Sashe 40
Dama Ta Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi ta saki tace "Yaya Zan dinga adua...kawai Allah Kar yasa su hanaka zuwa wajenmu...Kuma in da alkhairi a aikin Allah yasa su yarda..."ta fada mashi calmly, "Amin...Bari in dawo..."Ahmed ya fada Mata ya nufi kofar, Nasir ne ya Mike shima ya Fara binshi bakinshi duk ice cream,juyawa yayi ya kalleshi before yace "Kana zuwa wajen grandparents ne?..." Ya fadawa Nasir dake rike da robar ice cream da cokali,yaron tsayawa yayi Yana kallon shi Yana licking cokalinshj duk cheek dinshi ice cream ne "Taho mu tafi..."Ahmed ya fada mashi Yana mika mashi hannu, da sauri ya karaso ya rike mashi hannu, Amira da kanta ke kasa cewa yayi "Yaya...da ka barshi...Kar ka tafi dashi...."ta fada mashi calmly "Why...Bari in tafi dashi..." Ya fada Mata Yana goge bakin Nasir, "Aa..Yaya ka barshi pls..."ta fada tana mikewa ta Kama mashi dayan hannunshi, kallonta Ahmed yayi yace "Wai me yasa...kou rowar danki zakiyimin..." Yafada Mata, Kai ta Fara girgiza mashi kaman kanta zai fita saboda yanda take girgiza shi tana cewa "Yaya...ba Haka bane....ban son su...koreka...sabida...shi...."ta fada kaman zatayi kuka still shaking her head,da sauri ya Kama soft cheek dinta da two palm dinshi Yana cewa "Stop that...Kar kanki yayi maki ciwo..."ya fada Mata calmly Yana rike da kumatunta ta da hannuwanshi masu taushin gaske, "Bazasu koreni saboda shi ba..." Ya fada Yana kallon zaran zaran lashes dinta dake lumshe, Haka Nan she feels like pouring little bit of tears, Bata San abinda ke damunta ba exactly, "Zasu iya korar ka....banson....su Hana aikin... ganinshi Yana munana masu Rai...Dan Allah Kar kaje dashi..." Ta fada hawaye na rolling daga closed eyes dinta, tsaya kallonta kawai Ahmed yayi yanda in few seconds sai ta sauya to another person, it seem her Life have many pages she can easily turns to, Sam Bai gan abun kuka ba Amma now she's she's crying,. "Ki daina..."ya fada Mata cikin sanyimurya Yana cire hannunshi daga kumatunta, da sauri ta saka Bayan hannunta ta goge hawayen da suka Fara zubowa, hannunshi ta saki ta koma baya ta zauna bakin gado, Ahmed rasa abinda zai fada Mata yayi kawai ta fita rike da hannun Nasir, shi dai he yasan what will be will be nor matter the circumstances, in har da rabon tayi aikin then she will, as he was going out sai ya Fara tunawa da who he wants Amira to work with, "Faiz..." Ya furta under his breath, yasan faiz is not a womanizer so Bai da matsala da zai takurawa Amira sexually Amma yasan ba mutunci gareshi ba and he knows zai dinga raga Mata sabida shi but he will make sure in har Amira ta samu aikin she should abide by his rules and regulations yanda bazasu samu matsala ba, zai Bata good guidelines da zata bi da zasu zauna lafiya without single problem, yasan halinshi da kyau, he can count 50 attitude na faiz, yasan he is extra stubborn and hardly take correction saidai in yayi niyya, he knows in har Amira ta Bata mashi Rai he won't hesitate to manhandled her don ba kunya gareshi ba but the good thing is Amira on the other side Bata da matsala, with her kind of calm attitude tana iya zama da kowa. Ahmed na da Nasir ya Shiga bangaren Ismail don he thinks it's better ya fada mashi what's going on, Ismail na ganinshi da Nasir yaji wani irin sanyi cikin ranshi, hannu ya Mika mashi da sauri Nasir ya koma wajen ismail because they close, asalima Ismail yayi naming dinshi Nasir, shi yayi mashi huduba, "Habibi....Mai Kama da mummy..."ya fada yana dorashi Kan legs dinshi, "Aikam kaman su is so remarkable...kasan ikon Allah ne Wanan abun... such children na zuwa da resemblance din waynda Sukayi laifin amma nashi sai yazo Dana mahaifiyar shi...kaga babu yanda zaayi a gano mahafiinshi..." Ahmed ya fada Yana kallon Nasir that looks just like amira, "Hakane amma have you ever looked straight into his eyes... idanuwanshi bana Amira bane ba...his eyes are so different but so familiar to me..." Ismail ya fada Yana kallon Nasir,shima Ahmed kallonshi yayi ya kura mashi Ido yace "Yes....I see it..irin idanuwan Habib gareshi..." Da Sauri Ismail yace "Yes... exactly...they have same eyes...kasan shima jininmu ne...so the resemblance can come from anywhere...."ismail ya fada Yana kallon yaron dake Wasa a Kam kafarshi, "Hakane...ni yanzun ma sai Naga Yana Kama da Habib din ma.... anyway...wata magana naso na rakani wajen su daddy in fada masu" da sauri Ismail ya gyara zamanshi thinking it's what he is expecting, wato maganar auren ne zai fada,. Nan Ahmed ya fada mashi what he have in mind, Ismail was so surprised by what he said, "Aiki Kuma.... Amira as a secretary?...anya zasu yarda kuwa...nasan hakan zaiyi kyau sosai Amma da wuya su yarda... Ni wallahi da kace you want me to escort you I was thinking something different wallahi..."Ismail ya fada mashi "What were you thinking tou..." Ahmed ya tambayeshi, "Ai kawai