← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 237

Sashe 99

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri👏🏼kamar yarda muka Saba duk sallah munayin adashin kayan sallah Dana kayan kitchen to wannan lokacin ma lokaci yayi @ zee Musa collection taxo muku da hanya Mai sauki domin ga number 📞📞📞08029882667 💃🏼💃🏼💃🏼🤣 samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata 💃🏼💃🏼💃🏼🤣 idan matsalarki rashin sabbin plates 🍽️idan axumi yaxo 🍽️ to ansamu hanyar maganin wanan matsalar idan kina son siyan atamfane da lace Amma bakida kudi a lokaci daya to duk Dama ta samu Zaki iya shiga wannan dashi namu mu Aiko muki da kayanki ako Ina kikyee da yarda Allah
Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k 💃🏼
Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa 💃🏼💃🏼💃🏼hardakyee domin akwai tsarin zubi duk karshen wata iya yarda Zaki iya idan lokacin daukarki yayi ki Fadi duk abunda kikyeeso atura muki ko menene har supplement domin gyaran jikin domin ba iya Kaya muka tsaya ba wasu abubuwan ma sai ka shiga group Dina zakasha kallon sabbin abubuwa masu kyau da Kuma sauki
Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce 💃🏼💃🏼👍🏻🥰 ga number din da zaa iya damuna 💃🏼💃🏼🤣📞📞 08029882667

*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU....
ROMO ÆŠANYE
GAWURTATTU UKU
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

15

"Yaya Bara'u ina wuninku? Yaya barka da dare ya akaji da taro?"
Sai lokacin Hadiza ta fahimci ashe lalacewa tayi wajen kallon Shafa, yanda take wani gwalangwaso kamar babu ƙashi a jikinta. Sai da ta sauke ajjiyar zuchiya kafin tace.
"Taro alhamdulillah, ya baƙunta,?" Murmushi tayi gajere kawai. Shi kuma gogan sai yace.
"Matso ga abinci muci tare. Hadiza bata cokali" Dole ƙanwar naƙi kenan. Haka Hadiza ta ɗakko cokalin ta miƙa ma Shafa. Sai jujjuya shinkafar take yi ta kasa kai ko loma bakinta. Shafa da Gwadabe kuwa bil haƙƙi suke cin abincinsu. Carab a idanun Hadiza suka sakarma da juna wani murmushin ƙauna wanda ya kusan tarwatsa kan Hadiza. Shigowar Auwala da Amaryarshi Shatu, da Mammada da Amaryarshi Nana ne ya sanya Hadiza ta ɗago da fara,'arta ta tarbesu. Matan a ƙasa suka zauna, Mammada da Auwala kuma suka zauna a sama.
"Amare kun sha ƙamshi, kun rigamu shigowa naso in shiga da yamma to na ɗan tsaya yin gyare gyarene. Bari a zubo abinci ko?" Auwala da yasa hannu a abincinsu Bara'u ya soma ci yace.
"Yauwa dama Shatu taƙi cin tuwon ɓula wai ita shinkafa zata ci. Dama naso daga nan in kaita ɗakin Anty Badi'a ne nasan zamu samu abinci. Mammada zo mu muci nan. Hadiza ƙaro mana" Ya miƙa ma hadiza tiran abincin ta zuba musu. Nan ta zuba ma Amaren Yayun nata. Gwadabe da Shafa sai abincinsu suke ci, anata nishaɗi. Su Shatu ma suka saki jikinsu suka ci abinci. Hadiza fa sam taƙi cin abincin da wayo_da wayo. Bayan duk an kammala cin abincin sai su Bara'u suka haɗe nasihar da zasu yi musu du harda matan su Auwala. Daga haka kuma suka yi ma Hadiza Sallama, tare suka fita dasu Auwala da matansu zasu kaisu ɗakin Yaya Tasi'u da Yaya Jamilu. Ɗakin ya rage daga Gwadabe sai matanshi. Tattare kwanuka Hadiza ta soma yi.
"Zauna Hadiza inaso in ɗan yi magana daku nima" A sanyaye ta ajjiye kwanukan ta zauna a ƙasa shi kuma yana bisa kujera.
