Sashe 11
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wata wal ardi zai bamu mafita, zamu ji daɗi a gaba komai lokaci ne. Tashi mu je mu hura wuta, ga ɗan abinci mun samo daga ƙauye, ko fara ce in dafa mana, ina da yaji, mai ne babu dai." Tire na ɗakko na zuba shinkafa ƴar hausa Gongoni biyar, Uwani ta karɓa ta fita. Kurfot ɗina na zaro a ƙarƙashin gado da ƙullin gawayin hamsin a kai, nima na fito tsakar gidan. Wuta na hura da leda, Uwani na zaune a kujera tana tsintar shinkafa tace. "Ji gidan shiru kamar ba shi bane mai tarin hayaniya da bataliya ba" Yatsana nasa a leɓena nai mata nuni da tai shiru sabida Laila. Dole mu ka zama kuramen dole. Tashi nayi na ɗakko tukunya na buɗe randata dake bakin ƙofa cike da ruwa na zuba ruwan a tukunya, na ɗaura a wuta. Ruwan na tafasa Uwani ta wanke shinkafar ta zuba. Alwala muka ɗaura dukkanmu muka shiga ɗakin. Da sauri Laila ta ajjiye kwanon samira dake ajjiye a gefe guda. Kallonta nayi itama ta kalleni. Kai na girgiza na nufi hanyar shiga ciki. "Am Iyabo a ina zan ajjiye fantimotaina naga kamar basu dace su zauna a falo ba" Kallonta nayi na ƙara. To a ina kike ganin ya dace ki ajjiyesu in ba falon ba?" Na bata amsa cikin danne fishi, dan ji nake wallahi kamar in dira a wuyanta. "A uwar ɗaki mana, taya zan ajjiye kayana a falo?" Ta faɗa a gadarance irin ta dangi miji dan halinsu ne wannan kam. Cikin cusa haushi nayi dariya nace. Haba Laila, ai uwar ɗakina mallakinane tafi ƙarfinki, iyakar taki a falo take. Uwani mu shiga ko?" Na yi shigewata ciki na bar Laila tana surutai ni bansan ma me take cewa ba. Abinci na zuba mana a tire. Na zuba na Laila a kwanon silver, na zuba ma Toye nashi. Wani ƙaramin kwano na jawo a ƙasan gado, ragowar manjan miya ne a ciki nama mance dashi na tsiyayama Laila da Toye ragowar na ajjiye a gaban uwani danta soma cin abincinta ma gaya abunta. Falo na fita da zummar in ba Laila abincinta na tarar bata cikin falon. Ajjiye mata nayi a inda na barta. Na jawo hannun Toye yanata wasanshi muka shiga ciki na zaunar dashi. Kabbarar Sallah nayi. Ina cikin sallah muka jiyo sallamar namiji. Uwani ce ta fita dan dubawa. Sai da na idar sai gata da leda mai zane, da kuma baƙar leda da kuɗi dubu biyu. "Saƙone Gwadabe ya aiko miki. Gwadabe akwaishi da ƙoƙari akan komai ma, gaskiya ki sake gode ma Allah. Gwadabe ya riƙe miki amanar ƙaunarki. Iyabo kar ki kuskura wannan mai idanu a tsakar kan ta rabaki da mijinki." Tabalbalin sai na dage da tsaiwar dare. Domin tsorona bansan da wanne irin shiri tazo ba. Nasan kyanta, ko farinta, da kyan durinta bazai taɓar ruɗar Gwadabe ba. Na yarda da irin son da yake yi mun. Kuma na yarda yana ganin kyauna a hakan da nake, ko babu komai yakan yabeni ya kurantani. Kuma yasan da'itan ya tsallaketa ya auroni. Ni dai da sallar dare zan dage kar su je su nemar mun miji ta hanyar asiri. Uwani ina cikin damuwa sosai wallahi. Ke dai mu ci abinci kinji. Muna hirarmu muna cin abinci, anan na ba uwani labarin abinda ya faru a cikin gidannan ranar da zamu je Takai, da kuɗin hayar da zamu soma biya. Uwani tayi mamaki