← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 237

Sashe 25

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

harshen yarbanci kuma sukan maiyar da harafin H a matsayin a misali Alima a madadin Halima auwa a madadin Hauwa, Abu a madadin Habu. To itama Iyaa Kokodeen manya da Alima suke kiranta. Ta dubi Dada tace. "Gaskiya ne sosai, mu kanmu wanne haƙurinne ba mu yi ba, namu haƙurinma na mutan da ba irin na yaran zamani ba. " Ranar Burodami yasa mita, sai an kawar da maganar sai can ta dawo da zancan baya. Har Burodami Debisi ya gaji ya bar gidan amman bata sauya zani ba. Haka dai wunina ya kasance bamu muka tashi shirin tafiya gida ba sai da magriba ta kawo kai. Akamu Iyaa Kokodeen ta bani da garin albo dana amala, bata taɓa gajiyawa muddin zanzo sai ta bani. Dada kuma ta miƙo mun ƙunshin bakon da tayo mun tsarabata. Dada yaushe zaki koma, amman zaki zo gidana ko Dada?" Kawar da kai tayi tace. "Me zai kaini gidanki Jabu, ai babu. Jibi zan koma ni kam in sha Allah " To Dada gobe zan dawo akwai saƙo da nake son baki ki ba su Baɗɗo." Kai kawai ta gyaɗa mun. Iyaa kuma ta dire tace ban isa in dawo ba, in Lekan yananan in je ɗakin zaure in kirawoshi in yaso sai ya bini ya amso saƙon" Ba dan naso ba akayi hakan. Da Lekan muka dawo gida. Ƙannena su su huɗu ne, biyu mata biyu maza. Matan na cira musu atampopi guda ɗaɗɗaya sababbi dal. Na cire ma Dada lashi da Atampa coddibuwa, Baffa kuma na cire mishi shadda guda ɗaya ce rak. Na cirama ƙannena mazan kaya kala ɗaɗɗaya a cikin kayan da Hajiya ta bani in ba Gwadabe. Dada na ƙara mata da mayafai da hijabi, da sabon takalmi dan naga takalmin da tazo dashi a ƙafarta takalmin robane duk ya sha liƙi gashi har ɓulewa yayi. Nera dubu goma na zara na miƙa ma Lekan. Yasa hannu kenan zai karɓa Laila ta shigo babu ko sallama. Banji daɗin shigowar tataba sam, bin Lekan da kayan da na soma cusa mishi a bako tayi da kallo. Lekam muje nayi ma bayani a ƙofar gida" Biyoni yayi a tsakar gidanma da idanu yuuu su Yaya Haula suka bini. Baban Nazifi ya daka mun wata tsawa fitowarshi daga ban ɗaki kenan. "Waye wannan sannan wannan kayan da Za'a fita dashi menene a ciki?" Ya jufo mun tambayar bayan ya iso gabanmu. Ɗan fodiyo dake zaune a tabarma suna ƙirga kuɗi shi da Da'u ai sai ya taso yasa hannu ya fisge ledar hannuna ya zazzageta a ƙasa komai suka zubo ƙasa. Ganin matan gidan a gaban kayan Yaya Haula harda salati yasa na fashe da kukan baƙin ciki. Jin amon muryar Yaya Harisu ne yasa na sassauta. "Ina za'a kai kayan. Shi wannan gona_gonan ƙaton da kika shiga ɗakin mijinki dashi alhalin kinsan Gwadaben bayanan fa, ko gwalen naku na yarbawan zaki shigo mana dashi?" Lekan sarkin zuchiya har zai yi magana na dakatar dashi da yarbanci cewar kar ya sake yace komai. Na mayar da hankalina kan Da'u da Baban Nazifi ya bashi umarnin wauwara kayan. Kayan maza da suka gani yasa Baban Nazifi ɗago rigar yace. "Wannan ba rigar Gwadabe bace Iyabo. Wato sace kaya kike yi ƙannenki suna zuwa da daddare suna fitarwa ko? Kenan doguwar rigar Haula data ɓata muna tunanin ruwan sama ne ya