"Da farko dai ina mai roƙonku arziki ku haɗe kai ku samar da farin ciki, nutsuwa, zuriya ta gari a gidannan. Dole ku haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen haɗe kawunanku. Kar ku bari wasu su shiga rayuwarku su yi ƙoƙarin tarwatsaku. Gidannan cike yake da facaloli ke Hadiza kinsan komai. Nima ina da ilimi akan irin zaman, ni da Iyabo mun zauna tare da su Yaya Hambali, babu irin gulme_gulmen da ba'ayi a tsakankanin mata. Ni bazan hanaku tsaɓin kawaye a cikinsu ba, amman na horeku da ku iya bakunanku. Duk da dai ku ba mazauna bane, ke kina aikinki na koyarwa itama Shafa Yaya Tasi'u ma yace ta bashi takaddunta zuwa gobe in aka nutsa zan kai mishi zai samar mata aiki. Dan Allah ku taimaki talakan mijinku ku bashi nutsuwa, aikina na wahalar gaske ce ina roƙonku da ku samar da farin ciki a gidannan. Ni in so samune yau in ganku a wannan ɗakin gobe in ganku a ɗakin Shafa kuna hira kuna dariya." Fasali yaja tare da ɗan yin murmushi, suma murmushin suka mayar mishi.
"To kasancewar gobe zan bar ɗakin uwargida, kamar yadda addini ya tanadarma matar data taɓa aure inta kuma wani aure kuma tana da kishiya kwana uku Shari'a ta tanadar mata. Hadiza a matsayinki na babba da kwanan da rabon girkin na baki wuƙa da naman faɗin yadda za'ayi, kuma in sha Allah yadda kika ce hakan za'ayi" Hadiza wacce ƙwalla ta taru a idanunta tun lokacin da Gwadabe ya kirata bazawarar data taɓa aure a gaban kishiyarta, kuma ta ɗauki hakan a matsayin tozarci. Ta ɗanyi yaƙe tace.
"Nagode da wannan girma daka bani. A babin maslaha ina ganin tunda du mu biyun masu fita aikine zaifi kyau ace ko wacce ta dinga girkinta kawai, gudun shiga hakkin wani. Dangane da rabon kwana kuma ayi kwana uku_uku. Sannan ni na baka damar shiga ɗakin Amarya a darennan kwanana guda ɗaya na yafe shi naci girma." Tsam Gwadabe yayi yana karantar yanayinta da duk ya sauya, ya riga yasan da Hadiza zai samu matsala kishinta yayi yawa. Yanata tunanin to meye abunda ya ɓata ranta yanzu_yanzu. Kawar da tunanin yayi da cewa.
"Ba za'ayi haka ba, kuma ai akwai danginta a ɗakin sai zuwa gobe zasu kama hanya. Dangane da rabon girki da kwana naji abinda kika ce, kuma dama nayi miki alƙawarin duk yadda kikace ta zauna. Inaga in kuna da wani ƙarin bayani zaku iyayi" Du su biyun suka ce basu da wani ƙarin bayani. Sallamar Shafa yayi ta koma ɗakinta. Hadiza kuma rai a murtuke take ta faman kai kawo na fitar da kwanukan da aka gama cin abinci. Ruwan wanka ta kai mishi harda ɗiga mishi wannan haɗaɗɗen turaren wankan data siya a hannun mai gayya mai aiki Mrs Bukhari ( kema ki mallaki naki yana da sirri)
"Na kai maka ruwan wanka kaje ka watsa" A madadin ya tashi sai ma ya riƙo hannunta yai mata masauki a cinyoyinshi, dan nauyi sai da ƙashin guiwarshi yayi motsi mai zafi. Shi ya ƙura mata idanu, ita kuma ta ƙurama ledar tsakar ɗakinta idanu. Can sai hawaye shar_shar suka soma zubo mata.
"Ya Allah Hadiza menene ya kawo kuka kuma, shin nayi wata maganar data sosa miki ranki ne?" Shiru tayi shima shiru yayi yana kallonta da dai yaga abun bana ƙare bane sai ya rungume abarshi yaima bakinta riƙon alawar yara. Ji kake shiru sai sautin ajjiyar zuchiyar Hadiza. Sun jima a cikin wannan koramar da kyar ya zare jikinshi a nata. Miƙewa tayi da sauri, yai mata dariya tare da girgiza kai.
