← Book details Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 268

Sashe 221

Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda Amira ta sako Kaya ta fito Ahmed ya fada Mata cewa ya Kira Ismail Kuma yace an watse that yanzun suna Kan hanyar dawowa gida don hakan tayi hakuri kawai ba sai taje ba, ba Wai yayi waya da ismail ba Amma Bai son ta koma. Babu musu tacr mashi ok, ciki ta koma yayinda shi Kuma Ahmed ya tafi gida. Kafin su Hajiya su dawo har Habib da yayarshi sun iso gidan, dakin maigadi yaje ya zauna Yana jiran a hukunta shj, yasan it's going to be very serious. Yayarshi ta zauna waje don har lokacin Bata daina kuka ba, ismail na parking hajiya ta fito tana hawaye Because finally ta Sami Daman kuka that she have been hiding, kou ganin Yayar habib batayi ba ta Shiga ciki, direct dakin Amira dake kwance tana tunanin ahmed yayi Mata wayau Bak kaita ba don Saida ta kusa hour biyu gida it's kadai suka dawo, Ana bude kofsr ta Mike zaune itama tasan yau da akwai magana, Tana ganin Mom dinta  ta da face jike da hawaye ta mike tsaye,
"Amira...fadamin abinda kika fada a wajen reception... tell me it's a lie..." Hajiya ta fada tana kuka, Amira that sees no reason to cry komawa tayi gefe tace
"Am sorry... gaskiya ce..." Ta fada kanta kasa tana Wasa da yatsunta praying yau Kar a bigeta
"Gaskiya ce?...Amira gaskiya ce... you mean Habib yayi maki ciki Kika kasa fada min..." Ta fada cikin kuka, Nan Amira ta fadawa hajiya komai tana cikin fada bakin ciki yasa ta fara kuka itama,  hajiya Dora hannunta tayi bisa Kai tana kuka, ismail na tsaye a bakin kofar dakin Yana jinsu, he can't just believe Habib did this to his sister, he can't believe Amira took all pains because of him and Still ya dawo Bai aureta ba, a duniya yanzun Bai da makiyi kaman Habib, he hates him with passion, Yana fita ya ci Karo da Yayar habib kou kallon inda take baiyi ba ya wuceta dukda ta girmeshi, hajiya na kuka ta fito daga dakin Amira sister Habib na ganinta ta durkusa kasa itama tana kuka, she was crying so Loud saying she's sorry Bata San hakan ya faru ba, hajiya couldn't say a thing, ganin Yan reception sun Fara dawowa yasa ta koma gefe. Sai da nazifa ta dawo gida ta gane abinda ke faruwa, taci kuka kaman ranta xai fita, she remembers yanda yake fiye da elder brother a wajen su, kukan nata ya Zama biyu ga na tafiya gidan Miji ga Kuma na Bakin ciki abinda Habib yayiwa Amira. A Chan family house din alhaji Muhammad Kam duk sun Hadu kowa na fadin albarkacin bakinshi, kou kala alhaji Muhammad bai ce ba because he is totally speechless, at long last suka yanke hukuncin a Kira Habib da Amira don a sake tabbatar da magana don wasu suna ganin it's not possible that Habib bazai iya hakan ba, Kiran Yayar habib akayi Kan ta fadawa Habib yazo inda suke, aka Kuma Kiran ismail ya zo da Amira,. Yayar habib fita tayi don Kiran Habib yayinda shi Kuma Ismail ya fito don Kiran amira Yana Kiran Amira ya fito ya ci Karo da Habib da Bai San Yana dakin maigadi all this while ba, wani Irin kukan Kura yayi ya nufeshi a guje

