← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 237

Sashe 83

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
Domin neman ƙarin bayani
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU...
ROMO ÆŠANYE
BOOK 2
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

10
Haka sabuwar rayuwar gidan Malam taci gaba da kasancewa. Yaran basu da wani zaɓi face su bi umarnin mahaifinsu. Yayin da daga bayan fage iyayensu mata ke musu huɗubar tsiya, tare da cusa musu tsanar Baba Fhatsima da yaran ɗakinta. Ko gaishe da Baba Fhatsima suka je yi, cikin wulaƙanci da rashin girma suke gaisheta. Itako Baba asshi ko kallon inda Baba Fhatsima take bata yi, ƴar gaisuwarma sun dena, domin tunaninta shine Baba Fhatsima ta murɗa kambunta ta sake ƙwace gida a karo na biyu. Dan in ranar kwananta ne Malam ya dinga sunturi kenan a tsakar gidan. Itama in kwananta ne, zata shige turaka ta nitsu ta yi gyara na musamman a kunna turaren wuta. Da yamma taci adonta da kaya masu tsada tayi tafiyarta turaka. Wannan sauyi na Malam da Baba Fhatsima ya tsayama matan gidan daram a zuchiyarsu. Yayin da wasu suka soma sake sabon salon kula da malam, su Baba Asshi kuma bata da aiki sai ya da habaici a tsakar gida. Kuma taci alwashin ba zata taɓa tambayar Tasi'u kuɗi ko yai mata wani abun ba. Itama tana Ɗa Jamilu, kuma dai dai gwargwado shima yana samu, saidai Allah yayi shi da shegiyar rowa, dan ko matarshi Siyama da ƙyar take ɓamɓararshi.
Tasi'u ya dage sai gini aketa faman yi, abunka da kuɗi gininnan bai jima ba aka kasheshi, har an soma buga rabta. Ta wani ɓangare harya gama siyen kayan gado, da kujerun ƙannenshi mata, sauran tarkacen kitchen iyayensu mata ne zasu yi musu. Ya kuma riga ya sallami Baba Fhatsima da ishasshen kuɗin kayan kitchen ɗin Hadiza, da kuɗaɗen gudanar da harkar sha'anin bikin al'ada. A ranar da yaba Baba Fhatsima kuɗinne tace.
"Su matan Babanka ka basu kuÉ—in da zasu gabatar da sha'anin bikin al'adar ne, kasan fa ana kashe kuÉ—i musamman ga su da zasu aurar da maza. Kuma jibi ma za'aje kan goron mazan gidan. Jibi kuma Malam zai tafi Takai yaje ya sanar musu da lokacin biki" Tasi'u yace da Baba Fhatsima.
"Baba ban ba ko wacce daga cikin su ko sisi ba. Sabida a tunanina tunda auren maza zasu yi su yaran zasu bama iyayen kuÉ—in komai. Yarannan ba ganinki suke da gashi ba"
"Hatta Malam basa ganinshi da gashi. Kai dai kai musu domin Allah domin kuma uwayenka ne. Hatta Amaryar malam nasan zata yi nata taron, da anko duk zata yi naga sai fitarwa akeyi kashi_kashi. Itama ka bata abinda zata yi hidimarta dashi. Allah yayi albarka" Shiru yayi can ya girgiza kai yace.
"Babu komai za'ayi musu kamar yadda kika ce, in sha Allah. Naga yaronnan Gwadabe yayi ƙoƙari wajen haɗa akwatunan bikin. Sune can ko? Badi'a ta faɗamun yasa kaya masu tsada ba laifi, ta yi goshi a matsayinta na Bazawara " Baba Fhatsima tayi dariya.
"Yayi ƙoƙari babu shakka, Allah ya fiddamu kunya. Dan Allah ya buɗe musu kwanakin baya sosai. Kaga zinarin da suka tono yana da nauyi ainun. Shi ya taimaki harsu Auwala suka ƙarashe haɗa akwatunan nasu. Kuma sana'ar magani da yake yi matan gidannan na dariya suna tsokanar Hadiza wai taci baya. Sana'ar na taimaka mishi, ana siyen magungunan nashi sosai. Naga har almajiran malam siye suke yi. Kaga akwatin kishiyar Hadizan ma, komai iri ɗaya ya zuba har kala. Shine ma take ta ƙorafi ƙasanta da rashin hankali. Da abokinshi ma ya ɗauke mishi akwatin ita waccan ɗin, da dai ya samu halin yine yace zaiyi abinshi" Jawo mishi akwatunan tayi gabanshi, komai na ciki bai bambanta ba, girman takalmi, ɗan kamfai, rigar Mama shine kawai na ɗaya ya zarce na ɗaya. Dariya Yaya Tasi'u yayi.
"Hadiza daru ba. To na ƙara mata ko kala biyar ne" Baba Fhatsima tayi dariya itama tace.
"Rabu da'ita. Ta haÉ—a kaya famtimoti Babba, kuma duk ta É—inka abinta. Ga malam yayi musu kayan fitar biki. Ai kasanta da kishi, kullum cikin faÉ—a nake mata. Jibi Babarku Altine tana hanya zata zo ita da Balaraba Æ´ar wajenta. Kuma inajin sai an gama bikinnan zasu koma."
Altine ƙanwa take ga Baba Fhatsima. Mace mai kirki da son zumunci. Sai dai ba'a wanyewa lafiya tsakaninta da matan malam. Dan bata barin ko ta kwana. Balaraba kuma ɗiyarta ce, wacce da akaso ayi musu haɗin gida da Tasi'u. Amman a lokacin Tasi'u ya riga ya soma soyayya da matarshi Badi'a. Sai Balaraba ta auri saurayinta dama tana da saurayinta iyayene suka so ayi haɗin gida kawai. Yanzu kuma Allah yayi ma mijin nata rasuwa ya barta da yara bakwai.
"Allah sarki. Mama altine jibi ana hanya? To a ɓarayina zasu sauka gaskiya wannan karon ƙwaceta zanyi." Haka dai akaita hidimar biki ta ko wanne ɓangare, gidan a kacame yake ko da yaushe.
Washe Gari akaje kan goron Samarin gidan tare da kai fantimoti. An tsayar da biki wata biyu cib. Ranar a gidan ba'ai girki ba, abincinan da aka tawo dashi daga kan goro ya isa har maƙota sunci shi a wadace Washe gari Malam da Jamilu suka kama hanyar Takai a motar Jamilun, tare da akwatin Shafa wanda daga nan za'a kai nan gidansu Shafa dake Takai ɗin.
Chapter 83 · 0% Book details