"Ke ba yarinya ba, amman kinfi yarinya shagwaɓa bari in fito wanka sai kin faɗamun sanadin zub da hawayennan kina Amarya" Dariya tayi kawai. Shi ya wuce wanka ita kuma ta wanke kwanukan da akaci abincin a ƙaton bawo a kusa da kitchen ɗinta. Tana ganin shige da ficen Dangin Shafa. Yaya Tasi'u ne yazo wucewa.
"Yaya Tasi'u sannu da dawowa" kallonta yayi yana dariya. Hannayenshi rike da ledoji kawai saiya miƙo mata leda ɗaya.
"Zo ki karɓa Hadiza rabonku ne dan tunda na shigo gidan banci karo da kowa ba" Da sauri taje ta amshi ledar tana murna tare da yi mishi godiya.
"Ina Gwadaben?"
"Wanka yake yi, ni kuma wanke_wanke na gama"
Kafin ya bata amsa Yaya Jamilu ya shigo gidan shima. Abun mamaki wucesu yayi ba tare da yayi musu sallama ba balle ya tsaya a gaisa, É—auke kanshi yayi kamar ma bai gansu tsaye ba. Tasi'u ya girgiza kai yace.
"Allah ya nuna mana lokacin da iyalan Malam zasu haÉ—e kawunansu su mayar da damuwar Æ´an uwansu damuwarsu. Sai da Baba ta faÉ—a dama haÉ—akaarnan babu abinda zata haifar face sabon rikici. Jafaru da matarshi ne suka fito daga É—akin Zangina, sai fa da suka zo dab damu Jafarun yace.
"Sannunku" Itako matar tashi kalloma basu isheta ba" Kasa amsawa dukkansu suka yi suka bisu da idanu har saida suka shige ciki.
"Jeki ciki Hadiza kinji. Allah ya bamu lafiya sai da safe"
Jiki a mace Hadiza ta shige ciki. Lemo da ayaba ne a cikin ledar da Yaya Tasi'u ya bata. Lemun ta yanka musu ta saka a plate, Gwadabe na shigowa falon ƙamshin turaren wankan data zuba mai ya daki hancinta.
"Ina kuma muka samu lemo?" Yai mata tambayar yana mai ƙureta da ido.
"Yaya Tasi'u ne ya bani. Haɗuwa muka yi shi zai shige ɓarayinsu, yace a gaisheka"
"Ayya ina amsawa."
Wanka Hadiza tayo itama, a daren Gwadabe ya mantar da'ita wata damuwa data É—aurama kanta.
Washe gari kuma Dangin Shafa Amarya da su Goggo Iyatu duk suka É—unguma suka kama hanyar Takai, su Goggo Iyatu ko sallama ba sui da Gwadabe ba balle Amaren shi. Sai su Sakina da Ayashe ne kawai suka shigo su kai sallama da Hadiza. Gidan ya gare daga sabbin Amaren sai su Yaya Tasi'u.
Tun bayan tafiyar ƴan Takai Shafa ta shiga aikin gyaran ɓarayinta, daga cikin uwar ɗaki zuwa falo, zuwa kitchen. Daga cikin gida yauma aka kawo musu abincin karin kumallo. Tun bayan data ga Gwadabe yayi ma su Bara'u rakiya zuwa tasha, bata sake sanyashi a idanunta ba har azahar.
Tana zaune tana cin nakiya tana kurɓar shayi sai gashi ya shigo da fara'a ɗauke a fuskarshi.
"Amarya bakya laifi daÉ—i ake ci ne?" Murmushi tayi mishi kafin tace.
"Kaga nakiya ce nake ci na ɗan soma jin yinwa" Zama yayi a kusa daf da'ita ya gutsiri nakiyar ya jefa a bakinshi. Yana ƙarema ɗakin kallo yanda ta sake mai fasali yafi na farko fiye.