Alhamdullilah
3/15/21, 9:12 AM - Ummi Tandama: 62

Yanda ismail ya taho Habib Bai sani ba sai dai yaji wani irin naushi a Cikin shi, irin force din da Ismail yayi using yasa Habib ya fadi kasa wanwar lokaci guda, Habib Saurin boye face dinshi da hannunshi dake da ciwo yayi ya kudundune kasa yayinda ismail ya dinga harbinshj da kafa ta kowanne Angle, Yayar habib ce ta rike ismail Amma Sam yaki rukuwa
"Butulu....azzalumi....Dan iska...tsinanne...Allah yaisa..." Ismail ya dinga Fadi Yana Harbin Habib ya koina, ihu ya sake cika gida tunda har Yan daukan Amarya sunzo matan kokarin rike ismail suke Amma kou an janye shi daga gareshi before Habib ya sake Mikewa ya sake Kai mashi duka, duk jikin habib ciwo yake mashi sabida duka, dukda Yana boye kanshj sabida bakinshi Saida Ismail yayi nasaran Kai mashi duka guda bakinshi Wanda yasa ya saki ihu, Gam maigadi ya rike shi da karfin da Allah yayi mashi Amma Still ya tureshi, duk dukan da zaiyiwa Habib sai ya hada da zagi, Amira da Ismail yaje Kira ta fito taga abinda ke faruwa gefe daya ta tsaya Yana kallon su, she just feel a bar Ismail, haushin masu rike ismail kawai take ji, she hates this guy on the floor to bastard, Bata kaunar Mai kaunarshj, yayarshi da taga duk an kasa rike ismail ta shiga ciki da gudu yayinda Daman asiya tana gaban hajiya Tana cewa
"Mummy...ga Yaya... Chan...zai kashe Yaya...Habib..." Take fadawa hajiya da hawayen face dinta yaki bushewa, sai zuba kawai yake second by second, kawai tunanin how she treated this boy like her own son take, how she pampered him, give him money, give him freedom that Yana shjga koina na gidan, Bata tabayi mashi barrier ba, Bata taba hanashi shjga wani wajen a gidan ba, he walks freely, Amma ya Zama Wanda zai cuceta ya dasa Mata bakin cikin da har ta mutu bazai taba wankuwa ba a zuciyar ta, duk maganar da asiya take Mata Sam Bata ji, hankalin ta na Chan wani wajen, she's thinking so deep, wato da gaske Wanda ka taimaka Yana saka ka a wani irin Hali Haka, wato ka saka mutum a inuwa shi Kuma ya fiddaka Rana, Asiya was busy calling her Amma she was staring at same spot Bata kou blinking,da gudu Yayar habib ta shigo tana Kiran
,"Hajiya.... hajiya...kiyi Mana Rai... kiyiwa Ismail magana...Kar ya kashe shi...Habib yayi nadaman abinda yayi Dan Allah..." Ta fada cikin ihu tana kuka,maganar ta ya maido hajiya cikin hayyancinta, ahankali ta daga Kai Idanuwa cike da kwalla, Nasir na tsaye gaban hajiya dake kuka, sai kallon face dinta yake babu bakin da zai tambayeta what's up, ahankali hajiya ta Mike ta fita Nasir yabi bayanta, Yayar habib kallonshi tayi Tana kuka, dukda Ana cewa da Amira yake kaman she sees her brother, resemblance dinshi da kaninta yafi nashi da na Amira, she just wondered yanda akayi baa sani ba, don ita Bata gan abinda zaisa ba zata gane Dan Habib bane all this while ba,kawai dai Bata taba ganin yaron ba sai yau, duk sanda zata zo Gidan Bata ganinshi, hannunshi ta rike suka fita waje da sauri yayinda ismail was still busy punching habib kaman his life depends on it, da sauri hajiya ta fito taga abinda ke faruwa, before hajiya tayi magana Amira tayi Saurin riketa tana cewa
"Mummy...ki kyalesu.... just leave him..." Ta fada tana rike hannun mum dinta, fixgewa hajiya tayi ya kalli Ismail tace
"Ka Bari..." Ta fada mashi,still Ismail Bai daina ba don sai ka rantse shine victim di sabida yanda yake fada, he is so hurt and angry right now that in har Baa hanashi ba he won't stop fighting, he won't stop until yaga he is not moving anymore, so yake ya bazar dashi har lahira
"I said leave him!!!.." ta saka mashi
"No!!!" Ismail ya fada cikin anger, ita kanta hajiya Bata San Yana da irin wannan fushi ba sai yau, she have never seen him cry, Yayar habib sai kuka take tana yarfa hannuwa tana dorasu bisa Kai tana cewa
"Dan Allah Kar ka kasheshi...ka barshi Dan Allah..." Take fada yayinda take kuka Sosai, da sauri Hajiya ta isa Wajen Ismail ta jashi da karfin ta, kwacewa yayi Yana cewa
"Mummy let...me kill him....gwanda in kasheshi ayimin...daurin Rai da Rai..."
"Aa...barshi da halinshi... barshi Allah ya saka Mana amanan mu dayaci...ka barshi duniya yayi judging Dinshi..."ta fada tana janshi, Habib na kwance ya boye kanshj recieving all the punch that comes to him, inda zaa fadawa Amira she can watch Habib bleed sai ta ranste bazata iya ba Amma dayake iya daidai yanda ta soshi Haka take kinshi she won't mind a bar Ismail ya kashe shi, she won't mind watching him bleed to death, da kyar hajiya taja Ismail daga Kan Habib dake Nishi da kyar feeling more pain that he ever felt a rayuwar shi, he feels in har ya rayu with the pain he is feeling then he is really given a second chance, Ana barin shi Yayar shi ta rike shi, still bakin fara zubar da jini, Yana mikewa zaune ya zubda jinin bakinshi ya bude idanuwa da kyar, dukda gari yayi duhu he can see his son staring at him while he is holding someone, ahankali ya daga Kai yaga it's Amira, Kura Mata Ido yayi Yana kallon ta yayinda ita June take mashi wani irin kallon tsana da zallah kiyayya, ahankali ya sadda kanshj kasa, duk yanayin shi ya sauya, Ismail dake tsaye Kallon shi yayi yace
"Ka sani this will continue...duk sanda muka hadu da Kai...duk inda muka hadu da Kai...theFight continue.... wallahi in Kai Dan iska ne sai my nuna maka ni Mai cinuwar Yan iska ne...." Ya fada Yana barin wajen, part dinshi ya koma ya sauya Kaya ita Kuma hajiya ta koma ciki leaving Amira da danta waje, ahankali yayarshi ya rikeshj ya Mike zaune Yana zubda saliva Yana goge hawayen face dinshi, sai kallon Amira kawai yake, he still sees hate, he sees anger, Ismail na fitowa Suka Shiga Mota zuwa inda ake kiransu.
Chapter 221 · 0% Book details