I was thinking you want to talk to them about marrying her...Naga Kuna da kusanci sosai...I thought wallahi you're In love with her..." Ismail ya fada don jin abinda Ahmed zaice "Hmmm Wallahi Dan uwa Ina son Amira sosai...I love her passionately...Dana dawo tausayin ta Kuma yasa son da nake Mata ya karu sosai...aure ai nufin Allah ne....if da rabo a tsakanin mu then insha Allah I will marry her...kou kadna ban jin Zan iya cewa I won't marry her because of her situation..." Sai Kuma yayi Shuru thinking if he should tell him abinda mum dinshi ta fada game da ita or yayi shuru "Then why are you waiting...why kakeson tayi aiki if really you want to marry her..."ismail ya tambayeshi Yana kallon yanda ya sadda Kai kasa, shidai Ahmed feels he is like a hope to them don he sense that a yanda Ismail ke Magana and har ga Allah he doesn't want to make that hope go away, "Zan aureta...Amma kasan ban Dade da Fara aiki ba...nasan gida zaayi min komai but I want to have enough yanda Zan iya kula da ita da Nasir... before Allah ya bamu wasu yaran..." Ya fadawa ismail sounding so real, if you see how happy Ismail is sai kayi mamaki, ya nuna farin cikinshi karara,. "are you real?.."Ismail ya fada cikin serious excitement, "Muna irin wanann Wasa da Kai ne...na fada maka future plan Dina ne...Allah na gani banyi niyyar fadawa kowa wannan ba...kou kadan I want it to be a surprise...Kuma Allah na ganin ban son matar da Zan aura Bata aiki... we're in the era da duk kudin namiji Yana bukatar tallafin matarshi...."Ahmed ya fada cikin ranshi Yana aduar Allah yasa abinda ke ranshi ya Zama gaskiya Kar ya kasance karya yake masu, yasan shi deep down he meant all he said Amma his mom won't let it come to pass "But wani hanzari ba gudu ba...kana ganin su mummy da daddy zasu yarda...am thinking da kyar su yarda..."inji Ismail "Haba...sai ince Zan auri Amira kanwata suce aa... gaskiya nasan they won't say no...so relax.. yanzun dai zo ka rakani wajensu daddy...ka tayani da aduar Allah yasa su yarda ta Fara aikin..."ya fada mashi Yana kokarin mikewa, "Ai in kaje...ka fada masu you want to marry her but before you settle down Kama son ta fara aiki... kuma tell them zaka dinga kaita kana maidota...Kuma in kukayi sure zaka saka ta makaranta... believe me they won't say no to you...zasu yarda ..." Goshi Ahmed ya dafa thinking he is taking this to far by telling them what Ismail said, sadai Bai da zabi, "Amma baka ganin daddy zaice why not suyi maganar da wanshi sai Kuma ni Zan fada masu...ban son abinda zai sa suce na Raina su.." Ahmed ya fada cikin sanyimurya "Aa ba zancen raini...zaka fada masu ne ba don komai ba sai don kawai su yarda...don wallahi nasan babu Wanda zai yarda Amira ta sake fita waje...but with the point I have given you da gudu zasu yarda..." Ismail ya fada mashi, ajiyan zuciya Ahmed ya saki looking bit disturbed yace "Ok...Allah yasa Kar suce na Raina su... yanzun muje mu gan abinda zai biyo baya..." Ya mashi, "Ok da yaron zamu?.." Ismail ya tambayeshi Yana mikewa rike da Nasir, "Yes..." Ahmed ya fada mashi Yana mikawa yaron hannu sai ya taho wajenshi ya daukeshi ya Fara fita Ismail ya bi bayanshi, as they head to the parents apartment kowa da tunanin da yake, suna zuwa bakin kofar duk Suka tsaya ."wish us luck" Ahmed ya fadawa Nasir dake hannunshi before ya cire shoes din kafarshi ya Shiga ciki da sallama yayinda Ismail na biye dashi, amsawa alhaji dake Kan dining yayi yayinda mahaifiyar Amira ke zaune kusa dashi tana zuba mashi ruwa sanda suka shiga, amsawa hajiya da alhaji Sukayi suna kallon su, alhaji kallon yaron dake hannun Ahmed yayi kawai,. He looked at him for over good 2 minutes before ya sadda kanshi kasa, hajiya kallonshi tayi ta dauke kanta shi Kuna alhaji ya dauki ruwan da aka zuba mashi Yasha before yace "Join me..." Ya fada masu, "Mum gode daddy..." Ahmed ya fada Yana zama Kan carpet a tsakiya falon, Yana Zama ya Dora Nasir Kan kafarshi shi Kuma ismail ya zauna kusa dashi, alhaji Bai Kara cin abinci ba ya dawo falon, sake gaidashi Ahmed yayi, Nan alhaji ya tambayeshi aikin me yakeyi yanzun ya fada mashi ya samu aiki a wani NGO ne Nan cikin gari, alhaji looks so happy, kurawa yaron da tamkar Yana kallon Amira at young age yayi kawai sai yace "Zo..." Alhaji dake Kan kujera ta alfarma ya fada Yana warewa yaron two hands Dinshi, Nasir kallonshi ya tsaya yayi Bai je ba, "Go to Grandpa..."Ahmed ya fada Yana direshi, Nan yaron ya taka zuwa ga alhaji Muhammad dake kallonshi, Yana zuwa sai ya daukeshi ya Dora bisa kafarshi, ba karamin dadi Ismail yaji ba as it never happens,Basu San kou kadan alhaji have nothing against them ba, kawai dai Basu haduwa ne, Ahmed sanyi yaji cikin ranshi wishing he can snap this and send to Amira da take tsoron Kar a koreshi because of yaron, Ahmed kasa magana yayi ya sadda Kai kasa sai tunanin how he is going to start kawai yake, hajiya