ainun ta jinjina irin ƙiyayyar da dangin Gwadabe suke yi mun. Sai bayan la'asar Uwani ta shiga haramar tafiya. Shinkafa da taliya, da kayan miya, da ɗanyen kifi, manja, maggin da Gwadabe ya aiko yaro ya kawo duk sai dana ɗibar mata, na bata ɗari biyar. Bata tafi ba sai da ta ɗoramun miyar tumatur a gawayi, da kanta ta leƙa ta kai mun niƙan maƙota. Sai da na rufe uwar ɗakina sannan na rakota. Mun fito mun samu Laila tana cin gurasa da lemun koka kola, abincin dana ajjiye mata kuma ta tureshi gefe guda, ƴar ƙaramar rediyo ta kunna tana jin waƙat barmani choje, waƙar gwarne ikon Allah. Tana yi tana karkaɗa kafaɗarta. Wucewa muka yi jiki duk a sanyaye. A sanyaye mu kai sallama da Uwani tana sake jan kunnena kar in kuskura in bar gidana sabida wata. Ko dana dawo ban shiga falon ba, a tsakar gida na zauna ina tsintar shinkafa ina shaƙar iskar ƴanci. Dan da masu gidan na nan, da ananan ana zubar mun da habaici, gami da maganganun cin fuska marasa daɗin saurare. A taƙaice dai ko dana gama girkin dare na sake zuba ma Laila a wajen ta sake bar mun. Ta fita ta siyo tea da biredi. Ni ko tunda na janye yarona na shige ciki nasa sakata, ban sake sanin halin da Laila take ciki ba. Misalin ƙarfe goman dare sai ga kiran Gwadabe ya shigo wayata. Cike da zumuɗi da kewa na ɗauka. Daman a zaune nake dan tunda cikina ya tsufa ban fiye samun baccin dare ba. Allah sarki Gwadabe da yana nan da yanzu yana matsa mun ƙafafuna. Amincin Allah ya tabbata a gareka gwarzon gwaraza. Barka da hanya, da fatan kana cikin aminci?" Murmushi yayi mun yace. "Barka sa dare sarauniyar zuchiyar Gwadabe, da fatan kina cikin ɗakinki na sunna cikin aminci ko?" Farin ciki ne ya lulluɓeni bansan sanda na lumshe idanuna ba. Ina lafiya, sai kewarka dake nuƙurƙusar zuchiyata. Ya hanya fa?" "Ba daɗi hanya. Kin ganmu a Tafa mun tsaya cin abinci da Sallah. Shine nace bari in ji lafiyarki. Ina Toye?" Gashi nan yayi bacci. "To masha Allah babu dai wata matsala da Laila ta baki ko?" Baki na taɓe kafin nace. Babu wata matsala a halin yanzu. Amman abincin rana dana dare dana bata duk bata ci ba. Fita tayi ta sai abunda ranta yake so" Faɗa ya soma yi akan karma in ƙara saka mata abincin in nayi tunda abun iskanci ne. Ni dai nace. Ba za'ayi haka ba. Ai da duk take_takenta so take in ƙi zuba mata a kafa mun hujjar na hanata abinci ita da gidan ɗan uwanta. Kai dai ka yi tunanin nemo mana mafita kawai. Dan wallahi Allah bazan zauna da gansamemiyar bazawara kamar Laila ba." Dariya Gwadabe ya dinga yi mun yana tsokanata kan na fiye kishi. Nima da dariyar na bishi kawai. A haka mu kai sallama dashi. Bacci bai zo ma idanuna ba, ƙarfe sha ɗayan dare na ɗaura alwala a cikin bahun babba. Na raba dare ina neman tsarin Allah ga dukkan masu son cutar dani da mijina, da masu son ganin bayan auren. Na roƙi Allah yai mun katangar ƙarfe da Laila ya karemu da dukkan sharrin data kwaso. Gwadabe kuwa alkhairi duniya dana lahira na roƙar mishi. Sai zaman lafiya, da jin daɗi wanda bana gajiyawa wajen sake roƙa mana, kusan duk addu'o'in maimaicine ba dare ba rana. Sai dai yau