta sounding caring Amma face dinshi kaman Bai taba Dariya ba
"Am not hungry..." Ta amsa mashi, Mikewa yayi ya shjga Shiga ciki Yana cewa
"When am coming back Zan taho maki da favorite dinki..." Ya fada Mata Bai jira amsar ta ba ya shjga ciki don ya sauya Kaya, he is Rushing ba don komai ba sai don ya tarda Amira office, he knows in baa office ya tardata ba in gida ne he won't do her the way he wants to do her right now, Yana son ya fada Mata duk sanda Bata ganshi ba she should call and show she cares about him bawai ta dinga jiranshi ba, he wants to tell her ta dinga nuna mashi so kou da kuwa Bata sonshi, Yana fitowa ya dauki keys Dinshi ya fice kawai. Bintu dake zaune sai taga Sam her plan didn't work and doing it again won't even help, gashi ta hanashi zuwa wajen aiki don Kar ya ganta yanzun Kuma he is going to see her. Ajiyan zuciya kawai ta saki tace
"Na hakura...kou ba Komai he shows he respects me...let me not ruin that..." Ta fada cikin sanyimurya. Fajz na fita ya kalli agogo yaga kusan 3 da rabi, he just pray Kar ta bar office kafin ya iso.
Amira Kam zuwa gidan gona really help her Alot, she didn't have much time to think again, she was going through Daman zaka Bata a kalla hour guda da Yan mintuna Kan hanya wajsb zuwa da dawowa, kafin ta dawo daga gidan gona uku ya wuce, she took her phone and saw his miscall, Bai Dade da kiranta ba, Baki ta tabe taga shima ahmed ya kirata, number shi tayi redialing Yana picking Suka gaisa, Nan ya fada Mata he called and she told him ta leka gidan gona ne, Hira suka Dan taba ta tambayeshi hope ba wata matsala yace
"Ina son muyi magana...Amma ki Bari zanzo gida anjuma..."
"Yaya what's the problem..." Ta fada
Cikin damuwa
"Aa nothing serious...wata alfarma nakeson inzo nema ne ma ne.." ya fada Mata
"Alfarma wajena Kuma Yaya...well ka sani kou meye it's done...ka wuce ka nemi alfarma wajena... you're above that...kou me kake so is done..." Ta Fada mashi, dariyar farin ciki ahmed ya saki yace
"Ok sai mun hadu...Kuma na gode da karammawa. "
"Kafi karfin godiya Yaya... yanzun dai sai kazo...Inason in Yi sallah Nima in tafi gida..."
"Ok...Ina fajz..."
"Yaya yau vaizo ba..."
"Why what happened..." Ya tambayeta
"Nima ban sani ba..."
"So you didn't call him..."
"Yaya ka mance Yana da Mata?...i.cant just keep calling him to ask if he is coming or not...Kar in dinga batawa matarshi rai..."ta fada ranta bace
"Gaskiya hakan Bai kamata ba..."
"Nidai Yaya gaskiya am feeling I can't do this..."
"Pls don't say that...pls..."ahmed ya fada Mata as ya gane inda ta nufa
"Yaya in kazo zamuyi magana..." Ta fada mashi
"Ok...Amma maganr you think you can't sam bai taso ba..."
"Hmmm Yaya kenan...kawai sai kazo..." Ya fada sukayi sallama. Ajiye wayar tayi ta shjga bathroom din nan office dinta.
Chapter 244 · 0% Book details