Sashe 118
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Malam
"Yayi kyau Suwaiba Nagode gaya. Ku kuma duk ku watse ko wacce ta shige ɗakinta. Gobe da safe daku da mazajen naku ina nemanku a gida bakwai na safe. Kai kuma Sabitu sannu da Uwar taka kake sa'insa sabida ɗiban albarka ko?" Iyakar abinda Malam yace kenan ya juya ya fice. Idanu Hadiza da Baba Fhatsima suka haɗa. Ƙunci da damuwa ƙarara a shimfiɗe a fuskar Baba Fhatsima. Kai ta gyaɗa ta bi bayan mijinta. Suna fitowa Baba Suwaiba ta biyo bayansu. Tsautsayi malam bahaushe yace baya wuce ranarshi. Kuma shi dana sani ƙeyace. Malam na ganin fitowar Suwaiba yace.
"Na sakeki Suwaiba. Aurena dake ya ƙare, na gaji da baƙin ciki da takaicin da kuke ɗauramun ina shanyewa tsawon shekaru. Zuchiyata tarwatsewa kukeso tayi, ko faɗuwa kuke so inyi in mutu in bar baya da ƙura. To ta faru ta ƙare kije dan kanki." Baba Fhatsima ta dafe ƙirjinta. Baba Suwaiba kuma ta fashe da ihu harda kururuwa. Malam ya tafi ya barsu su biyun a tsaye yana tafe dafe da kanshi da yake jin kamar zai tarwatse.
"Ki ƙarama bokanki kuɗi Fhatsima burinki ya idasa cika. A baya har hauka kika sa nayi na fito tsirara. A yanzu kinsa Malam ya sakeni ni Suwaiba. Ki rubuta ki ajjiye akwai ranar ɗaukar fansa tana tafe duk daren daɗewa ni Suwaiba saina saki zubar da hawaye." Cikin kuka take maganar. Murmushi Kawai Baba Fhatsima tayi tace.
"Allah ya kyauta. Nasha tabara na sha yasin"
"Ki ƙara da amanan rasulu. Fhatsima sai naga bayanki dake da yaranki duka, dani kike zancan" Har Baba Fhatsima ta ƙule Baba Suwaiba na zage_zage.
Wannan lamarin ya rura wutar hatsaniya mai girma hatsaniyar da a tarihin rayuwar iyalin malam ba'a taɓa yin irinshi ba. Dan abun yakai harda faɗa da makami a tsakanin yaran Baba Suwaiba da su Auwala da suke kare uwarsu. Baba Fhatsima sai kulleta akayi ita da Malam a turaka. Yaya Tasi'u kuma ganin abun ya wuce gona da iri sai ya kira ƴan sanda aka fita da yaran Baba Suwaiba zuwa police station domin yima tubkar hanci.
Malam yana goye da hannunshi a bayanshi sai kai kawo yake yi harda hawaye a idanunshi. Abun a tausayane ace dattijon magidanci yana hawaye ku kanku kunsan abun yakai intaha. Tunaninshi yake mayarwa baya a lokacin da suke rayuwarsu ta talauci da tsantsar soyayya shi da Fhatsima. Fhatsima tayi mishi son da harya koma ga Allah ma bazai samu macen da zata soshi rabin haka ba. Gashi a sakamakon giyar jini a jika da giyar kuÉ—in da bai taka kara ya karyaba ya É—ebo ma kanshi kara da kiyashi É—aukar marar sani. Yau shine aka tura a É—aki Æ´aÆ´an cikinshi na fito na fito dashi kan uwarsu. Fhatsimar daya raina a baya ita da Æ´aÆ´anta a yanzu sune garkuwarshi. Madallah da mace tagari, madallah da uwa tagari.
A daren Malam ciwonshi ya tashi bil haƙƙi gaga_gaga aka wuce dashi asibiti. Hankulan kab ƴan gidan a tashe yake gaya. Dan ɗaiɗaiku daga cikin ƴaƴanshi masu mishi fatan mutuwane kawai sukai baccinsu harda minshari. Masu son rayuwar malam sune suka kasa rintsawa har zuwa wayewar gari.