na ƙarama adda'ar tsawo da wasu salon roƙon. Sai wajajen jefin assalatu bacci ya kwasheni ina daga zaune. Amman ana kiran sallar farko na buɗe idanuna. Yinƙurawa nayi na tashi na buɗe ƙofata na fito da bahun ɗina na fice. Laila na saman doguwar kujera tana bacci saye da wandon bacci iyakarshi guiwa, rigar wandan mai shara_ shara ne har kan mamanta ina iya ganowa. Gabana ya doka da ƙarfi, kifiyar kishi ta soki tsokar jikina. Kai kawai na girgiza domin nasan tabbas dama a rina. Laila da kyan sufa da launin fata take son Jaye Gwadabe daga gareni. Dan tana da kyau tubarkalla masha Allah. Kuma ko a ƙauyen ita idanta a buɗe yake tar. Fita nayi na kama ruwa, na ɗaura alwala na koma ɗakin. Dai _dai da farkawar Laila tana tsaye tana miƙa. Na ƙarema wandon baccinta kallo shima shara_sharenne ina hango zaratan cinyoyinta farare luwai_luwai dasu. Ya kamata ki sani cewar nan ɗakin matar wanki ce, ba ɗakin aurenki ba. Wannan shigar a ɗakin mijinki kaɗai ya dace ki yita ba anan ba. Zan iya lamuntar komai, banda shigar banza mai nuna tsaraici, ki kiyaye sosai" Hararata Laila tayi tare da yin shewa tace. "Ashe ana tsoron iya inji ƴaƴan maiya. Babu rami me ya kawo rami Iyabo? Ashema baki yarda da nagartarki ba a matsayinki na mace ba." Murmushi nayi mata kawai domin bani da lokacin misayar yawu da'ita. Bayan na idar da sallah na yi azkar da adda'a, na jima sosai ina tunanin yanda ƙarshen zaman Laila a cikin ɗakina zai kasance. Ta yaya, kuma ya za'ayi tabar ɗakinnan alhalin Babalace ta bata umarnin zama, kuma dani da Gwadabe duk a ƙarƙashin ikonta muke. Wata zuchiyar tace. "Ai matsawar ba barin gidan kikayi ba Iyabo. To tabbas Laila babu inda zata fita taje. Babu makawa Gwadabe sai ya aureta. A daddafe na miƙe na shiga gyaran ɗaki, sai da na kintsa komai, na fitar mana da wankin kayayyakinmu na soma wankewa inayi ina rera waƙar yarbawa, amman wani shashe na zuchiyata a cike yake da tsoro da fargabar zamana tare da Laila. Kafin takwas na safe na gama komai har shara da wanka duk mun yi. Abinci na ɗunɗuma mana, kamar jiya na sake zuba ma Laila nata dai na dire mata. Ina gama karyawa na fito cikin shiri, na yi kaye_kayen kayana masu amfani na kulle uwar ɗakina. Laila na falo tana cin abincin dana ajjiye mata na yi ficewata ina jaye da hannun Toye, har zuwa bayan layinmu gidan da nake yin aikin shara, wanke_wanke, da goge _goge, sai wanki amman injinne yake wankewa, ya ɗauraye, ya busar gogewa ne dai nawa, sai in jera a sib, sai kuma girki amman shi ba ko da taushe bane. Babu wanda yasan ina yin wannan aiki, domin yana daga cikin sirrinmu ni da Gwadabe. Matan gida dai suna gutsiri tsomarsu akan fitar da nake yi tun safe, bani zan dawo ba sai azahar, har Gwadabe Yaya Hambali ya tara da zancan dan a tunaninsu gantali nake zuwa kawai. Yaya Haula kuwa cewa tayi bin gidajen maƙota nake yi yawon tsogumi, dan babu wanda ya kai yarbawa gulma da munafurci a cewarta. Da sallama na shiga madaidaicin gidan. Matar gidan tana ciki, dan na hango ƙofar falon a wangale. Bayan sallama kai tsaye na shiga falon. Tana zaune tana duba wasu