gudu da'ita ta rariya ashe kece kika sata? Asirinki ya gama tonuwa a gidannan ƙila harda ƙarshen zamanki " In kada baki in yi magana na kasa. Lekanne yace. "Wannan kayan data samu a sunan Taiwo da Kahinde ne, sauran kuma nata ne na gida, sai kayan mijinta guda biyu. Mahaifiyarta ce tazo daga ƙauye shine ta bayar a kaima ƙannenta, kuna da matsala da hakanne to? Batun sata kuma Antimi Iyabo ba ɓarauniya bace ba'a mana wannan tarbiyyar ba." Salati Gude ta saka tace. "Au ita Iyabon dama tana da ƙanne mu bamu sani ba? Sannan iyakar saninmu uwarta ma ita kanta ba tace ga inda take ba, yasar da'ita tayi tun tana ƙarama ai." Yaya Harisu yace. "To munji babu kayan da zai fita a gidannan. Kai kuma fice mana a gida" Kamar kuwa jira Lekan yake yi ya fita fuu yana sababi da yare. Da manuniya Yaya Haula ta nuna ni tace. "Wabillahillazi huwarrahmanu sai kin biyani doguwar rigata, nera dubu takwas na siyeta , tunda na kama ɓarauniyar rigar." Nan su Gude suka soma tafi tare da yi mun kururuwar naji kunya. Tsugunnawa nayi jikina na rawa na kwashe kayana zan shiga ɗaki dasu, Baban Nazifi ya warce buhun yace. "Har sai kin biya kuɗin rigar da kika sata zaki samu kayanki, Allah wadaran halinki." Tiɓi_tiɓi da kayan mazaunai na tafi ɗaki da gudu na faɗa akan gado na sau rikitaccen kuka irin wanda ban taɓa yin irinshi ba a duniya. A wannan halin Gwadabe ya dawo tafiya ya tarar dani, dan wallahi ko sallamarshi ma banji ba, sai jin hannunshi nayi a jikina, ina ɗagowa da naga shine na kife na sake rugujewa da kuka. A ƙagauce yace. "Wani abunne ya faru da kika je wunin gida ko? Iyabo kiyi haƙuri ki dena kuka akan matsalolinmu dan Allah." Banza nayi mishi da ƙyar ya iya nasarar shawo kaina na faɗa mishi abinda ya faru" Shiru yayi kamar ruwa ya cinyeshi yana riƙe da kumatunshi. Amman naga ranshi ya ɓaci ainun har jijiyoyin goshinshi sun tsaya. "Yanzu kayan suna ina, ina shi Lekan ɗin?" Cikin rawar murya nace. Kayan suna hannun Baban Nazifi, Lekan kuma Yaya Harisu ne ya koreshi." Numfashi ya ja dogo yace. "Ina zuwa ki goya Kahinde da Taiwo zamu fita." Gwadabe na kirayi sunanshi da gaggawa, kulawa ma yabawa dan ko juyowa bai ba. Ina zaune a bakin gado da goyo a bayana, sai na soma jiyo maganganu sama sama ina jiyo tashin muryoyi daga tsakar gida. Ni dai ban ko yi yinƙurin miƙewa ba, hayaniyar sai ƙara tsananta take yi, jin kamar ana titirniyar dambe ne yasa na fito da gudu, aikuwa ƙafafuna suka harɗe na faɗi rib cikina da Manana suka daku da ƙasa. Take wasu hawayen wahala suka wanke mun fuska. Abunka da mai ƙiba sai fa da dabara na miƙe ƙafata naji ta nai mun mugun zafi, a haka na daure na fita. Da'u Gwadabe ya damƙa yake ta kai mishi mahangurɓa, Yaya Harisu na riƙe da Gwadabe ta baya yana jayeshi, Ɗan fodiyo na riƙe da Da'u ga Auwal a tsakiya yayi musu iyaka. Baban Nazifi kuwa yana gefe yana sharce hawaye Yaya Haula tana rarrashinshi kamar wanda jaki ya kada shi da ƙasa. Su kuma matan gidan suna cure waje guda da yaransu maza da mata. "Ni zaka duba ka ce matata ɓarauniyace, me aka kamata ta sata da za a ci zarafinta ita da ɗan