"Me yasa baki ɓararraka ko taliya bace, ba naga taliyar Hausa a kitchen kusan kwalla uku ba, ai ko mai da yaji sai ki zuba. Tunda su Baba Fhatsima sunma yi ƙoƙari suma suna buƙatar hutu. Naji gidan duk ya kaure da ƙamshi da halama amaren gidan sun soma girki"
Sailuba ɗiyar Yaya Tasi'u ce tayo sallama ta shigo. Hannunta riƙe da filas ɗin abinci, a gabansu ta dire tare da gaishesu cikin girmamawa.
"Innata ce tace in kawo. Tace kiyi haƙuri aikine yai mata yawa sai yanzu ta sauke sanwar" Murmushi Shafa tayi tace.
"Babu komai kice mata nagode Allah ya saka da Alkhairi" Da "Ameen" Sailuba ta amsa tai musu sallama ta fice.Shafa kuma tayi sauri ta É—akko plate da cokula biyu ta juye musu abincin.
"Bismillah mu ci ko tunda dai kana nan aka shigo da abincin " Bai mata musu ba sai yayi kamar yadda tace dashi.
Hadiza kuma tana can ta tusa abinci a gaba tana jiran shigowar Gwadabe su ci, yace zai ɗan leƙa Shafa a tsaitsaye. Yau zai shigo, gobe xai shigo, saida ya share awa uku kyawawa. A wannan lokacin Hadiza ta kai maƙura wajen ɓacin rai. Abincinta ta zuba tayi shigewarta ɗaki ta zauna kenan akan gado ta jiyo yana sallama a falo. Jin motsin cokali a uwar ɗakine yasa ya leƙo uwar ɗakin suka haɗa idanu, take yasha jinin jikinshi, amman lokacin sallah ya riga da yayi haka dole yayi alwala ya tafi masallaci. Yana dawowa kuma kamata yayi ya ɗebi ƴan suturu ko kala ukune ya koma ɗakin Shafa daga la'asar kwananta zai soma.
Har ya gama ɗiban kayan da zaiyi amfani dashi Hadiza tana daga kwance tana kallonshi, sai tubka da warwara take yi. Wani irin muƙu_,muƙun kishi ke turniƙeta. A kusa da kanta dab ya zauna yana shafar sumar kanta dake sheƙi da ƙamshi.
"To ni kam zan tafi Hadiza. Sai bayan kwana bakwai zan dawo. Zanyi kewarki sosai, tare da wannan ƙamshin naki mai tasiri a zuchiya" Wani kallo tayi mai shi ba harara ba, shi ba kallon so ba. Dan ya kasa fassara irin kallon..
"Abincinka dake ajjiye a falo fa, kaci ne?"
"A'a É—azu ina shiga É—akin Shafa Sailuba na kawo abinci. To shine shafar ta zuba mana, kinga ai ba zata ji daÉ—i ba in banci ba, kafin zuwan Sailuba kuma naci nakiya"
"Agen? Hmmm shikenan a sauka lafiya ango. Lallai ga zumuɗin yage tantani nan ina gani a tattare da kai. Nutsuwarka harta gushe sabida kula da kai zai koma hannun Shafa " Baki ya buɗe zai yi rarrashi. Tayi saurin ɗaga mishi hannu, sai kuma ta fashe da kuka. Ƙur yayi yana kallonta kawai yana tunanin irin danƙareren aikin dake gabanshi. Dan ya lura Hadiza bats son a zauna lafiya balle a samu haɗin kan da zai samar da nagartattun ƴaƴa. Da wuri ya kamata yaima tubkar hanci dan gudu kada wankin hula ya kaishi ga dare. Masu iya zance na cewa. Itace tun yana ɗanye ake tankwarashi, matsawar ya bushe to sai dai a ɓallashi. Dannewa yayi ya shiga aikin rarrashinta da shafar bayanta har tayi shiru. Tana gani ya fice a ɗakin Izuwa ɗakin Shafa.
Tohfa
MRS BUKHARI
09153081057
Ga masu san magana dani kai tsaye ta whatApp ga number na
Masoyana sunata mun ƙorafin babu number na a jikin littafi kuma suna son muyi zumunci, ƙorafi ya ƙare.
Chapter 99 · 0% Book details