← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 268

Sashe 201

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wajen karfe biyar ahmed yaje gidan su Amira, hajiya was so happy to see him wato mahaifiyar Amira, kowa sai sannu da zuwa suke mashj, even little nasir yayi Missing dinshi sosai, he hugged him, daukanshi yayi ya shjga dakin Amira rike dashi, Yana bude kofsr Amira dake kwance ta bude Ido, ganin ahmed ne yasa tayi Saurin mikewa, he sees yanda ta rame, wato Amira Bata son tashin hankali kou kadan as it easily shows itself on her, yanda ta rame shows ta Shiga damuwa sosai,
"Yaya..." Amira da ta kasa boye farin cikinta ta fada tana mikewa zaune,
"Na'am ..." Ya fada Yana Zama a wajen zaman shi wato stool din mirror, Amira sai gyara Zamanta take looking so excited, all she feels is ya yafe Mata tunda har yazo gareta, she's so happy he is here, it's like all her happiness is back again,
"Ya bayan saduwa..." Ahmed ya fada with a smile Kan face dinshi Yana kallon yanda ta sadda Kai kasa with a smile,
"Lafiya...Lau Yaya...ya aiki.. " ta tambayeshi,
"Lafiya lau...ya naki aikin.. " ya tambayeta, shuru tayi Bata amsa mashi ba sai Wasa take da yatsunta,
"Baki amsa ba...I said ya aiki..." Ya tambayeta
"Nayi.... resigning..." Ta amsa mashi kanta kasa..
"Resigning...why... saboda me..." Ya tambayeta
"Kawai...I want to prove... myself to... you..." Ta fada kanta kasa
"Haba ai hakan rashin hankali ne...ya zaayi ki bar aikin da ake biyanki hundred if thousands just to prove yourself... yanzun dai ki koma aikinki...." Ya fada atakaice
"Yaya...I don't want to..." Bata karasa ba yace
"Nace ki koma bakin aikin ki..." Ya daka Mata tsawa,
"Yaya... resigning nayi....nasan sunyi replacing dina..." Ta qmsa mashi Still not looking at him
"Kawai go back...sai in dai ban Isa dake ba..Kuma why layin ki Bai zuwa...kou kin daina business din ne..." Ya fada Mata, da sauri ta Mike ta bude inda ta ajiye wayar ta for very long ta dauko shi, kunnawa tayi
"Yanzun Ina son ji...when Zaki komai office..." Ahmed ya fada Mata cikin iko
"Zan koma.... Allah yasa su amshe ni...." Ta fada kanta kasa.
"Good...Allah ya taimaka..." Ya fada Mata Yana mikewa, sai da ya gama Mikewa yace
"Zan tafi...am just coming from office ban Isa gida ba..." Ya fada kaman kawai he came to tell her to go back to office and nothing more, da sauri itama ta mike tace
"Yaya..." Ta kirashi cikin sanyimurya
"Naam..." Ya amsa Mata atakaice Yana kallon ta
"Pls...ka yafemin?... Wallahi duk abinda ta Fadi karya ne..." Ta fada kanta kasa
"Amira in Banda abunki...tunda nazo inda kike ai kinsan am ok...Allah ya yafe Mana asiri..." Ya fada Babu any feeling kou sanyin lafazi kaman yanda ya Saba Yi mataz she still knows something is wrong don ba Haka yake Mata ba, shi kanshi Ahmed ya kasa sakij jiki daita kaman da, yasan if ya saki jiki da ita kadan zai iya koamwa gidan jiya, hakan yasa Bai sake Bata lokaci ba, sannan ya kasa fada Mata maganar aurenshi, he feels in har ya fada Mata yanzun Bai kyauta ba, she's so fragile, kawai zai bari lokaci ya fada Mata
"Yaya...da gaske Kake...ka yafemin...I don't feel it..." Ta fada mashi
"Amma you heard it ai..ai Shine all that matters... yanzun dai make sure kin koma aikinki gobe...am I clear?..." Ya fada Mata
"Yes..."
."good." Ya amsa Mata Yana juyawa, da sauri ta dauki hijab tabi bayanshi yayinda shi kuma ya fita rike da nasir sai Wasa yake mashi, sanda ya dawo falo Babu kowa, dire nasir yayi tare da juyawa ga Amira yace
"Nidai Zan tafi..ki gaida su mummy..." Ya fada Mata daga Nan falo Alaman Bai son ta rakashi unlike before da har complain yake Kan Bata son raka shi in yazo,
"Yaya...Bari in raka...ka.." tafada cikin sanyimurya, Bai sake Cewa komai ba ya shige mata gaba ita Kuma ta bishi, Yana sauri har tqzara ya Shiga tsakanin su sosai, tsayawa kawai tayi tana kallon shi ya juyo bayab ya bude mota ya sakar Mata murmushi ita Kam Bata maida mashi martani ba because this is not how Ahmed dinta ke behaving, hannu ya Dan daga Mata bayab ya Shiga Mota, duk yanda Amira ta damu Bata Kai ahmed damuwa ba, seeing her raise that flame again Amma Bai son ya sake tadawa kanshi hankali, not after ya nemi yafiyar mum dinshi, Haka ya tafi Yana kallon Amira dake tsaye. Dakin mom dinta ta Shiga ta fada Mata yanda sukayi da ahmed, .
"Alhamdullilah...naji Dadi Daya dawo...sai ki Shiga hankalin ki Kuma..." hajiya Ta fada Mata,
"Hmmm ...mummy... behavior dinshi ya sauya sosai...kaman ba shi ba ...' Amira ta fada cikin sanyimurya
"What did you expect...ai ba lokaci guda zai dawo Kanan yanda yake ba... ahankali zaa koma gidan jiya.. " hajiya ta amsa Mata, hakan yasa Amira taji sanyi cikin ranta. Tayi tunanin insha Allah zasu karq komawa daidai
"Amma mummy kina ganin...zaa amshe ni a office...I have been away for a while....Kuma resignation latter na bada..." Ta fada kanta kasa
"Sai ki gwada ki gani...ai aiki irin naki ba abun Wasa bane,..." Hajiya ta amsa Mata
"Gobe in Allah ya kaimu... zanje wajen alhaji...in fada mashi I want to come back... muji if zai yarda..."
"Ba wajen alhaji Zaki ba...wajen oganki Zaki...ai he is the one that gave job in the first place..."hajiya ta fada Mata, shuru tayi Tana tunanin ganinta a gaban faiz and tana mashi magana, kou kadan Bata son sakashi a Ido, he is so annoying, she still remembers the behavior he display ranar da bintu take masu sharri, rashin maganar da yayi is the main reason of her anger, Zama yayi with his head down irin she's totally speaking the truth, sannan yayi Mata Rami, she begged him yanda ba saj sun je ba yace it's going to be alright, it's all a lie, ta tsani yaudara, Bata kaunar mutum ya yaudareta, fajz is the main cause of abinda ya Faru tsakanin ta da ahmed,. Bata dai Kara cewa komai ba.

Wace gari ta shirya ta tafi office, office din faiz ta nufa wayanda ke aiki wajen sai oyoyo suke Mata, she have a very good working relationship with with them hakan yasa da Basu ganta ba duk suna tunanin faiz yayi halinshi,gashi Basu da number ta, and they can't ask the boss, tana shjga office din faiz secretary dinshi tace Bai Nan, Bai zo ba. Secretary dinta ta bawa number ta ta fada Mata in faiz ya dawo ta kirata ta fada Mata she wants to see him. Gida ta koma hajiya na asking dinta how it went ta fada Mata ta koma dakinta.
Chapter 201 · 0% Book details