uwanta? Kaya kuma ga kuɗin rigarki Haula ku bamu kayanmu" Ban san Gwadabe na da zuchiya haka ba sai yau. Ƴan uwanshi suka rufu a kanshi da zagi da cin zarafina. Baban Nazifi ne ya jefo mana bugun kayan ya sauka a ƙirjina tab, ba da ban ina da ƙiba ba da sai na faɗi. Yaya Haula kuma ta fisge kudin hannun Gwadabe. "Gobe_gobe ku tattare yanaku _yanaku ku bar mun gidana, tunda ba da uwa da uban Iyabo aka haɗa kuɗi akasai gidan ba. Ku kuma ko wacce ta koma ciki ta ja ƴaƴanta" "Kullo ɗakin mu je mu dawo kinji Iyabo?" Ya faɗa yana haki. Da ɗingishi na koma na kullo ɗakin muka fita. Amman fa har muka isa gidanmu babu wanda yace da wani komai. Acanma mun shiga mun samu kab matan gidan da samarin gidan a tsakar gida Iyaa tana ta faman kwakwaso da sababin abinda ya abku. Ai muna shigowa ta dira a wuyan Gwadabe da zagi, har kakan kakanshi sai da ta zaga. Mahaifiyata ta kaɗa kanta ta shige ciki, Gwadabe ya miƙo mun buhun kayan na shiga ɗaki na sameta, na baro Gwadabe na ba iyaa haƙuri amman kamar ƙara ma zigasu yake yi. Ina jiyo sanda Iyaa Kokodeen ta koreshi shima waje. Da ƙyar mahaifiyata ta yarda ta karɓi kayannan, shima sai ajjiyewa nayi a gefenta. Ina gunjin kuka na nufi hanyar waje. Muryarta na rawa tace. "Jabu ki yi ma mijinki biyayya. Muddin shi yana ƙaunarki kar ki sake wannan rikice_rikicen banbanci ƙabila da aketa gwabzawa kice zaki kaso aurenki. Ko beyerabe kika aura ba tsira zaki yi ba. Dan a ƙarƙashin ko wacce igiyar aure akwai ƙalubale, in kika ji na wasu naki ba komai bane. Kice ina gaisheshi bamu samu damar gaisawa ba" Kasa amsata nayi na fice ina dingishi, a ƙofar gida na tad da Gwadabe idanunshi sun rine sosai. Haka muka rankaya gida, a daren dai ɓarawon baccine ya kwashemu muka wayi gari da labarin Baban Nazifi yace dukkansu zasu tafi Takai akwai meeting da za'a gabatar. Ni dai har Gwadabe yai mun sallama ya fita ina sharar hawaye. Ga ƙafata ta aune ta yi him. Tsabar ɓacin rai Gwadabe bai ga ƙafarba bai san ƙafar ta samu rauni ba. Haka na wuni ni dai sukuku ba laka, ƙafa fa kafin la'asar ta sake hayewa da ƙyar nake takawa. Ina zaune akan kujera ina kirɓa sakwara sai ga ƴan Takai sun yi sallama. Gwadabe na ƙura ma idanu sai naga har ya faɗa. Yana isowa ya cafe taɓaryar a ƙoƙarinshi na ganin ya kore damuwar dake cin ranshi. Ya hau dukan sakwara a turmi, dan da nan ya kammala tsab. Durƙusawar da zaiyi ya taya ni kai filas ɗin abinci ciki, sai yaga ƙafata a kumbure. "Me ya samu ƙafarli ta aune haka, kuma kike zaune kina aiki? A'a taso muje maza_maza" Babu shiri muka fice a gidan. "Ɗan iska na mamaji" Cewar Baban Nazifi kenan. Ashe targaɗe naji a idanun sawuna, mai ɗori ya gyara mun muka dawo gida. Bayan sallar isha muna zaune muna cin abinci yke bani labarin yadda akayi a takai. "Abun babu daɗi. Babala dama kinsan sai dai ma ta daɗa kwaye mun baya, gashi Goggo Iyatu tana nan mahaifiyar Laila, itama tai ta kunnawa abun wuta. Mun tsaya akan dukkan abinda ya ɓace a gidannan kece kika sace kuma ni zan biya. Wallahi nayi iyakar yina dan in fahimtar dasu fur sunƙi. Ni dai
Chapter 25 · 0% Book details